Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

  Babi na Uku: Yin wasiyya da daya cikin uku na dukiya. Alhasanul Basari ya ce: “Wasiyya ba ta halatta ga kafirin amana face daya cikin uku. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ka yi hukunci a tsakaninsu da Littafin Allah… (k:5:49).” 441. An karbo daga kuitaiba dan Sa’id ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

 

Babi na Uku:

Yin wasiyya da daya cikin uku na dukiya. Alhasanul Basari ya ce: “Wasiyya ba ta halatta ga kafirin amana face daya cikin uku. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ka yi hukunci a tsakaninsu da Littafin Allah… (k:5:49).”

441. An karbo daga kuitaiba dan Sa’id ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Hisham dan Urwatu daga Babansa daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Da dai mutane sun rintsa (rage) wasiyyarsu zuwa daya cikin hudu. Domin lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “daya cikin uku, daya cikin uku na da yawa.”

442. An karbo daga Muhammad danAbdurrahim ya ce: “Zakariyya’u dan Addiyu ya ba mu labari ya ce: “Marwan ya ba mu labari daga Hashim dan Hashim daga Amir dan Sa’ad daga Babansa (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na yi rashin lafiya sai Annabi (SAW) ya zo gaishe ni, sai na ce: “Ya Manzon Allah! Ka rokan mini Allah kada Ya mayar da ni bisa duga-dugaina (kada in mutu a garin da na yi kaura daga gare ta, wato Makka).” Sai (Annabi) ya ce: “Ina fatar Allah zai daukaka (maka tsawon kwana), Ya amfanar da wadansu mutane.” (Sa’ad) ya ce: “Ina son in yi wasiyya, saboda ’yata daya ce a gare ni, na ce: “Na yi wasiyyar sadaka da rabin dukiyata.” Sai ya ce, mini: “Rabi na da yawa.” Na ce, “daya cikin uku.” Ya ce: “daya cikin uku! daya cikin uku na da yawa.” ya ce: “Daga nan sai mutane suka rika yin wasiyya da daya cikin uku na dukiyarsu; sai ya halatta musu haka.”

Babi na Hudu: Maganar mai wasiyya ga wanda aka yi wasiyyar bisa cewa: “Ka kula mini da dana.” Da bayanin abin da ke halatta ga wasiyya daga wanda ke da’awa (kara):

443. An karbo daga Abdullahi dan Maslamah ya ce: “Daga Malik daga dan Shihab ya ce, daga Urwatu dan Zubair daga A’isha matar Annabi (SAW) (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai ita ta ce: “Utbatu dan Abu Wakkas ya kasance ya yi alkawari (wasiyya) zuwa ga dan uwansa Sa’ad dan Abu Wakkas cewa: dan baiwar Zama’atu nawa ne ka karba mini shi. Lokacin Fatahu Makkah sai Sa’ad ya karbe shi ya ce: “dan dan uwana ne, wanda ya kasance ya yi mini alkawarinsa gare ni.” Sai Abdu dan Zama’atu ya mike ya ce: “dan uwana ne, dan baiwar Babana, wanda aka haifa bisa shimfidarsa. Sai suka kai kara zuwa ga Manzon Allah (SAW). Sa’ad ya ce: “Ya Manzon Allah, dan dan uwana ne, wanda ya yi mini alkawarinsa (wasiyyarsa).” Sai Abdu dan Zama’atu ya mike ya ce: “Shi dan uwana ne, dan baiwar Babana.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Shi naka ne, ya Abdu dan Zama’atu, saboda da wanda aka haifa bisa shimfida shi ne da. Amma mai zina sai jifa kadai a kansa.” Sa’an nan ya ce, wa Saudatu: “Ki rika sanya hijabui a tsakaninki da shi lokacin da ya ga kamanninsa da Utbatu, bai taba ganinta ba har ya hadu da Allah (mutuwa).”

Babi na Biyar: Idan mara lafiya ya yi nuni da kansa to ya zama shaida bayyananniya wanda ake fahimta (a yi hukunci da ita):

444. An karbo daga Hassan dan Abu Abbad ya ce: “Hammam ya ba mu labari daga kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Hakika wadansu Yahudawa sun taba rotsa kan wata baiwa a tsakanin duwatsu biyu. Sai aka ce mata: “Wa ya aikata miki haka? Shin wane ne? Har sai da aka ambaci sunan Bayahuden nan, sai ta yi nuni da kanta, aka zo da shi bai gushe bisa tuhuma ba har sai da ya yi furuci. Annabi (SAW) ya umurta aka rotse (fashe) kansa da duwatsu.”