Tarbiyyar Yara: Jan hankalin Gwamnatocin Arewa dangane da tsarin koyo da koyarwa a makarantunmu
Tunzura yara ’yan makaranta cikin harkar siyasa, ta hanyar sa su yin zanga-zanga a ranar Alhamis 25 ga Oktoba 2018, domin nuna goyon bayan mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, bisa zargin da ake yi masa na karbar rashawa daga ’yan kwangila, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa cikin wasu hotunan […]
Tunzura yara ’yan makaranta cikin harkar siyasa, ta hanyar sa su yin zanga-zanga a ranar Alhamis 25 ga Oktoba 2018, domin nuna goyon bayan mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, bisa zargin da ake yi masa na karbar rashawa daga ’yan kwangila, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa cikin wasu hotunan bidiyo guda biyu, ya ja hankulan jama’ar Najeriya, tare da fadin albarkacin bakinsu.
Duk da yake Gwamnatin Kano ta nisanta kanta daga wannan al’amarin, tare da bayyana kudirinta na yin bincike don hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki, ya kamata a yi tsokaci kan illolin da wannan abu ka iya jawowa, da manyan dalilan da suka haddasa faruwarsa da kuma yadda za a magance su.
Mafi illar abin da wannan abu zai jawo shi ne cusa mummunar akida da gurbata tarbiyyar kananan yara. Tunzura yara su yi zanga-zanga don nuna goyon bayan abin da ba a tabbatar da gaskiyarsa ba, zai dasa mummunar akidar cewar karadi da taratsi su ne kan gaba wajen neman biyan bukata ko cin nasara, amma ba hujja ce abar nema ba. A yayin da mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da magoya bayansa ke kokarin wanke shi daga zargin karbar rashawa, sun afka cikin abin da ka iya zama laifi mafi muni na cin zarafin yara. Da alama wannan abu zai bibiye mu a cikin tarihinmu na kasancewa al’uma ta farko da wannan abin kunya ya faru a cikinta, tare da zubar mana da kima. Kuma zai yi wuya mu iya musanta zargin da ake yi mana na sanya yara kanana jefa kuri’a lokacin zabe.
A wani bangaren kuma akwai alamun gagarumin sakaci da amanar da aka danka wa malaman makaranta da mahukunta na bangaren ilimi a Jihar Kano, domin kulawar yara na karkashinsu a lokacin da suka fito da su ba don su wakilci ilmi ba, sai don su shiga cikin zanga-zangar da ba ta dace da karancin shekarunsu ba. Har wa yau, akwai alamun rashin adalcin ganin cewar hotunan wadannan yara masu zanga-zanga sun nuna alamun fitowarsu daga makarantun gwamnati, inda ’ya’yan talakawa ke halarta. Kuma su ne makarantun da ke cikin mafi munin karancin kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa, a yayin da ’ya’yan masu hali ke halartar makarantu mafiya inganci kuma ba su daga cikin masu zanga-zangar. Lallai akwai alamar rauni bisa bangaren da ke da alhakin sa ido kan gudanar da ilimi a Jihar Kano.
Manyan dalilan da suka haifar da wannan yanayi sun hada da halin ko-in-kula da harkokin ilimi, musamman a Arewacin Najeriya. Mu sani cewa har yanzu Najeriya na daga cikin kasashe mafiya yawan yaran da ba su zuwa makaranta a fadin duniya. Kuma abin takaici shi ne abin ya fi shafar ’ya’yanmu mata. Wannan babbar barazana ce ga ci gaban al’umma.
