Tare da Sheikh

240. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ’yanta rabonsa cikin abin mallaka da suka yi tarayya da wani cikin bawa, kuma ya kasance yana da dukiyar da ya kai kimar […]

Tare da Sheikh
Tare da Sheikh

240. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ’yanta rabonsa cikin abin mallaka da suka yi tarayya da wani cikin bawa, kuma ya kasance yana da dukiyar da ya kai kimar shi (bawan), to shi yake da hakkin ’yanci.” Nafi’u ya ce, “Idan ba haka ba to shi dai ya ’yanta nasa rabon daga gare shi (bawa).” Ayyub ya ce, “Ban sani ba wanne ne daga ciki Nafi’u ya fade shi ko wani abu ne daga cikin Hadisin.”
241. An karbo daga Ahmad dan Mikdam ya ce: “Fudail dan Sulaiman ya ba mu labari ya ce, Musa dan Ukubah ya ba mu labari ya ce, “Nafi’u ya ba ni labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai shi ya kasance yana fatawa (amsa) ga bawa ko baiwa da ke tsakanin mutum biyu sai dayansu ya ’yanta rabonsa daga gare shi yana cewa: “Hakika (wanda ya ’yanta rabosa) ya wajaba a kansa ya ’yanta shi (bawan) dukkansa. Idan wanda ya ’yanta shi na da dukiyar da zai biya kimar kudin bawan, sai a yi masa kudin bisa adalci ya biya abokan tarayyarsa rabonsu. Ya fita hanyarsa (bawa).” dan Umar yana ba da labarinsa daga Annabi (SAW). Kuma Laisu da dan Abu Zi’ib da dan Is’hak da Juwairiyyat da Yahya dan Sa’id da Isma’il dan Umayyat daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) daga Annabi (SAW) a takaice.

Babi na Biyar: Idan mutum ya ’yanta rabonsa daga bawa kuma ba ya da dukiyar da zai iya biyan sauran rabon abokan tarayyarsa. To bai halatta a tsanata wa bawan ga biyan sauran kudin da ya rage daga rubutun kudin fansa:
242. An karbo daga Ahmad dan Abu Raja’u ya ce: “Yahya dan Adam ya ba mu labari ya ce, Jarir dan Abu Hazim ya ce: “Na ji kattada ya ce, “Nadaru dan Anas dan Malik daga Bashir dan Naheek daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ’yanta wani rabo daga bawan da suka yi tarayya da wani….da kamar abin da ya gabata.”
243. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari ya ce, Sa’id ya ba mu labari daga kattada daga Nadar dan Anas daga Bashir dan Naheek daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya ’yanta wani rabo, ko ya ce wani yanki daga abin mallaka (bawa), to kubutar wan an bawa na cikin dukiyarsa idan yana da dukiya, idan ba haka ba, sai a sanya kimar sauran kudin bisa adalci ga bawan ba tare da tsananta masa ba wajen biyan sauran kudin.” Hajjaj dan Hajjaju ya karbo shi da Abban da Musa dan Khalf daga kattada, Shu’aba ya takaita shi.

Babi na Shida: Hukuncin kuskure da mantuwa cikin ’yanta bawa da sakin aure da makamancinsa. Babu ’yantawa face cikin tafarkin Allah. Bisa fadar Annabi (SAW) cewa: “Kowane mutum yana da sakamakon niyyarsa, babu (hukuncin tabbatar da) niyya ga mai mantuwa da mai kuskure”:
244. An karbo daga Humaidi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Mis’ar ya ba mu labari daga kattada daga Zurarat dan Aufa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Hakika Allah Ya ketarar da al’ummata bisa ga abin da kirjinta ya yi mata wasi-wasi matukar ba ta yi aiki da shi ba, ko kuma ba ta yi magana da shi ba.”
245. An karbo daga Muhammad dan Kasir ya ce: “Sufiyan ya ce, Yahya dan Sa’id ya ba mu labari daga Muhammad dan Ibrahim Tamimi daga Alkamatu dan Wakdasu Lasiyyu ya ce: “Na ji Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da shi) ya karbo daga Annabi (SAW) ya ce: “Ayyuka da niyya suke tafiya (gudana), kuma kowane mutum na da irin tasa sakamakon niyya. Wanda hijirarsa (kauransa), ta kasance zuwa ga Allah da ManzonSa ne, to sakamakon hijirarsa na ga Allah da ManzonSa. Wanda hijirarsa ta kasance saboda duniya ko don wata mace da zai aure ta, sakamakon hijirarsa na ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi.”