Taqaddamar abinci: Edita ya kwada wa matarsa guduma ta mutu

Wani Editan jaridar Gulf News Francis AMthew ya yi ikrarin kashe matarsa, tare da boye duk wata hujja ta aikata laifin, kamar yadda jami’in gurfanar da masu laifi na Masarautar Dubai ya bayyana. Mathew mai shekara 60 wanda suka shafe shekara 30 suna zaman aure da matarsa mai shekara 62 ya bayyana wa masu tuhumarsa […]

Taqaddamar abinci: Edita ya kwada wa matarsa guduma ta mutu

Wani Editan jaridar Gulf News Francis AMthew ya yi ikrarin kashe matarsa, tare da boye duk wata hujja ta aikata laifin, kamar yadda jami’in gurfanar da masu laifi na Masarautar Dubai ya bayyana.

Mathew mai shekara 60 wanda suka shafe shekara 30 suna zaman aure da matarsa mai shekara 62 ya bayyana wa masu tuhumarsa cewa rikicin ya auku ne kan takaddamar abincin rana a gidansu da ke Jumeirah.

A cewarsa, bayan ya yi mata tsawa Jane ta ki yi masa magana, sai ta tafi xakin kwanciyarsu ta kwanta, inda ya same ta ya kwaxa mata guduma a ka.

Waxanda suka gurfanar da mai laifin gaban kotu, sun  ce Mathew ya ce ya tsorata ne da ya ga tana zubar da jini mai yawa, sai ya xauke gudumar ya fice da ita daga gidan, inda ya boye ta kimanin mita 200 daga gidansu.

Ya bayyana wa masu gabatar da mai laifi a kotu cewa, sai ya dawo gida ya fito da akwakun karfe na ajiya da ke boye, inda ya watso takardun cikinsa suka bazu a gidan. Daga nan sai ya kira ’yan sanda, inda ya ba su rahoton cewa barayi sun shiga gidansu, sun kai wa matarsa hari.

An xauke matarsa zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar.

Binciken musababbin mutuwa na kwakkwaf  da ’yan  sanda suka gudanar a wurin da aka aikata laifin ya nuna alamun shi ya aikata laifi, don haka aka tsare shi, inda aka tunkare shi da tuhuma. Ya yi ikrarin cewa shi ya kashe ta.

Mathew ya nuna matukar bakin cikinsa kan yadda ya kashe matarsa bayan sun shafe shekaru tare, sai ya ce ga shi kuma matarsa ya “rushe ta.”

An ruwaito dai ya rubuta wasika zuwa ga xansa, inda ya nuna nadamarsa kan abin da ya faru, ya kuma yi nuni da cewa bai yi niyar kashe matarsa ba, hakan dai ya faru ne bayan  ya harzuka.

Yanzu dai ana tuhumar Mathew da laifin yunkurin  kisa.

Mathew dai ya kasance tsohon  Editan jaridar Dubai ta GulfNews a tsakanin shekarun 1995 zuwa 2005. Francis da Jane sanannun baki ne ’yan kasar Birtaniya  ne da ke aiki a Dubai. Jaridar Khaleejtimes ta bayar da cikakken rhaoton yadda Edita ya kwaxa wa matarsa guduma ta mutu.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana