Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 02
Babi na Biyu: Tarayya cikin dukiyar da ta kai a fitar mata da zakka akan yi daidaito wajen fitar zakka:207. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi dan Musanna ya ce, “Babana ya ba ni labari ya ce, Sumamat dan Abdullahi dan Anas ya ce: “Lallai Anas ya ba shi labari cewa, lallai Abubakar Siddik (Allah […]
Babi na Biyu: Tarayya cikin dukiyar da ta kai a fitar mata da zakka akan yi daidaito wajen fitar zakka:
207. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi dan Musanna ya ce, “Babana ya ba ni labari ya ce, Sumamat dan Abdullahi dan Anas ya ce: “Lallai Anas ya ba shi labari cewa, lallai Abubakar Siddik (Allah Ya yarda da su), ya rubuta masa wajibcin zakka wanda Manzon Allah (SAW) ya farlanta ya ce: “Dukan abin da ya kasance na tarayya, to lallai za su rika daidaita abin da za su fitar game da zakka.”
Babi na Uku: Rabon dukiyar ganima:
208. An karbo daga Aliyu dan Hakam mutumin Madina ya ce: “Abu Awanatu ya ba mu labari daga Sa’id dan Masruk daga Ababatu dan Rifa’atu dan Rafi’u dan Khadija daga kakansa ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a Zul-Hulaifa sai yunwa ta shafi mutane lokacin da suka sau rakuma da dukiyar ganima. Mai ruwaya ya ce, “Annabi (SAW) ya kasance yana wani bangare daga jama’ar sahabbai, sai su jama’ar farko suka yi gaggawa suka yanka dabbobinsu suka kafa tukwanen girki. Sai Annabi (SAW) ya iso ya umurta da tukwanen nan aka sauke aka kashe wutar. Sa’an nan ya yi rabo bisa daidaiton tumaki goma a matsayin rakumi daya. Ana cikin haka sai wani rakumi ya kwace da gudu sai (jama’a) suka fita nemansa har sai da suka gajiya, a lokacin dawakai kadanne, sai wani mutum ya hau daya daga cikinsu ya dauki kwarinsa sai ya harbe shi da kyauronsa sai Allah Ya kaddara tsayuwarsa bisa ga haka. Annabi (SAW) ya ce, “Lallai akwai wasu daga cikin dabbobi wadanda suke da halaye irin na dabbobin daji, idan suka yi muku irin wannan hali to ku aikata irin abin da kuka aikatar nan (wato ku harbe su da kibiya).” Sai kakana ya ce: “Lallai mu, mukan yi kaunar haduwa ko kuma tsoron abokan gaba gobe, kuma ga shi ba mu da wukake. Shin za mu iya yanka da iwa ko kyauro? Ya ce, “Abin da ya zubar da jini kuma an ambaci sunan Allah a kansa to ku ci shi. Amma hakori da akaifa (farce) ba abin yanka ba ne da sannu zan ba ku labarinku game da haka, amma kun ga hakori kashi ne, amma akaifa abin yankan mutanen Habasha ne.”
Babi na Hudu: Hada dabino bibbiyu wajen cin abinci a tsakanin mutum biyu ko uku har sai mutum ya nemi izini abokan cinsa:
209. An karbo daga Khallad dan Yahya ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Jabalatu d dan Suhaim ya ba mu labari ya ce, “Na ji dan Umar (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Annabi (SAW) ya hana game da mutumin da ke hada dabino biyu lokacin cin abinci har sai ya nemi izinin abokin cinsa.”
210. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Jabalatu ya ce, “Mun kasance a Madina sai wata shekarar yunwa ta same mu, sai dan Zubair ya rika ciyar da mu abinci da dabino. Kuma dan Umar ya kasance yana shudewa gare mu yana ce mana: Kada ku rika hada dabino biyu lokacin ci. Domin lallai Annabi (SAW) ya hana game da hadamar cin dabino bibbiyu face idan mutum ya nemi izinin dan uwansa (abokin cinsa).”