A kiyasin asusun tallafa wa ilimin yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), akwai yara sama da miliyan 14 da ba su zuwa makaranta a Arewacin Najeriya. Fatara da rashin tsaro sun kara muni, tabarbarewar ilimi musamman a Arewa Maso Gabashin Najeriya. Bugu da kari, a kiyasin UNESCO, wajibi ne kowace gwamnati ta zamanto tana kashe akalla kimanin kaso ashirin da biyar zuwa ashirin da bakwai cikin dari (25-27%) na kasafin kudin ayyuka a kowace shekara a bisa hidimar ilimi, in har ana son cin ma ingancin da ake bukata ga ilimi. A halin yanzu gwamnatocin tarayya da na jihohin Najeriya suna ware kimanin kaso goma cikin dari (10%) ko ma kasa da haka a bangaren ilimi. Kaico! Babu shakka koma-baya da tabarbarewar harkokin ilimi a Arewacin Najeriya ya kai a sanya Dokar-Ta-Baci a bangaren ilimi domin ceto shi daga yanayin da yake ciki a halin yanzu.
A yau sai ga shi duk da mummunan yanayin tabarbarewar harkokin ilimi da illar barace-baracen kananan yara da ta addabi Arewacin Najeriya, ’yan tsirarun yaran da suka samu zuwa makaranta ake yunkurin yi masu fashin kuruciyarsu da cin zarafinsu ta hanya mafi muni, watau yin amfani da su a wajen yin zanga-zangar siyasa.
Ina mafita?
Yawancin masu sharhi sun tabbatar da cewa munin cin zarafin kananan yara, ta hanyar fitar da su daga azuzuwansu da tunzura su don yin zanga-zanga ya zarce na zargin karbar rashawa da ake yi wa mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje. Duk da yake Gwamnatin Kano ta nisanta kanta daga wannan aika-aika, tare da bayyana kudirinta na yin bincike don hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki, ya kamata a gaggauta aiwatar da wannan bincike tare da yin abin da sharia ta tanadar.
Har wa yau, ya kyautu mai girma gwamna ya fito ya nemi afuwar iyayen yara game da wannan lamari, domin kuwa an fara samun jama’ar da suka ci alwashin daukar matakan shari’a baya ga tir da suka yi bisa abin da ya faru kan yaranmu. Hausawa sun ce alhaki kuikuyo ne, don yana bibiyar wanda ya aikata shi. An yi hasashen cewar in har wadannan yara suka girma suka fahimci cewa an ci zarafinsu, tabbas za su kyamaci wannan abu, kuma za su tsani duk wanda ya gallaza masu ba tare da saninsu ba. Kuma a sakamakon ci gaban da aka samu a fagen kimiyyar sadarwa da adana bayanai na zamani, watakila bayan wasu shekaru yaran su bankado wadannan hotuna da rahotannin da ake yadawa a yanzu, kuma su dauki matakin shari’a a kan Gwamnatin Kano ta yanzu, da masu hannu a cikin cin zarafinsu.
Ga wadansu ’yan shawarwari bisa yadda za a samu ci gaban ilimi da yadda za a magance aukuwar abu mai kama da wannan a nan gaba:
A Samar da kyakkyawan tushen tarbiyya ga yara daga mu iyaye (a gidajenmu) da kuma malamai (a makarantu):
Iyayaye maza da mata mu tuna ’ya’ya wata babbar baiwa ce da Allah (SWT) ke yi wa halittunsa, mutane da dabbobi. Ya ishe mu ishara mai girma kan baiwar ’ya’ya, cewar Allah shi Ya halicce su amma kuma ya dangana su gare mu har ake kiran su da ’yarka ko danka. Don haka kiyaye hakkokin ’ya’ya yake da muhimmanci domin bayyana godiya ga Ubangiji, Sarkin baiwa. Malaman makaranta na da gagarumar gudunmawa bisa ilimintarwa da tarbiyya ga yara, bisa gwargwadon matakin rayuwar yaran. Wannan ya hada da kiyaye jin su da ganinsu daga abin da zai gurbata tunaninsu da ayyukansu. Sauraro da gani suna da matukar tasiri kan tunani, hikima da ayyukan kananan yara. Mu kwadaitar da yara bisa kyawawan dabi’u da kuma tsoratarwa ga barin munanan dabi’u kuma mu ma iyaye da malamai mu zamanto ma su aikata kyawawan dabi’u da nisantar munana domin yara su yi koyi da mu. Mu ilimintar da yara kan zamantakewa a cikin gida da unguwa da kuma cudanya da mutane tare da kimsa masu tsoron Allah a sasari da boye cikin duk abin da za su aikata da tunanin rayuwa bayan mutuwa, da kuma yin tanadi domin ranar hisabi. Ta wannan hanya ce za su samu kwarin gwiwar bin abubuwan da ake bukata, da kuma nisantar wadanda ba a bukata.
