Tantance ministoci: Kowa zai haye
Ranar Talatar makon nan ce, 13-10-15, Majalisar Dattawa ta fara tantance sunayen jerin mutane 21, da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ma ta a ranar 30-09-15, da kuma wasu 15, da ya sake mika ma ta a ranar Litinin din nan, wanda ya kawo adadin mutanen da ya ke so Majalisar Dattawan ta amince […]
Ranar Talatar makon nan ce, 13-10-15, Majalisar Dattawa ta fara tantance sunayen jerin mutane 21, da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ma ta a ranar 30-09-15, da kuma wasu 15, da ya sake mika ma ta a ranar Litinin din nan, wanda ya kawo adadin mutanen da ya ke so Majalisar Dattawan ta amince masa don ya nada su akan mukaman Ministoci a gwamnatinsa zuwa 36, da wannan kari yanzu kowace jiha tana da Wakili a Majalisar Ministocin da za a kafa nan gaba kadan.Tun a jawabinsa na kama aiki ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata Shugaba Buhari, ya bayyana karara, cewa ba zai nada Ministocinsa ba, har sa a cikin watan Satumba, watanni hudu kenan bayan hawansa kan karagar mulki.
Jinkirin bayyana sunayen Ministocin ya sanya jam`iyyar adawa ta rinka kiraye-kirayen idan har Shugaba Buhari da jam`iyyar APC, ba za su iya ba, ya kamata ya kauce. Ga sauran `yan kasa ma wasu sun nuna zakuwar ya kamata a nada Ministocin, ko nasu sa hau mulki. Amma dai Shugaba Buhari ya ci gaba da bayanin cewa sai zuwa karshen watan Satumban zai bayyana sunayen Ministocin nasa.
Koda a ranar 30 ga watan na Satumba da ta zama ranar karshe akan cika alkawarin shugaba Buhari, sai da ta kai fagen Kakakin Majalisar Dattawan Sanata Dino Melaye, karshen zaman Majalisar na wannan yinin, ya sanar, cewa har suka kammala zaman yinin, jerin sunayen wadanda ake son a nada Ministocin bai karaso Majalisar ba. Amma kuma can bayaan la`asar, sai Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Abubakar Bukola Saraki ta shafin sadarwarsa na Tweeter ya ba da shelar cewa yanzu-yanzun nan fadar shugaban kasa ta aiko masa jerin sunayen mutane 21, da ta ke son a nada Ministoci, har ma ya kara da cewa ba zai bayyana sunayensu ba kamar yadda `yan kasa suka zaku su ji, har sai ranar Talata 6-10-15, in Allah Ya kaimu a zauren Majalisar.
Haka din kuwa aka yi, inda aka bar abokan aikinmu da `yan kasa wajen yin shaci-fadin jerin sunayen mutanen da aka mika wa Majalisar Dattawan don nema zama Ministocin ya kunsa, har sai da ranar Talatar ta zo. Bayan bayyana sunayen ne sai kuma a ranar Alhamis din makon jiyan 08-10-15, Majalisar Dattawan a wani zamanta ta bayyana irin ka`idojin da za ta yi amfani da su wajen tantance wadanda za a nada Ministocin.Wasu daga cikin ka`idojin sun hada da lallai, wadanda za a nada din, bayan sun cika sharuddan da Kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada na shekaru da ilmi da makamantansu, sai kuma sun zo ma ta da shaidar sun bayyana kaddarorin da suka mallaka da Hukumar da`ar Ma`aikata, wato CCB, sannan kowannensu ya gabatar mata da kofe-kofe 151, na tarihin rayuwarsa abin da ake kira Cb, sannan kuma har sai Sanatoci biyu daga cikin uku na jiharsa sun amince da aba shi mukamin Ministan, kana zai samu tsallake siradin Majalisar Dattawan na zama Ministoci.
Tun ba a kai ga mika jerin sunayen wadanda ake son a nada mukaman Ministocin ba, ake ta zargin ana zaman doya da man ja, tsakanin Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Saraki da fadar shugaban kasa, musamman bayan da Hukumar CCB, ta gurfanar da shugaban Majalisar Dattawan gaban Kotun da`ar ma`aikata, wato CCT, bisa ga zargin ya yi karya cikin bayyana dukiya da kaddarorin da ya mallaka a lokacin yana Gwamnan Jihar Kwara tsakanin shekaru 2003 zuwa 2011. Gurfanarwar da aka ce ba ta rasa nasaba da irin yadda Shugaban Majalisar Dattawan ya yi kutsen zama shugaban Majalisar, alhali Sanata Ahmed Lawan, jam`iyyar ta yi nunen `yan Majalisar su zaba.
