Tanto Dike ta karyata jita-jitar za ta kashe kanta

Fitacciyar jarumar fina-finan Kudanci Najeriya Tonto Dike ta karyata jita-jitar za ta kashe kanta. Jarumar ta karyata jita-jitar ne a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai.Ta ce: “Ban yi yunkurin kashe kaina ba, jita-jita ce kawai. Duk wanda ya yi fice ba a raba shi da irin wadannan labarai marasa kan gado, ni […]

Tanto Dike ta karyata jita-jitar za ta kashe kanta

Tonto DikeFitacciyar jarumar fina-finan Kudanci Najeriya Tonto Dike ta karyata jita-jitar za ta kashe kanta.
Jarumar ta karyata jita-jitar ne a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai.
Ta ce: “Ban yi yunkurin kashe kaina ba, jita-jita ce kawai. Duk wanda ya yi fice ba a raba shi da irin wadannan labarai marasa kan gado, ni ma ga shi yanzu ana yamididi a kaina.”
An baza jita-jitar jarumar za ta kashe kanta ne sakamakon wakokin ‘High’ da ‘It’s Ober’ da ta fitar wadanda ba su samu karbuwa ba, sannan masoyanta sun taso ta a gaba a shafin sadarwa na Twitter, bugu da kari ta fadi a lokacin da ita da Iyanya suke gudanar da wata waka a  kan wani dandamali a Landan.
Ta ce faduwar da ta yi ba za ta sanya ta karaya ba, sai dai ta kara samun karfin gwiwa.