Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Babi na Casa’in da Shida: Abin da aka ambata game da yakin masu sanya takalmar gashi (dangarafai): 616. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Zuhuri ya ce, daga Sa’id dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “kiyama ba […]
Babi na Casa’in da Shida: Abin da aka ambata game da yakin masu sanya takalmar gashi (dangarafai):
616. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Zuhuri ya ce, daga Sa’id dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “kiyama ba za ta tsayu ba face kun yaki wadansu mutane takalmansu (dangarafi) na gashi ne. Kuma kiyama ba za ta tsayu ba face kun yaki wadansu jama’a fuskarsu kamar garkuwa da aka rufe da jemammiyar fata.” A wata ruwaya daga Abu Huraira ta ce: “Masu kananun idanuwa, masu shafaffen hanci, fuskarsu kamar garkuwa da aka rufe da jemammiyar fata.”
Babi na Casa’in da Bakwai: Wanda ya jera (sahu) sahabbansa lokacin karayar yaki. Da bayanin sauka bisa dabbarsa tare da neman taimakon Allah:
617. An karbo daga Amru dan Khalid Alharrani ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari ya ce, na ji Barra’u wani mutum ya tambaye shi cewa: “Shin ko kun gudu a Ranar Yakin Hunain ya Abu Umarata? Ya ce,“A’a wallahi Manzon Allah (SAW) bai gudu ba, amma lallai shi lokacin da matasa daga sahabbansa suka rika fitowa ba su da makamai tare da su. Sai suka yi wa kabilar Hawazin da Bani Nasar kawanya marhaba wadanda ba su kuskure wajen harbin kibau, suka rika harbinsu. Sai Musulmi suka yiwo ta wajen Annabi (SAW) lokacin yana bisa alfadararsa fara. Tare da shi da dan Baffarsa Abu Sufiyan dan Haris dan Abdulmudallib yana janye da shi. Sai ya sauka ya nemi taimakon Allah. Sa’an nan ya rika cewa: “Lallai ni ne Annabin ba karya ba ne. Ni ne dan Abdulmudallib, sa’an nan ya sanya sahhabansa cikin sahu.
Babi na Casa’in da Takwas: Addu’a a kan mushirikai lokacin karayar yaki ko idan aka firgita:
618. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Isa ya ba mu labari daga Hisham daga Muhammad daga Ubaidatu daga Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Lokacin da Yakin Ahzab ya kasance Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ya cika gidajensu da kaburburansu da wuta, saboda sun shagaltarda mu game da Sallar La’asar har zuwa buyar rana (Yana nufin kafiran da ake yaki da su)”.
619. An karbo daga kabisatu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Zakawan daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana addu’ar kunuti da cewa: “Ya Allah! Ka tserar da Salmata dan Hisham, Allah Ka tserar da Walid dan Walid. Allah Ka tserar da Ayyash dan Rabi’atu; Allah Ka tserar da raunana daga cikin mummunai. Allah Ka tsananta azabarKa bisa kabilar Mudar. Allah Ka sanya musu fari (rashin ruwa) kamar yadda Ka sanya wa mutanen Annabi Yusuf (AS).”
620. An karbo daga Ahmad dan Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Isma’il dan Abu Khalid cewa: “Lallai shi ya ji Abdullahi dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi addu’a a kan mushirikai a Ranar Yakin Ahzab ya rika cewa: “Ya Allah! Mai saukar da Littafi, Mai gaugawar hisabi, Ya Allah! Ka karya kungiyar kafirai, Ya Allah! Ka karya su, Ka girgiza su (firgita su).”
621. An karbo daga Abdullahi dan Abu Sahiba ya ce: “Ja’afar dan Aunu ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga Abu Is’hak daga Amru dan Maimun ya ba mu labari daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana Sallah a cikin inuwar Ka’aba. Sai Abu Jahil da wasu jama’a daga kabilar kuraishawa tare da shi suka ce: “An soke taguwar a wani bangare daga cikin Makka, sai suka aika aka zo da kayan cikinta suka dora a kansa (Annabi SAW). Sai Fadima (RA) ta zo ta ture shi daga gare shi. Sai (Annabi SAW) ya ce: “Ya Allah! Na bar ka da kuraishawa (Ka hallaka su). Ya Allah! Na bar ka da kuraishawa, Ya Allah! Na bar ka da kuraishawa: Ya Allah! Na bar ka (ka hallaka) Abu Jahil. Na bar ka da Utbatu dan Rabi’ata. Na bar ka da Shaibatu dan Rabi’ata. Na barka da Walid dan Utbatu. Na bar ka da Ubayyu dan Khalf. Na bar ka da Ukbah dan Mu’aid.” Abdullahi ya ce: “Hakika na gan su an hallaka su cikin rijiyar Badar suna matattu.”
Sha’aban: