Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

BABI NA ISHIRIN DA dAYA:-Abinda aka ambata game halayen mutane cikin mu’amalarsu da husumarsu tsakanin Musulmi da Yahudawa.132. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abdul Malik danMaisarat ya ba ni labari ya ce: “Na ji Nazzal danSairat ya ce, na ji Abdullahi ya ce, na ji wani […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

BABI NA ISHIRIN DA dAYA:-
Abinda aka ambata game halayen mutane cikin mu’amalarsu da husumarsu tsakanin Musulmi da Yahudawa.
132. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abdul Malik danMaisarat ya ba ni labari ya ce: “Na ji Nazzal danSairat ya ce, na ji Abdullahi ya ce, na ji wani mutum ya karanta wata aya, ya ce, na ji daga Annabi (S.A.W) bisa sabanin haka sai na kama hannunsa na tafi da shi zuwa ga Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce: “Dukkanku kuna kan daidai,” Shu’aba ya ce, “Ina tsammaninsa ya ce, “Kada ku rika sabani domin hakika wadanda ke gabaninku sun saba ne sai suka halaka.”
133. An karbo daga Yahya dankaza’at ya ce: “Ibrahim danSa’ad daga danShihab daga Abi Salmat da Abdurrahman A’araji daga Abihuraira Allah ya yarda da shi ya ce: Wasu mutane biyu sun taba zagin junansu, daya daga cikin Musulmai kuma dayan daga Yahudawa. Sai Musulmin ya ce, “Ina rantsuwa da wanda ya zabi Muhammad (AS) bisa halittu, sai Bayahuden ya ce, “Ina rantsuwa da wanda ya zabi Musa akan halittu, sai Musulmin ya daga hannunsa ya mari fuskar Bayahuden nan saboda fadin haka. Sai Bayahuden ya tafi zua ga Annabi (S.A.W) ya ba shi labari da abinda ya kasance game da al’amarinsa da Musulmin nan. Sai Annabi (S.A.W) ya kira Musulmin ya tambaye shi game da haka ya ba shi labari. Annabi (S.A.W) ya ce, “Kada ku fifitani akan Musa, domin lallai mutane zasu mace (suma) rana kiyama, sai in suma tare da su kuma sai in kasance farkon wanda ya farka. Sai in iske Musa na rumgume da gefen Al’arshi ban sani ba shin ko ya kasance tare da wadanda suka suma sai dai ya riga ni farkawa ko kuwa a’a ya kasance ne daga wadanda Allah ya yi togiya kansu.” (Ma’anar shine Allah ya ce: “Idan aka yi busa cikin kaho dukkan abinda ke cikin sama da kasa sai su mutu (suma) face wadanda Allah Ya so 39:68).
134. An karbo daga Musa danIsma’il ya ce: Wuhaib ya ba mu labari ya ce, Amru danYahya ya ba mu labari daga Babansa daga Sa’id Alkhudri Allah ya yarda da shi ya ce: “Wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune sai wani Bayahude yazo ya ce, “Ya Abal kasim wani mutum daga sahabbanka ya bugi fuska ta,” sai (Annabi) ya ce, “Wane ne? ya ce, “Wani mutum daga mutanen Madina,” (Annabi) ya ce: “Kira shi,” da yazo (Annabi) ya ce: “Shin ka buge shi? Ya ce, “Na ji shi ne acikin kasuwa yana rantsuwa da cewa: ya rantse da wanda ya zabi Musa akan mutane,” sai na ce, “Kai daddauda! Har da Muhammad S.A.W? Sai fushi ya kama ni sai na bugi (mari) fuskarsa.” Sai Annabi (S.A.W) ya ce, “Kada ku rika fifitawa tsakanin Annabawa lallai mutane zasu suma (mutu) ranan kiyama, sai in kasance nine farkon wanda kasa ta ke ce mashi ya fito, sai na iske Musa na rike da wani ginshikI daga ginshikan Al’arshi, ban sani ba shin ko ya mutu ko kuwa anyi mashi hisabi bisa sumar da yayi ta farko (kamar yanda yake cikin Al-kur’ani lokacin da Musa ya nemi ganin Allah, sai ya fadi sumamme).”
135. An karbo daga Musa ya ce: “Hammamu ya ba mu labari daga katada daga Anas Allah ya yarda da shi cewa: Hakika wani Bayahude ya taba rotsa kan wata kuyanga a tsakanin duwatsu biyu, sai aka ce: Wa ya aikata miki haka? Shin wane da wane ne? Har  sai da aka ambaci sunan wan nan Bayahude sai tayi nuni da kanta cewa shi ne,” Sai aka kamo Bayahuden ya tabbatar sai Annabi (S.A.W) ya umurta da shi aka rotse kansa a tsakanin duwatsu biyu.”