Tarayya Turai ta kaddamar da gidauniyar tallafi ta Dala miliyan 143 a Borno

kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da gidauniyar tallafi ta Dala miliyan 143 a Borno a ci gaba da shirinta na magance matsalar rayuwa da ake ciki a yankin Arewa maso Gabas. Shugaban Sashin Hadin kai a ayarin kungiyar a Najeriya, Mista Kurt Cornelis ne ya sanar da haka a lokacin da yake kaddamar da gidauniyar […]

Tarayya Turai ta kaddamar da gidauniyar tallafi ta Dala miliyan 143 a Borno

kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da gidauniyar tallafi ta Dala miliyan 143 a Borno a ci gaba da shirinta na magance matsalar rayuwa da ake ciki a yankin Arewa maso Gabas. Shugaban Sashin Hadin kai a ayarin kungiyar a Najeriya, Mista Kurt Cornelis ne ya sanar da haka a lokacin da yake kaddamar da gidauniyar ta shekara uku a ranar 24 da watan Janairu a Maiduguri. Ya ce shirin tallafin zai taimaka wajen sanya natsuwa a zukatan ’yan gudun hijira da yakin Boko Haram ya shafa a yankunan Borno. A cewar Cornelis, tallafin zai taimaka wa akalla mutum miliyan daya da za su amfana da shirye-shirye tara da za su gudanar. “Wannan shirin na Borno ne kawai, kuma makasudin shirin shi ne a gyara kayayyakin more rayuwa da suka lalace a sanadiyar rikicin Boko Haram.

“Hakan ya hada da gyara ajujuwan makarantu da asibitoci da cibiyoyin samar da ruwa da makamashi mara illa da kuma abinci mai gina jiki. bangare na biyu shi ne za mu fara harkar noma domin mu samar da ayyukan yi ga mutanen da rikicin ya shafa domin su sake gyara rayuwarsu, wanda zai sa su daina jiran dan abincin da ake ba su da sauran kayayyakin tallafi,” inji shi.

Cornelis ya ce za a shirya ayyukan ne yadda za su zamo cikin sauki kuma za a fuskanci matasa ne da mata da marasa karfi, sannan zai taimaka wajen dawo da mutane garuruwansu. Shirin zai kasance a karkashin kulawar wani kwamiti da zai hada da wakilan Gwamnatin Jihar Borno da Tarayyar Turai da Hukumar Jin kai da Kare Jama’a ta Turai da Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare ta Najeriya da kuma Kwamitin PCNI.