Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

BABI NA HUdU:- Darajojin masu jihadi domin daukaka kalmar Allah ana cewa: “Waccan hanyata ce, ko a ce, wannan hanya ta ce (bisa lafazin mace ko namiji). Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce: “Guzzan (jam’I ne) dayansa sh ine gazi. Kuma ya ce: “Ma’anar su ne darajoji watau suna da darajoji.”     483. An karbo […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

BABI NA HUdU:-

Darajojin masu jihadi domin daukaka kalmar Allah ana cewa: “Waccan hanyata ce, ko a ce, wannan hanya ta ce (bisa lafazin mace ko namiji). Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce: “Guzzan (jam’I ne) dayansa sh ine gazi. Kuma ya ce: “Ma’anar su ne darajoji watau suna da darajoji.”

 

  483. An karbo daga Yahya dan Salih ya ce: “Fulaih ya ba mu labari daga Hilal dan Aliyu daga Adda’u danYassar daga Abuhuraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah da ManzonSa kuma ya tsayar da sallah, ya yi azumin Ramadan ya zo hakki ne a kan Allah ya shigar da shi Aljanna, ya yi yakin domin daukaka kalmar Allah ko ya yi zamansa a kasarsa wacce aka haife shi cikinta.” Sai (sahabbai) suka ce: “Ya Manzon Allah! Shin mu bai wa mutane labari (bushara)? Ya ce, “Lallai cikin Aljanna akwai darajoji dari wanda Allah Ya tanadar  ga masu jihadi domin daukaka kalmar Allah. Tsakanin kowace daraja ya kai kamar fadin sama da kasa. Amma idan     zaku roki Allah, to ku roke shi Aljannar Firdaus domin ita ce matsakaiciyar Aljanna kuma ita ce madaukakiyar Aljanna.” Ina tsammanin ya ce: “A samanta Al-arshin Mai Rahama ya ke, kuma daga can ne koramai ke gudana.” Muhammad dan Fulaih ya ce, daga Babansa cewa: “A samansa Al-arshin Mai Rahama yake.”

 

  484. An karbo daga Jarir ya ce: “Abu Raja’u ya ba mu labari daga Samurat ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Na gani a daren jiya wasu mutane biyu sun zo mini suka taka (ta fi) da ni zuwa ga wata itaciya, suka shigar da ni wani gida wanda ya fi kyawo ko ya fi fifita ban taba ganin wanda ya fi shi kyawo ba. Ya ce, “Amma wannan gida, gidan masu shahada ne.”

 

  BABI NA BIYAR:-

  Fita yaki domin daukaka kalmar Allah da safe ko da yammaci. Bisa fadar Annabi (SAW) cewa: “Wurin ajiyar bakar dayanku cikin Aljanna ya fi duniya da abin da  ke cikinta.”

 

 485. An karbo daga Mu’allah dan Asad ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai sammakon fita yaki da safe, ko da yammaci ya fi duniya da abin da  ke cikinta.”

 

 

   486. An karbo daga Ibrahim dan Mundhir ya ce: “Muhammad dan Flaih ya ba mu labari Babana ya ba ni labari Hilal danAliyu daga Abdirrahman dan Abu Amrat daga Abuhuraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Wurin ajiyar bakar dayanku cikin Aljanna shi yaf i alheri daga abin da  rana ta bullo kansa kuma ta buya (wato duniya da abin da  ke cikinta).” Kuma ya ce: “Sammakon zuwa yaki da safe ko da yammaci ya fi alheri ga dukkan abin da  rana ta bulla kansa kuma ta buya.”

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos