Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Dari da Saba’in da Tara: Bisa fadar Annabi (SAW) ga Yahudawa: “Ku musulunta, ku tsira.” Makburi ya fade shi daga Abu Huraira.   Babi na Dari da Tamanin: Idan wadansu jama’a suka musulunta a gidajen yaki. Kuma alhali suna da dukiya da kasa to tasu ce: 10. An karbo daga  Mahmud ya ce: […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Dari da Saba’in da Tara: Bisa fadar Annabi (SAW) ga Yahudawa: “Ku musulunta, ku tsira.” Makburi ya fade shi daga Abu Huraira.

 

Babi na Dari da Tamanin:

Idan wadansu jama’a suka musulunta a gidajen yaki. Kuma alhali suna da dukiya da kasa to tasu ce:

10. An karbo daga  Mahmud ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari daga Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Aliyu dan Husain daga Amru dan Affan daga Usamatu dan Zaid ya ce: “Na ce, “Ya Manzon Allah! Shin gobe ina za ka sauka a Hajjinsa? Ya ce: “Shin Akilu ya bar mana wani gida ne? Sai ya ce: “Lallai gobe mu, masu sauka a farfajiyar (kwarin) kabilar Kinanata  Muhassab inda Kuraishawa suka yi rantsuwa bisa kare kafirci. Saboda Bani Kinanata sun rantsar da Kuraishawa bisa ga Bani Hashim aka ba za su yi ciniki da su ba, ba za su ba su masauki ba.” Zuhuri ya ce: “Khaif sunan wani kwari ne.”

11. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Zaidu dan Aslam daga Babansa cewa: Lallai Umar ya taba sanya wani bawansa aiki wanda ake kira da sunan Hunayya bisa kiwon dabbobin sadaka. Ya ce: “Ya Hunayya ka tara fika-fikan game da aikin Musulmi, kuma ka ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta. Domin lallai addu’ar wanda aka zalunta karbabbiya ce. Ka kyale wadanda ke da taguwa kadan da wadanda ke da tumaki marasa yawa su yi kiwo tare da kai. Amma ka kyale ni da tumakin Abdurrahman dan Auf ko tumakin Usman dan Affan, saboda su idan tumakinsu suka hallaka suna da gona da dabinai. Amma fa masu taguwar nan kadan da tumaki kadan idan nasu suka hallaka, mai kara zai zo gare ni da kukan cewa: “Ya Sarkin Muminai! Ya Sarkin Muminai! Shin za ka kyale su da ni suna cewa: An tozartar da dabbobinsu sun hallaka, ban ko kula ba? Lallai ka sani ruwa da makiyaya sun fi mini sauki a kan zinare da azurfa. Ina rantsuwa da Allah, lallai yin haka za ku ga na zalunce su, saboda nan garinsu ne. Sun yi mata yaki a Jahiliyya, kuma suka musulunta a cikinta. Ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunSa ba domin dukiyar da na dauka don yakin daukaka kalmar Allah na dauki lamunin tsaro ba, da ban dauki lamunin tsaron wata kasa ba daga garinsu ko da kamar taki guda.”

 

Babi na Dari da Tamanin da Daya:

Lissafa yawan jama’a ga shugaba:

12. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga A’amashi  daga Abu Wa’il daga Huzaifa (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Ku lissafa mini yawan wadanda ke fadin kalmar shahada (Musulmi). Muka rubuta masa kamar mutum dubu da dari biyar. Muka ce: “Shin muna jin tsoro ne, alhali mun kai dubu da dari biyar? To, kuwa hakika na ganmu an jarrabe mu, har sai da muka kai mutum bai iya Sallah shi kadai (a boye) saboda tsoro.”

13. An karbo daga Abdan ya ce: “Daga Abu Hamzat daga Ama’ashi da muka bincika sai muka gan mu kamar mutum dari biyar muke.” Abu Mu’awiya ya ce: “Mun kai kamar mutum dari shida zuwa dari bakwai.”

14. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Dan Juraij daga Amru dan Dinar daga Abu Ma’abad daga Dan Abbas (Allah Ya yarda da su),, ya ce: “Wani mutm ya zo ga Manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai ni an rubuta ni zuwa yakin wuri kaza-da-kaza kuma ga matata za ta tafi aikin Hajji. Sai (Annabi) ya ce: “Koma ka yi Hajji da  matarka.”

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara