Tarayyar Turai za ta soma aika wa Ukraine makamai
Wannan ne karon farko da EU za ta yi hakan a tarihinta.
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta sanar da cewa za ta soma aika makamai zuwa Ukraine domin taimaka wa kasar wajen tunkarar dakarun Rasha da suka mamaye ta.
Wannan ne karon farko da EU za ta yi hakan a tarihinta.
Da take magana yayin taron manema labarai a Yammacin ranar Lahadi, Shugabar Hukumar Turai Ursula von der Leyen ta ce yunkurin na nufin “samun sauyi”.
Ta kuma sanar da wasu jerin takunkumai da aka saka wa Rasha da Belarus, ciki har da hana jiragen kasar bi ta sararin samaniyar kasashen kungiyar.
Tun farko kasashen na Turai daya bayan daya suka ce za su rufe sararin samaniyarsu ga jiragen Rasha, ciki har da Jamus na tsawon wata uku.
Yayin da aka rufe samaniyar Ukraine, yanzu jiragen na da tsirarun hanyoyin da za su iya bi a nahiyar.
Gomman jirage a filayen jirage na Domodedovo da Sheremetyevo sun soke jigila a yau Lahadi, ciki har da na zuwa Paris, Faransa, da Vienna da Kaliningrad.