Waccan tuhumar gurfanarwa, an ta zargin a zaman ramuwar gayya fadar shugaban kasa wai ta sa aka yi ta, zargin da fadar ta yi ta musantawa. Wannan ya sanya akai ta hasashen cewa a duk lokacin da shugaban kasa ya gabatarwa da Majalisar jerin sunayen wadanda ya ke son Majalisar ta amince da su a zaman ministocin, to, kuwa majalisar ba za ta amince mai da su ba a cikin ruwan sanya. Amma kuma sai ga shi bayan mika jerin sunayen mutanen, an yi wani zaman sirri tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin Majalisun Dokokin na kasa a karkashin jagorancin shugaban Malaisar Dattawan Sanata Saraki da suka hada da Kakakiin Majalisar Wakilai ta Tarayya Mista Yakubu Dogara da sauran makarraban Majalisun Dokokin biyu. Bayan kammala taron an ruwaito Sanata Saraki yana cewa an yi taron ne da aniyar yadda za a kara samun cikakken hadin kai don yi wa jama`ar kasa ayyuka da aniyar a samu CANJIN da ya sa `yan kasa suka zabi jam`iyyar APC. Sanata Saraki ya kuma musanta cewa a wajen taron na su da Shugaba Buhari an yi batun shari`arsa da ke gaban Kotun da`ar ma`aikata.
A gefe daya ana zargin sabanin Sanata Saraki ya samu shugabancin Majalisar Dattawan ba Sanata Ahmad Lawan ba da ake zargin bayan kasancewarsa dan takarar jam`iyyar APC ne, shi ne kuma wanda jagoran jam`iyyar ta APC na kasa baki daya Sanata Ahmed Bola Tinubu ya so a nada shugaban Majalisar. Rashin samun hakan daga bangaren Sanata Tinubu ta sanya ba a jituwa tsakanin Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Saraki da Sanata Tinubu, kamar yadda ta bayyana a kwanannan inda shugabannin biyu suka rinka sukar juna ta kafofin yada labarai. Sanata Tinubu yana cewa har gobe Sanata Saraki dan jam`iyyar PDP ne, ya yin da Sanata Saraki ke cewa shi cikakken dan jam`iyyar APC na halak malak ne.
A duk cikin jerin mutane 21 na farko da aka gabatar don zama Ministocin, mutane biyu kawai ta bayyana da zauren Majalisar Dattawan za su fuskanci tantancewa mai cike da kalubale da ka iya kaisu ga fagen rashin kai bentansu. Su ne tsohon Gwamnan Jihar Ribas, kuma Darakta Janar na kamfen din yakin neman zaben Shugaba Buhari, Mista Rotimi Amaechi da Hajiya Amuna Mohammed Wakiliyar Sakataren Majalisar dinkin Duniya akan shirin Muradan karni. Ya yin da ake ta takun saka tsakanin Gwamnan Jihar Ribas Mista Nyeson Wike na jam`iyyar PDP da tsohon gwamnan jihar Amaechi, tun a shekarar 2013, da Amaechin ya bar PDP, tare da wasu gwamnonin PDP hudu zuwa sabuwar jam`iyyar hadaka ta APC.
Wannan sabani ya sanya Sanata George Sekibo, ya gabatarwa da Majalisar koken neman a cire sunan Mista Amaechi, akan suna tuhumarsa da yin ba daidai ba a lokacin mulkinsa a jihar tsakanin 2007 zuwa 2015.
Ita kuwa Hajiya Amuna Mohammed, Sanata danjuma La`ah na manazabar Kudancin Jihar Kaduna, shi ma ya gabatar da koken a janye sunanta, domin a fadarsa mutanen mazabarsa, sun ce ba su san ta ba a zaman `yar asalin jihar ba. Zuwa yanzu dukkan wadannan mutane biyu bayan bayyanarsu gaban Kwamitin da`a na Majalisar Dattawan,Kwamitin ya wanke su daga laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa. Duk da irin sabarta-juyarta ta siyasa da ke tattare da tantance ministocin, ko kusa ba na jin akwai wanda ba zai kai bentansa ba, domin kuwa babu tarihin majalisar ta taba soke wani komai laifinsa. Ko da Sanata Musliu Obanikoro na Jihar Legas ne kadai a shekarar 2011, Majalisar Dattawa da farko ta ki tantance shi, saboda Sanatocin ACN uku daga Jihar Legasa sun ki mara masa baya, amma daga baya dai majalisar ta amince da shi. Don haka a wannan karon ma kowa zai haye, don kuwa ai magana ce ta kowa ya san kowa.