Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya

Ana fargabar mutuwar mutane da dama sakamakon gobarar tankokin man da suka yi hastari a safiyar Litinin

Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya

Tankar mai na ci da wuta

Wasu manyan motocin dakon sun  yi bindiga a yankin Ɗan Magaji da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Ana fargabar mutuwar mutane da dama sakamakon gobarar tankokin man bayan sun yi hastari a safiyar Litinin.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a kusa da Makarantar Rochas Foundation, kan titin Kaduna–Kano bypass daga Kwangila zuwa Dan Magaji.

Hatsarin ya haɗa da manyan motoci biyu masu ɗauke da man fetur da kuma motoci biyu ƙirar Golf ɗauke da fasinjoji.

A sakamakon haka, tankokin biyu suka yi bindiga, wanda ya tayar da wutar gobara mai ƙarfi tare da hayaƙi mai kauri ya lulluɓe hanyar.

Jami’an ceto da tsaro sun rufe hanyar, tare da gargaɗin direbobi da su guji bi ta wurin yayin da ake ci gaba da aikin ceto da dawo da gawarwaki.