Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 2

Babi na Hudu: Wanda ya nemi a shayar da shi. Sahal ya ce, “Annabi (SAW) ya ce mini: “Shayar da ni (ban ruwa in sha)”:284. An karbo daga Khalid dan Makhlad ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu labari ya ce, Abu duwalatu ya ba mu labari ya ce, “Na ji Anas (Allah Ya […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 2
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 2

Babi na Hudu: Wanda ya nemi a shayar da shi. Sahal ya ce, “Annabi (SAW) ya ce mini: “Shayar da ni (ban ruwa in sha)”:
284. An karbo daga Khalid dan Makhlad ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu labari ya ce, Abu duwalatu ya ba mu labari ya ce, “Na ji Anas (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya zo gidanmu wannan ya nemi a ba shi ruwa sai muka tatsar masa wata tunkiyarmu. Sa’an nan na jawo masa ruwa daga rijiyarmu wannan na mika masa, lokacin Abubakar na gefensa na hagu, Umar na fuskantarsa wani Balaraben kauye na gefen damarsa. Lokacin da ya kare sha, Umar ya ce, “Ga Abubakar nan, sai (Annabi) ya mika wa Balaraben kauyen nan sauransa sa’an nan ya ce: “(mutumin da) ke bangaren dama shi ne ya fi cancanta, ya fadi haka har sau biyu, sai ya ce, “Ku rika farawa da dama.” Anas ya ce, “Wannan ita ce, Sunnar (Annabi), sau biyu ko sau uku.”
Babi na Biyar: Hukuncin karbar kyautar dabbar farauta. Annabi (SAW) ya karbi damtse daya daga Abu kattada:
285. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Hisham dan Zaid dan Anas dan Malik daga Anas (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Mu tashi wani zomo a wurin Marra-Zahran mutane suka bi shi har suka gaji, sai na iske shi na kama, na zo da shi ga Abu dalha ya yanka shi. Ya aika zuwa ga Manzon Allah (SAW) da katara ko cinya. Ya ce, “Cinya ce babu shakka cikinsa, sai (Annabi) ya karbe shi.” Na ce, “Shin ya ci wani abu daga gare shi? Ya ce, “Ya ci daga gare shi.” Sa’an nan ya ce, daga baya ya karbe shi.
Babi na Shida: Hukuncin karbar kyauta:
286. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utba dan Mas’ud daga Abdullahi dan Abbas daga Sa’ab dan Jassamah (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai an yi wa Manzon Allah (SAW) kyautar jakin dawa (wanda aka samo daga farauta), sai ya ki karba, lokacin da (Annabi) ya ga kamar ransa ya baci. Sai ya ce, “Amma ka sani lallai mu, ba muki karbar maka wannan kyauta ba, face don mu muna cikin Ihrami.”
Babi na Bakwai: Karbar kyauta:
287. An karbo Ibrahim dan Musa ya ce: “Abdatu ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai mutane sun kasance suna kirdadon (neman dacewa) da kyautarsu ga yini A’isha wadda suke nema da ita. Ko ya ce, “Wanda suke neman yardar Manzon Allah (SAW) da ita.”
288. An karbo daga Adamu ya ce “Shu’aba ya ba mu labari ya ce, Ja’afar dan Iyas ya ba mu labari ya ce, “Na ji Sa’id dan Jubair ya ce, daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce “Ummu Hufaid innar dan Abbas ta taba ba Annabi (SAW) kyautar cuku da mai da naman damo. Sai Annabi (SAW) ya ci cuku da mai ya bar naman damo don kyama.” dan Abbas ya ce, “Kuma an ci a teburin Manzon Allah (SAW) da dai haramun ne da ba a ci a bisa a teburin Manzon Allah (SAW) ba.”
289. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Ma’nu ya ba mu labari ya ce, Ibrahim dan dahman ya ba mu labari daga Muhammad dan Ziyad daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance idan aka zo da abinci yakan tambaya game da shi cewa: Shin kyauta ne ko sadaka? Idan aka ce ta sadaka ce, yakan ce wa sahabbansa ku ci shi bai ci. Idan aka ce, kyauta ne sai (SAW) ya sanya hannunsa ya ci tare da su.”