Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Babi na Ashirin da Bakwai: Idan mutum ya yi sadakar wakafi ta gona amma bai bayyana iyakoki ba, to ya halatta, haka ma hukuncin sadakar da ba gona ba: 465. An karbo daga Abdullahi dan Maslamatu ya ce: “Daga Malik daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha cewa: “Lallai shi, ya ji Anas dan Malik […]
Babi na Ashirin da Bakwai:
Idan mutum ya yi sadakar wakafi ta gona amma bai bayyana iyakoki ba, to ya halatta, haka ma hukuncin sadakar da ba gona ba:
465. An karbo daga Abdullahi dan Maslamatu ya ce: “Daga Malik daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha cewa: “Lallai shi, ya ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Abu dalha ya kasance ya fi mutanen Madina yawan gonakin dabinai. Kuma ya kasance fiyayyiyar dukiyarsa da ya fi so ita ce wadda take Bairuha’u ta wajen alkiblar Masallaci. Annabi (SAW) ya kasance yana shigarta ya sha daga ruwanta, a cikinta akwai idon ruwa mai kyau. Anas ya ce: “Lokacin da wannan aya ta sauka cewa: “Ba za ku samu hakikanin da’a (Aljanna) ba, har sai kun ciyar daga abin da kuke so…” (k:2:92). Sai Abu dalha ya mike ya ce: “Ya Manzon Allah! Hakika Allah Yana cewa: “Ba za ku samu hakikanin da’a ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so…” to lallai ni, dukiyar da na fi so a gare ne, ita ce wadda take Bairuha’u, na mika ta sadaka saboda Allah, ina kaunar ladanta da tanadin ladanta a wurin Allah. Ka sanya (raba) ta duk inda Allah Ya nuna maka haka.” Sai (Annabi) ya ce: “Madallah da jarumi! Wannan dukiya ce mai riba, ko ya ce, mai albarka,” Maslamah ya yi shakka (kokwanto). Annabi ya ce: “Lallai na ji abin da ka ce, amma ina ganin ka raba ta ga danginka makusanta.” Sai Abu dalha ya ce; “Zan aikata haka ya Manzon Allah! Sai Abu dalha ya raba ta cikin danginsa makusanta har da ’ya’yan baffaninsa.” Isma’il da Abdullah dan Yusuf da Yahya dan Yahya sun ce: “Daga Malik cewa: “Dukiya ce mai riba (wadda aka sarrafa ta ta hanyar Allah).”
466. An karbo daga Muhammad dan Abdurrahim ya ce: “Rauhu dan Ubadah ya ba mu labari ya ce, Zakariyya dan Is’hak ya ba ni labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari daga Ikramah daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai wani mutum ya ce da Manzon Allah (SAW), lallai mahaifiyarsa ta rasu, shin zai amfane ta idan ya yi mata sadaka? Ya ce, “Na’am,” ya ce, “Lallai dukiyata na Makhramah ina shaida maka hakika ni, na sadakar da ita, saboda ita (mahaifiyata).”
Babi na Ashirin da Takwas:
Idan wadansu jama’a suka yi sadakar wakafin gona haka ya halatta:
467. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari daga Abu Tayyah daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya umurci da a gina masallaci. Sai ya ce: “Ya kabilar Najjar ku sanya mini kudin gonakinku wadannan.” Sai suka ce: “A’a, wallahi ba mu neman kudinsu daga gare ka face wurin Allah (wato muna neman sakamakonsu wurin Allah, don haka suka bayar domin Allah).”
Babi na Ashirin da Tara:
Bayanin sadakar wakafi da yadda ake rubutawa:
468. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari ya ce, dan Aunu ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Umar ya samu wata gona a Khaibara, sai ya tafi ga Annabi (SAW) ya ce: “Na samu wata kasa a Khaibara ban taba samun wata dukiya kamarta ba, wadda nafi so, kuma zan yi sadakar wakafi da ita. To me za ka umarce ni da aikatawa? Ya ce, “Idan ka so sai ka tsare (rike) asalinta ka yi sadaka da ita. Sai Umar ya yi sadaka ita bisa cewa; ba a sayar da asalinta, kuma ba a kyautarta, kuma ba a gadonta, amma dai ana ciyar da ’ya’yanta ga talakawa da makusanta da bayi da daukaka kalmar Allah da baki da matafiya, kuma babu laifi ga wanda ke shugabancinta ya ci daga gare ta bisa kyautatawa, ko ya ciyar da abokinsa ba wanda ke tara dukiya da ita ba.