Bai wa ilimi fifiko bisa dukkan manyan ayyukan gwamnati a Arewacin Najeriya:
Ya zama wajibi gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya su farka domin aiwatar da muhimman gyararraki da nufin inganta ilimi, wanda shi ne tafarkin magance fatara da rashin tsaro da kuma ci gaban al’uma.
Sa’annan a ba da muhimmanci a bangaren sa ido don tabbatar da ingancin ilimin a makarantun gwamnati da masu zaman kansu. A wani bangaren kuma tilas ne a kyautata wa malaman makaranta ta hanyar biyan su albashi mai tsoka da kuma samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa da ya dace da muhimman ayyukansu na rainon shuwagabanni, kuma ruhin al’umma.
Bisa ga ilimin ’ya’yanmu mata, gwamnatoci da al’ummar Arewacin Najeriya su kara zage damtse wajen samar da yanayi mai inganci don habaka ilimin ’ya’yanmu mata tare da kare mutunci da kimarsu na iyaye kuma tubalan gina al’uma managarciya. A kuma samar da kyakkyawan tsaro a gare su bisa tafarkin neman iliminsu a kowane mataki.
Shigar da ilimin Alkur’ani da Arabiyya cikin tsarin ilimin zamani a Arewacin Najeriya:
Ilimin Alkur’ani mai girma da Arabiyya da na addinin Musulunci shi ne tushen wayewa da ci gaba a tarihin al’umar Musulmin Arewacin Najeriya, wanda a halin yanzu yake fuskantar kalubalen dusashewa. A halin yanzu, ’ya’yanmu da suke cikin tafarkin Almajirci sun fada a cikin munanan yanayin barace-barace a maimakon inganta rayuwarsu. Don haka dole ne gwamnatoci da al’ummar Arewacin Najeriya su samar da tsare-tsare da za su maido da martabar wannan ilimi tare da shigar da shi cikin tsarin ilimin zamani da kuma gwama manhajarsa da ta fagagen ilimin kimiyya da fasaha ta wadannan hanyoyi:
Ba da damammaki ga mahaddata Alkur’ani mai girma su halarci horarwa ta musamman a fagagen ilimin zamani. Wannan zai ba su damar samun kwarewa da kuma takardun shaidar da za ta ba su cancantar samun ayyukan yi a fannonin rayuwa. Ya kyautu a bai wa mahaddata Alkur’ani fifiko na musamman wajen shiga jami’o’i da sauran manyan makarantu, baya ga cika sauran sharuddan da ake nema.
Samar da tsarin manhajojin ilimi a fannonin adabi, kimiyya, fasaha, tattalin arziki, zamantakewa, da sauransu, masu tushe daga koyarwar Alkur’ani mai girma. Yunkurin samar da muhimman ilimi a fagen kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa da Ajami zai taimaka wajen yaduwarsu da saukin fahimta da kuma tasirinsa ga ci gaban al’umma.
Tura ta kai bango! Tilas dukkan masu ruwa da tsaki daga gwamnatoci da al’umar Arewacin Najeriya su farka domin tsamo ilimi daga yanayin da yake ciki a halin yanzu. Babu shakka koma-baya da tabarbarewar harkokin ilimi a Arewacin Najera ya kai a sanya Dokar-Ta Baci a bangaren ilimi domin ceto shi daga yanayin da yake ciki a halin yanzu. Allah Ya sa mu dace.
Farfesa Sarkinfada ya aiko da tsokacin nan daga Jami’ar Bayero Kano, [email protected] <mailto:[email protected]>