Tarayyar Turai za ta tarairayi ’yan gudun hijira dubu 50

Tarayyar Turai za ta kwasi ’yan gudun hijira dubu 50 daga Afirka da Gabas ta tsakiya da Turkiyya, don shawo kan masu shiga hadari a tekun Mediterranean wajen shiga kasashen tarayyar . An gabatar da kudurin shirin tarairayar ’yan gudun hijirar ne ga kasashenTarayyar Turai da za su aiwatar nan da shekara biyu masu zuwa, […]

Tarayyar Turai za ta tarairayi ’yan gudun hijira dubu 50
Tarayyar Turai za ta tarairayi ’yan gudun hijira dubu 50

Tarayyar Turai za ta kwasi ’yan gudun hijira dubu 50 daga Afirka da Gabas ta tsakiya da Turkiyya, don shawo kan masu shiga hadari a tekun Mediterranean wajen shiga kasashen tarayyar .

An gabatar da kudurin shirin tarairayar ’yan gudun hijirar ne ga kasashenTarayyar Turai da za su aiwatar nan da shekara biyu masu zuwa, kartkashin shirin sake tsugunnar da al’umma na yankin, wanda aka bullo da shi lokacin da rikicin kaurar al’umma ta addabi nahiyar a shekarar 2015.

“Akwai bukatar mu shawo kan matsalar tafiye-tafiye ba bisa ka’ida ba,” a cewar Kwamishinan kaurar Al’umma na Tarayyar Turai Dimitris Abramopoulos kamar yadda ya bayyana wa taron ’yan jarida a Brussels.

Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da cewa, ‘fito wa Tarayyar Turai da shirin sake tsugunnar da al’umma zai dauki nauyin akalla mutum dubu 50 da ke tattare da hadari kuma suke bukatar kariyar hukumomin duniya don shiga Turai nan da shekaru biyu masu zuwa.”

Tuni Tarayyar Turai ta sake tsugunnar da mutane dubu 23 ’yan gudun hijirar da ke sansaninsu da ke wajen Tarayyar Turai, a karkashin shirin, musamman wadanda suka fito daga Turkiyya da Jordan, wadanda suka cunkushe a kasar don gudun ceton rai daga yakin Siriya.

Za a ci gaba da shirin sake tsugunnar da mutanen, amma “za a fi mayar da hankali,” kan mutanen da suka fito daga Libiya da Masar da Nijar da Sudan da Chadi da Habasha, a cewar hukumar.

Wannan shirin dai ya saba wa shirin sake tsugunnar Tarayyar Turai da ke bayar da kason adadin ’yan gudun hijirar da suka isa Italiya da Girka da ake mayar da su wasu kasashen Turai, al’amarin da aka ce ya kawo karshe tun Larabar da ta wuce.

A Larabar da ta gabata ne dai Paparoma Francis ya kaddamar da shirin fadakarwa na shekara biyu kan matsalolin da nsuka dabaibaye ’yan gudun hijira, don shawo kan kiyayyar da ake nuna musu a Amurka da Turai da sauran wurare.

Fadakarwar tasa na kira ne kan lallai al’umma ta tarairayi ’yan gudun hijirar a saurari bayaninsu, sabanin yadda ake nuna musu kyara.

Paparoma Francis, wanda shi kansa da ne ga dan gudun hijirar Italiya da ya isa kasar Argentina, ya kaddamar da fadakarwarsa ne a taron mako-mako da yake gabnatarwa,  inda ya nuna aniyarsa ta bayar da mafaka ga ’yan gudun hijira da suka yi dandazo a dandalin St. Peter.