Tarayyar Turai ta kafa asusu don ‘yan gudun hijirar Afirka
A jiya Alhamis ne Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai (EU) da takwarorinsu na kasashen nahiyar Afirka suka sanya hannu kan wata yarjejeniya da nufin taimaka wa ‘yan gudun hijirar da suka fito daga Afirka, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.kungiyar EU ta amince ta bayar da tallafin Dala biliyan daya da miliyan dari […]
A jiya Alhamis ne Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai (EU) da takwarorinsu na kasashen nahiyar Afirka suka sanya hannu kan wata yarjejeniya da nufin taimaka wa ‘yan gudun hijirar da suka fito daga Afirka, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
kungiyar EU ta amince ta bayar da tallafin Dala biliyan daya da miliyan dari tara ga kasashen Afirkan domin su hana ‘yan kasashensu zuwa nahiyar Turai.
An gudanar da taron ne a kasar Malta, wadda take cikin kasashen farko na nahiyar Turai da ’yan gudun hijiran suke fara kwarara saboda yadda take kusa da nahiyar Afirka.
kasashen da za su ci gajiyar wannan tallafi sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Gambiya da Mali da Mauritaniya da Nijar da Senegal da kuma Najeriya.
Kodayake, Shugaban Senegal, Macky Sall, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Raya Tattalin Arzikin kasashen Yankin Afirka ta Yamma (ECOWAS), ya ce taimakon zai taimaka wajen fara dakile kaurar jama’a daga nahiyar, amma suna neman karin kudi.
Za a yi amfani da kudin ne wajen samar da ayyukan yi da samar da ilimi, da kiwon lafiya da kuma tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin.