Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Babi na Ashirin da Uku: Abubuwa nawa ne wadanda aka yi masa wasiyya zai aikata cikin dukiyar maraya. Kuma kamar na wane zai ci, saboda ladar aikinsa a cikin dukiyar maraya?: 461. An karbo daga Harun dan Ash’as ya ce: “Abu Sa’id bawan bani Hashim ya ba mu labari ya ce, Sakhru dan Juwairiyya ya […]
Babi na Ashirin da Uku:
Abubuwa nawa ne wadanda aka yi masa wasiyya zai aikata cikin dukiyar maraya. Kuma kamar na wane zai ci, saboda ladar aikinsa a cikin dukiyar maraya?:
461. An karbo daga Harun dan Ash’as ya ce: “Abu Sa’id bawan bani Hashim ya ba mu labari ya ce, Sakhru dan Juwairiyya ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Umar ya yi sadaka da wata dukiyarsa a zamanin Manzon Allah (SAW) wanda ta kasance a kira da sunan Thamghu kuma ta kasance gonar dabinai ne. Sai Umar ya ce: “Ya Manzon Allah!Hakika ni na bayar da dukiyata wannan sadaka saboda ita na fi so cikin raina, don haka na yi nufin sadaka da ita.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ka yi sadaka da asalinta ba a sayarwa kuma ba a kyautarta kuma ba a gadonta, amma kowa yana iya cin ’ya’yanta.” Sai Umar ya yi sadaka da ita wannan gona domin daukaka kalmar Allah, da bayi da miskinai da baki. Da matafiyi da dangi makusanta, kuma babu laifi ga duk wanda ya shugabance ta ya yi amfani (ya ci) daga gare ta bisa kyautatawa, ko ya ciyar da abokinsa ban da mai tarawa (don tara dukiya).”
462. An karbo daga Ubaidu dan Isma’il ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari daga Hisham daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), game da fassarar wannan aya cewa: “Wanda ya kasance mawadaci ya kame kansa, wanda ya kasance fakiri ya ci bisa kyautatawa.” (k:4:6).” Ta ce, “An saukar da ita ce, ga mai shugabancin maraya ya samu daga cikin dukiyarsa idan yana da bukata ya ci gwargwadon (aikinsa) cikin dukiyar bisa kyautatawa.”
Babi na Ashirin da Hudu: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Lallai wadanda suke cin dukiyar maraya da zalunci suna ci wa cikkunansu wuta ne, da sannu za su konu da wutar Sa’ira (mai kamu)” (k:4:10).
463. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba ni labari daga Sauru dan Zaid Madani daga Abul Ghais daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Ku nisanci abubuwan halaka guda bakwai.” Suka ce, “Mene ne su ya Manzon Allah!” Ya ce, “Hada Allah da wani da sihiri (tsafe-tsafe) da kisan rai wanda Allah Ya katange face da hakki da cin dukiyar riba da cin dukiyar maraya da juya baya (gudu) lokacin yakin da ba a ninka ku uku ba da kazafi ga mata masu aure muminai masu kamun kai.”
Babi na Ashirin da Biyar: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Suna tambayarka game da marayu. Ka ce: “Gyara gare su shi ne ya fi alheri, idan kuka gauraya su (cikin kasuwancinku) to ’yan uwanku ne…har zuwa karshen aya cewa: “Da Ya kallafa muku, kuma Ya kama ku da laifin haka ya kuntata muku.” Domin ma’anar Annata, kaskantarwa. Sulaiman dan Harb ya ba mu labari ya ce, Hammad ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u ya ce: “dan bai taba raddi (kin) shugabantar da wani ba bisa wasiyyarsa ba.” dan Sirin ya kasance abin da ya fi soyuwa gare shi game da dukiyar maraya shi ne yakan tara masu yi masa nasiha da waliyyansa (maraya) domin su duba su ga abin da ya fi alheri (wajen gudanar da al’amarin marayan).” dawus ya kasance idan an tambaye shi game da wani abu na al’amarin marayu sai ya karanto wannan aya cewa: “Allah Shi ne Mafi sanin mai nufin barna da mai nufin gyara…” (k:2:220). Adda’u ya ce: “Game da maraya karami ko babba waliyyinsa zai iya ciyarwa ga kowane mutum gwagwadon rabonsa.”
Babi na Ashirin da Shida: daukar maraya aiki cikin tafiya ko halin zaman gida idan ya kasance haka shi ne ya fi zama maslaha gare shi. Uwa da kishiyar uwa ke da hakkin lura da maraya koda yake ba su ne masu lura da shi ba:
464. An karbo daga Yakub dan Ibrahim dan Kasir ya ce: “dan Ulayyatu ya ba mu labari ya ce, Abdul’aziz ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya iso Madina ba ya da mai yi masa aiki, sai Abu dalha (mijin mahaifiyata) ya rike hannuna ya tafi da ni zuwa ga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah (SAW)! Lallai Anas yaro ne mai hikima, don haka na zo da shi ya rika yi maka hidina (aiki).” Anas ya ce: “Sai na rika yin masa (Annabi) hidima a cikin tafiya ko halin zaman gida. Bai taba ce mini komai ba wanda na aikata shi kamar ko ya ce: “Don me ka aikata wannan kamar haka?” Ko kuma abin da ban aika ta shi ba, ya ce: “Don me ya sa ba ka aika ta wannan ba?”