Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi   Babi na Tamanin da Biyar:  Sanya kwalkwali domin fita yakin daukaka kalmar Allah: 595. An karbo daga Abdullahi dan Maslamah ya ce: “Abdurrahman dan Abu Hazim ya ba mu labari daga Sahlu (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai shi an tambaye shi game da yadda aka yi […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

 

Babi na Tamanin da Biyar: 

Sanya kwalkwali domin fita yakin daukaka kalmar Allah:

595. An karbo daga Abdullahi dan Maslamah ya ce: “Abdurrahman dan Abu Hazim ya ba mu labari daga Sahlu (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai shi an tambaye shi game da yadda aka yi da raunin Annabi (SAW) Ranar Yakin Uhudu sai ya ce: “An yi wa fuskar Manzon Allah (SAW) rauni har jini sai da ya rufe ta (fuska) aka karya hakoransa na gaba, kwalkwalin kansa ya fashe. Sai Fadima (AS) ta kasance tana wanke masa jinin, Aliyu (RA) yana zuba ruwa. Lokacin da jinin ya ci gaba da zuba bai tsaya ba face sai da ta samo tabarmar kaba ta kona ta har sai da ta zamo toka. Sai ta rika lika masa bisa raunin, jinin ya tsaya.”

 

Babi na Tamanin da Shida: 

Wanda bai ga laifin wanda ya karya takwabi ko soke dabbobi lokacin mutuwa:

596. An karbo daga Amru dan Abbas ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari daga Sufiyan daga Abu Is’hak daga Amru dan Haris ya ce: “Annabi (SAW) bai bar komai ba bayan rasuwarsa face takwabinsa da alfadara da wata kasa a Khaibara da ya bar ta sadaka.”

 

Babi na Tamanin da Bakwai: 

Rarrabuwar jama’a ga shugaba lokacin sauka a zango da tsakar rana da bayanin neman inuwar itatuwa:

597. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sinan dan Abu Sinan da Abu Salmah cewa: “Lallai Jabir ya ba shi labari.”

598. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari dan Shihab ya ba mu labari daga Sinan dan Abu Sinan Du’aliy cewa: “Lallai Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ba shi labari cewa: “Lallai shi ya fita yaki tare da Annabi (SAW) suna cikin tafiya har tsakiyar wuni haka ya iske su ne a kwari mai itatuwa masu yawan kaya. Sai mutane suka rarraba wajen neman inuwar itace. Annabi (SAW) ya sauka a karkashin wata itaciya ya rataya takwabinsa sa’an nan ya yi barci. Sai ya farka ya ga wani mutum tare da shi bai san da shi ba. Annabi (SAW) ya ce: “Lallai wannan ya dauke takwabina ya ce: “Wane ne zai tsare ka daga gare ni? Na ce, “Allah ne, sai ya mayar da takobin cikin kubensa sai (Annabi) ya mike ya zauna. Sa’an nan bai hukunta shi ba.”

 

Babi na Tamanin da Takwas:

Abin da aka ambata game da masu. An karbo daga dan Umar daga Annabi (SAW) ya ce: “An sanya arzikina a karkashin mashina. Kuma an sanya wulakanci da kaskanci na biyan haraji ga duk wanda ya saba wa umurnina.”

599. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf  ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Nadar bawan  Umar dan Ubaidullahi daga Nafi’u bawan Abu kattada mutumin Madina daga Abu kattada (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai shi ya kasance tare da Manzon Allah (SAW) cikin wata tafiya har sai da muka kasance a daya daga sashen hanyoyin garin Makka. Sai shi (Abu kattada) ya jinkirta shi da abokansa masu Ihrami alhali shi ba ya da Ihrami. Sai ya ga wani jakin dawa ya daidaita bisa godiyarsa. Sai ya roki abokansa da su miko masa bulalarsa sai suka ki. Ya roke su game da mashinsa suka ki. Sai ya tafi ya dauke shi sa’an nan ya kai hari ga jakin ya kashe shi (harbe shi bisa ambaton sunan Allah). Sai wadansu daga cikin sahabban Annabi AS suka ci, wadansu kuma suka ki ci. Lokacin da suka iske Manzon Allah (SAW) sai suka tambaye shi game da haka ya ce: “Abin sani dai abinci ne wanda Allah Ya ciyar da ku game da shi.” An karbo daga Zaid dan Aslam daga Adda’u dan Yassar daga Abu kattada cewa: game da jakin dawa da misalin Hadisin Abu Nadar cewa: (Annabi) ya ce: “Shin ko kuna da sauran namansa?”           

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara