Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

487. An karbo daga kabusat ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi),, daga Annabi (SAW) ya ce: “Maraita zuwa yaki da yamma ko da safe ya fi duniya da abin da  ke cikinta.”     BABI NA SHIDA:-     Hurul Ain (matan Aljanna) […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

487. An karbo daga kabusat ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi),, daga Annabi (SAW) ya ce: “Maraita zuwa yaki da yamma ko da safe ya fi duniya da abin da  ke cikinta.”

    BABI NA SHIDA:-     Hurul Ain (matan Aljanna) da siffofinsu. Ana kiransu da sunan masu kyawon gani ta gefe (kaikaice), wato masu tsananin bakin ido, kuma masu tsananin farin ido, (Allah) Ya ce: “Kuma muka aura musu da Huru (‘yan matan Aljanna).”

  488. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Mu’awiyya dan Amru ya ba mu labari daga Is’hak daga Humaid ya ce: “Na ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya karbo daga Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani mutum daga cikin mutane da zai mutum kuma na da alherinsa wurin Allah kamar duniya da abin da  ke cikinta har a ce ya yi gurin ya komo duniya  face wanda aka kashe ta hanyar yaki shi zai yi burin ya komo duniya, domin shi komowarsa duniya zai faranta masa rai ko don a sake kashe shi kashi na biyu, saboda sakamakon da ya gani.” Mai ruwaya ya ce: “Na ji Ansa ya karbo daga Annabi (SAW) cewa: “Maraita (yammaci) wurin daukaka kalmar Allah, ko sammako ya fi alherin duniya da Abin da  ke cikinta. Kuma wurin ajiyar bakar dayanku a Aljanna ko ya ce, ‘wurin bulalar dabbar dayanku ya fi alheri daga duniya da abin da  ke cikinta. Da wata mace daga matan Aljanna za ta leko zuwa ga mutanen duniya da ta haskaka abin da  ke tsakaninsu da kuma ta cika su da kamshi, kuma lullubinda ke kanta ya fi duniya da abin da  ke cikinta alheri.”

   BABI NA BAKWAI:-   Burin mutuwa a fagen yakin daukaka kalmar Allah.

  489. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id dan Musayyib ya ba mu labari cewa: “Lallai Abahuraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunSa ba domin wasu mazaje (mutane) daga cikin mummunai ba wadanda rayukansu ba ya musu  dadi ba idan suka saba gare Ni (zuwa yaki ba). Saboda ban samu abin da  zan dauki nauyinsu ba, da ni, ban zauna a bayan wani yaki ba domin sakamako ga daukaka kalmar Allah. Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunSa da na yi burin fita zuwa yakin daukaka kalmar Allah, sannan aka kashe kuma a sake rayar da ni sannan in fita zuwa yakin daukaka kalmar Allah a kashe ni a rayar da ni sannan aka she ni a sake rayar da ni.”   490. An karbo daga Yusuf  danYakub ya ce: “Saffar ya ba mu labari ya ce, Isma’il dan Ulayyat ya ba mu labari daga Ayyub daga Humaid dan Hilal daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi huduba sai ya ce: “Zaid ya dauki tutar yakin aka kashe shi, sannan Ja’afar ya dauki tutar yaki aka ka she shi, sannan dan Rawah ya dauki tutar yaki aka kashe shi, sanan Khalid danWalid ya dauka ba tare da an nada shi ba aka ci nasara. (Mai ruwaya) ya ce: (Annabi ya ce) “Ba mu fatar haduwa da su nan duniya (saboda masaukinsu a Aljanna ya fi nan duniya).” Mai ruwaya ya ce: “Ba mu fatan haduwarsu a nan duniya saboda masaukin na Aljanna ya fi nan, sai aka ga idanuwansa (Annabi) na zubar da hawaye.” 

  BABI NA TAKWAS:-   Wanda ya fado bisa hanyar zuwa yakin daukaka kalmar Allah shima ya  yi shahada (yana tare da wadanda suka fita yakin kuma aka kashe su). Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sannan kuma mutuwa ta riske shi, to, lallai ne, ladansa ya auku ga Allah…har zuwa karshen (4:100).”   491. An karbo daga Abdullahi danYusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba mu labari daga Muhammad dan Habban daga Anas dan Malik ya karbo daga innarsa hiram ’yar Milhan ta ce: “Annabi (SAW) ya yi barci a wani yini kusa da ni, sannan da ya farka sai ya rika murmushi na ce: “Me ya sanya ka murmushi (dariya)? Ya ce, “Wasu mutane ne daga al’ummata aka nuna mini su suna ketare kogin nan mai launin kore kamar sarkin da ke bisa kujerar sarauta.” Sai ta ce: “Ka rokan mini Allah Ya sanya ni daga cikinsu, sai ya yi (rokan) mata (Allah). Sannan ya sake barci ya aika misalin farko sai ta sake fada masa abin da  ta fadi da farko ya amsa mata misalinsa. Sai ta ce: “Ka rokar mini Allah Ya sanya ni daga cikinsu, sai ya ce: Ke kina daga cikin jama’ar farko. Sai ta fita tare da mijinta Ubbadat dan Samit suna mai nufin yaki a lokacin da musulman farko da suka haye kogin nan tare da Mu’awiyya. Lokacin da suka juyo daga yakinsu suna masu tafiya ayari, sai suka sauka a Sham (Siriya), sai aka kusanto mata da dabba domin ta hau sai (dabbar) ta kayar da ita, ta mutu.”

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos