Tara kan rashin rijistar binne gawa a Jihar Kaduna
A watan Afrilun da ya gabata ne majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da wata doka da za ta tilasta wa al’ummar jihar yi wa gawa rijista kafin su rufe mamaci a makabarta, idan kuma ba a yi ba akwai tara mai yawa da za a biya. Majalisar ta tura dokar ga gwamnan jihar Kaduna […]
A watan Afrilun da ya gabata ne majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da wata doka da za ta tilasta wa al’ummar jihar yi wa gawa rijista kafin su rufe mamaci a makabarta, idan kuma ba a yi ba akwai tara mai yawa da za a biya.
Majalisar ta tura dokar ga gwamnan jihar Kaduna domin ya sanya mata hannu ta fara aiki.
Majalisar ta nuna cewa ta yi dokar ne da nufin sanin yawan wadanda suka mutu da kuma jariran da suka mutu kafin a yi masu rijistar haihuwa. Saboda haka dokar za ta tabbatar karamar hukuma tana yin rijistar duk wanda ya rasu tare da yin rijistar duk jaririn da aka haifa a yankin nata.
Da zarar ofishin karamar hukuma ta samu labarin rasuwa za ta bayar da wata takarda mai suna ‘form A’ a cika kafin a binne gawar. Kuma ba a yarda a rufe gawa, ba tare da an samu shaidar izinin rufe ta ba, sai dai idan alkalin majistare ko likita ko jami’in da ya binciki sanadiyyar mutuwar mamacin ne ya bayar da umurnin yin haka a rubuce.
Haka kuma wata majiya ta nuna cewa rijistar ba kyauta ba ne, za a biya Naira dubu biyar ne kafin a samu shedar amincewa a binne gawa. Wata hanyar samun kudin shiga kenan ga kananan hukumomin jihar Kaduna.
Dokar ta tanadi cewa duk wanda ya rufe mamaci ba tare da izini ba, za a ci tararsa kudin da ba zai kasa Naira dubu 50 ba.
Haka kuma duk wanda ya binne jaririn da ya rasu ko jaririn da aka haifa babu rai, ba tare da izini ba, shi ma zai biya tarar kudin da ba zai gaza Naira dubu 50 ba.
Dokar kuma ta bai wa kananan hukumomi damar samar da isasshen kudi domin samar da makabartu da ma’aikatan da za su gudanar da su da tabbatar da tsaronsu da kuma katange su.
Wannan doka da majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da ita a yayin wani zama da mataimakin shugaban majalisar Nuhu Shadalafiya ya jagoranta, ta jawo cece-ku-ce a tsakanin al’ummar jihar, musamman shugabannin addinin musulunci, inda tuni Majalisar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna ta soki lamirin dokar, tare da shawartar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i da ya yi watsi da dokar kada ya sanya mata hannu.
Hakan yana kunshe ne a jawabin bayan taron majalisar Limamai da Malaman wanda ke dauke da sanya hannun sakatarenta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu da shugabanta Sheikh Ibrahim Nakaka, inda majalisar malaman ta nuna cewa dokar ta saba wa koyarwar addinin musulunci.
Majalisar Limamai da Malaman ta kuma bayyana takaicin ganin duk da rashin amincewar da ta nuna ga dokar tun da farko, sai da majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da ita.
Abin da yake daure wa mutane kai game da wannan dokar shi ne, ana nufin ba za a yi wa mamaci jana’iza ba ne sai tare da izinin hukuma, kuma ba a yarda da samun izini daga mai unguwa ko dagaci ko sarki ba, sai dai daga alkali ko likita ko jami’in karamar hukuma? To idan ba ranar aiki ba ne aka yi rasuwar sai an jira an dawo aiki ke nan? Idan kuma ranar aiki ne amma an tashi aiki sai an jira an koma aiki ke nan kafin a binne gawar?
Shin a makabartu mallakar gwamnati da za a bude ne za a tabbatar babu wanda ya rufe mamacinsa a cikinsu sai da izinin hukuma, ko kuwa har da makabartun da mutane suka samar wa kansu ne dokar za ta yi aiki?
Domin a iya sanina mafi yawan makabartun da ke jihar Kaduna mutane ne suka samar wa kansu ba gwamnati ba, kuma wadanda ke kula da makabartun ‘yan aikin sa-kai ne ba gwamnati ce ta dauke su aiki ba. Ko kuwa ana nufin za a ajiye jami’in gwamnati ne a kowace makabarta da jama’a suka samar wa kansu a jihar Kaduna da zai tabbatar an yi wa gawa rijista kafin a rufe ta a makabartar?
Aiwatar da wannan dokar dai zai yi matukar wahala, musamman ga al’ummar musulmi, saboda a tsarinsu ba a so a dauki lokaci mai tsawo sosai ba a rufe mamaci ba, saboda haka za a iya fuskantar matsala idan an yi rasuwa an binne mamaci sai kuma a ga wani jami’in gwamnati ya zo yana tambayar takardar izinin rufe gawar, a wannan halin da iyalai da ‘yan uwan mamacin suke cikin juyayin rashin da suka yi ana iya samun tashin hankali, domin kuwa da me za su ji? Da rashin da aka yi musu za su ji, ko da tuhumar gwamnati kan rashin yin rijista?
Idan har ya zama dole gwamnati ta yi amfani da wannan dokar domin sanin adadin mutanen da suka mutu a jihar Kaduna, kamata ya yi ta bi hanyar lalama maimakon ta hanyar tursasawa har ma da tara. Gwamnati tana iya tura ma’aikatanta masu kula da makabartu zuwa gidajen da aka yi rasuwa da kansu su rika tambaya ko an yi rijistar mamacin? Idan ba a yi ba sai su ce to mun zo ne domin mu yi masa rijista. Sai su samu duk bayanan da suke bukata a wurin dangin mamacin, su yi tafiyarsu ba tare da wata hatsaniya ba.
Wannan dai ba karamin aiki ba ne, domin a garuruwa da birane ne kawai za a iya samun nasarar yin rijistar, amma zai yi wahala a samu nasara a yankunan karkara saboda a kan yi mutuwa da dama amma hukuma ba ta sani ba.