Jarin 110.9bn: FCMB ya gabatar da sabbin tsare-tsaren ci gaban bankin
Taron ya yi cikakken bayani game da manufofin Rukunin FCMB, tare da sanya shi zama wata kafa mai inganci ga masu zuba jari.
Rukunin FCMB Plc, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin hada-hadar kuɗi a Najeriya, suna ƙoƙarin tara Naira biliyan 110.9, kuma sun bayar da ƙwararan hujjojin da ya kamata masu zuba hannun jari ya kamata su yi la’akari dangane da hakan.
A ranar 29 ga watan Yuli, 2024, rukunin suka fara bayar da hannun jarin biliyan 15.197 a kan farashin Naira 7.30, da nufin tara Naira biliyan 110.9 kafin lokacin rufe wannan garaɓasa a ranar 4 ga watan Satumba, 2024.
- Najeriya ta ƙara kuɗin yin takardar fasfo
- Bibiyar Kasafin Kuɗi: Media Trust da Gidauniyar MacArthur sun horar da ’yan jarida
A wani taro da suka gudanar a Kasuwar Zuba Hannun Jari ta Najeriya (NGX), Rukunin FCMB sun bayyana nasararsu a harkar hada-hadar kuɗi, sannan sun bayyana dalilin da ya sa wannan taro ya zamo wani babban tubali kan cimma nasara a gaba.
Shugaban Rukunin Kamfanin, Ladi Balogun, ya bayyana cewa wannan yunƙuri na tara kuɗin ya zama wani ɓangare na babban shirin da bankin ke yi na cika sharuɗan da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya gindaya tare da ƙara bunƙasa shirye-shiryen kamfanin a nan gaba.
Ya ce akwai shirin ƙara tara kuɗi har Naira biliyan 397 a nan gaba, wanda FCMB ke shirin tabbatar da matsayinsa a kasuwar hada-hadar kuɗi.
Ba wai FCMB na ƙara girma ba ne kawai, suna ƙara samun ci gaba da bunƙasa sosai. Bankin yana ƙara samun sabbin abokan cinikayya kimanin miliyan biyu a kowace shekara, wanda hakan ya sanya suka zama cikin manyan bankuna a Najeriya.
A cewar Balogun, kuɗin da za su tara daga wannan yunƙurin zai taimaka wajen bayar da lamuni ga manyan fannoni kamar harkar noma, ƙananan masana’antu (SMEs), da kuma kayayyakin da ba su da alaƙa da mai —waɗanda suke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin Najeriya.
“Manufarmu ita ce, samar da ribar ga masu zuba hannun jari, duk da ƙarin hannayen jari da muke fitarwa. Kuɗaɗen da za mu tara za mu yi amfani da su wajen bunƙasa kasuwancinmu, musamman ta hanyar bayar da lamuni ga manyan fannoni kamar harkar noma, ƙananan masana’antu, da kayayyakin da ba su da alaƙa da harkar mai, waɗanda muke ganin suna da muhimmanci ga ci gaban Najeriya.”
Balogun, ya jaddada cewa sabon tsarin tara kuɗin zai bai wa FCMB damar zuba jari a sabbin fasahohi, ƙara ƙarfi a harkar kasuwanci, da kuma ci gaba da bunƙasa harkar zuba hannun jari.
FCMB, sun bayyana ci gaban da suka samu mai tarin yawa a ɓangaren samun kuɗaɗen shiga da riba, wanda ke tabbatar da ingancin tsare-tsarensu na kasuwanci da kuma dabarun da suke amfani da su.
Tsarin samar da kuɗin zai taimaka wajen zuba jari mai yawa a fannin fasahar zamani, zai taimaka wa FCMB wajen samun ƙarin abokan ciniki da kuma kasancewa a gaba a tsakanin abokan takararsa.
Duk da ƙalubalen tattalin arziƙin ƙasar nan ke fuskanta, FCMB suna ci gaba da samun nasara, suna bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan matsaloli da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
A taƙaice, yunƙurin Rukunin FCMB na tara kuɗaɗen ba wai ya tsaya ba ne kawai don cika sharuɗa da dokoki ba ne; har da ciyar da kamfanin gaba, musamman ta ɓangaren masu zuba hannun jari da suke neman tsari mai ɗorewa, Rukunin FCMB ya bayyana cewar wannan wata babbar dama ce ga masu zuba hannun jari wadda bai kamata su bari ta suɓuce musu ba.
Muhimman bayanai game da taron:
- Rukunin FCMB ya bayyana irin ribar da yake samu mai gwaɓi a kowace shekara, hakan na da nasaba da tsare-tsaren kasuwancinsa na musamman da dabarun da suke amfani da su.
- Kuɗaɗen da za a tara za su tallafawa harkokin fasahar zamani, faɗaɗa kasuwancin kamfanin, da kuma ƙarfafa harkar takara a ɓangaren kasuwanci.
- Duk da ƙalubalen tattalin arziƙi, Rukunin FCMB, ya jajirce wajen ci gaba da samun nasara tare da shawo kan matsaloli da kuma ci gaba da girma.
- Shugabannin Rukunin suna da ƙwarewa mai tarin yawa a harkar masana’antu, wanda ke ƙara wa masu zuba hannun jari ƙwarin gwiwar yin mu’amala da kamfanin.
- Taron ya yi cikakken bayani game da manufofin Rukunin FCMB, tare da sanya shi zama wata kafa mai inganci ga masu zuba jari.
- An bai wa masu zuba hannun jari tabbaci, ta hanyar buƙatar su yi la’akari da kyakkyawan ayyuka da Rukunin FCMB ke yi a fannin kuɗi, shirye-shiryen samar da ci gaba, da kuma damar samun riba mai gwaɓi.