Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi (1)
Babi na Ashirin da Hudu: “Fitar da masu sabo da masu husuma daga gidaje bayan sanarwa. Hakika Umar ya fitar da ’yar uwan Abubakar lokacin da ta yi kukan mutuwa (daga murya wajen kuka)”: 141. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Muhammad dan Abu Addiyi ya ba mu labari daga Shu’abah daga Sa’ad […]
Babi na Ashirin da Hudu: “Fitar da masu sabo da masu husuma daga gidaje bayan sanarwa. Hakika Umar ya fitar da ’yar uwan Abubakar lokacin da ta yi kukan mutuwa (daga murya wajen kuka)”:
141. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Muhammad dan Abu Addiyi ya ba mu labari daga Shu’abah daga Sa’ad dan Ibrahim daga Humaid dan Abdurrahman daga Annabi (SAW) ya ce; “Hakika na yi himmar zan umarci a yi Sallah idan an tsayar da ita, sai in fita da wasu jama’a zuwa gidajen wasu mutane wadanda ba su halartar Sallar Isha sai in kona (sanya wuta) a kansu.”
Babi na Ashirin da Biyar: Abin da aka samo game da ajiyar takardar wasiyyar mamaci da bayanin wanda ya yi da’awar wasiyya:
142. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Zuhuri daga Urwat daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Abdu dan Zam’atu da Sa’ad dan Abu Wakkas sun yi husuma zuwa ga Manzon Allah (SAW) game da dan kuayngar Zam’atu, Sa’ad ya ce: “Ya Manzon Allah! dan uwana ya yi mini wasiyya idan na iso in duba (nemi) dan Zam’atu in karbe shi saboda cewa, lallai dana ne.” Abdu dan Zam’atu ya ce, “dan uwana ne domin dan kuyangar Babana wanda aka haifa a shimfidar Babana. Sai Annabi (SAW) ya ga kamanni bayyananne da Utbatu, sai (Annabi) ya ce: “Shi (bawa) naka ne, ya Abdu dan Zam’atu, da na shimfida ne jifar dutse kan mazinaci (idan yana da aure), Saudat ki tsare (shakamakanke) kanki daga gare shi.”