Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 21
255. An karbo daga dan Abu Maryam ya ce: ‘Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, Urwatu ya ambata cewa: “Lallai Marwan da Miswar dan Makhramat ya ba shi labara cewa: Hakika Annabi (SAW) ya mike lokacin da tawagar kabilar Hawazin suka zo masa, suka tambaye (roke) shi da ya […]
255. An karbo daga dan Abu Maryam ya ce: ‘Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, Urwatu ya ambata cewa: “Lallai Marwan da Miswar dan Makhramat ya ba shi labara cewa: Hakika Annabi (SAW) ya mike lokacin da tawagar kabilar Hawazin suka zo masa, suka tambaye (roke) shi da ya mayar musu da dukiyarsu da kamammun yakinsu (fursunonin yaki). Sai (Annabi) ya ce: “Lallai abin da ke tare da ni kuke gani, kuma fiyayyiyar magana gare ni wadda aka fi gaskiya cikinta., sai dai ku zabi dayan abubuwan nan biyu: Ko dai a mayar muku da dukiyar ko fursunonin yaki. Kamar yanda kuka ga na jinkirta rabonsu, kuma Annabi (SAW) ya kasance ya rika dakonsu (saurararon zabinsu) har darare goma sha, lokacin da ya tafi zuwa da’ifa. Lokacin da ya bayyana musu cewa, lallai Annabi (SAW) bai mayar musu da dukkan abin da suka bukata ba face daya cikin biyu sai suka ce, “To hakika mu, mun zabi fursunonin yaki.” Sai Annabi (SAW) ya mike cikin mutane ya yi wa Allah yabo da abin da Ya cancanta da shi. Sa’an nan ya ce: Bayan haka, lallai ’yan uwanku sun zo mana, suna masu tuba kuma hakika ni, na ga abin da ya kamata zan mika musu kamammun yakinsu, wanda ya ga yana son aikata haka, to ya aika ta, wanda ya ga ba zai iya aikata haka ba, yana son rabonsa za mu ba shi rabonsa daga abin da Allah Ya ba mu na dukiyar ganima, to shi ma yana iya aikata haka. Sai mutane suka halatta maka ka aikata dukkan abin da ka so (ya Manzon Allah). Sai (Annabi) ya ce, “Lallai mu ba mu san wanda ya yi izini da wanda bai yi izini ba daga cikinku. Ku koma har sai kun turo mana manyan masananku (shugabanninku), mutanen suka koma ga masanansu suka yi musu magana (izini). Sa’an nan suka komo zuwa ga Annabi (SAW) da labari cewa, sun yarda kuma sun yi izini. Wannan shi ne abin da ya iso gare shi game da labarin tawagar Hawazin.” Anas ya ce, “Abbas ya ce, ga Annabi (SAW) cewa: “Na fanshi kaina, na fanshi Akil…har zuwa karshe kamar yanda ya gabata.”
256. An karbo daga Aliyu dan Husain ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari, ya ce, dan Aunu ya ba mu labari, ya ce: “Na rubuta takarda zuwa ga Nafi’u sai ya rubuto mini da amsar takarda da cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya kai hari ga kabilar Musdalak lokacin da ba su shirya ba. Alhali su suna masu hari (boye) da dabbobinsu a wurin shayar da dabbobi. Sai aka kashe mayakansu aka kama fursunonin yakinsu na zuriyarsu. A nan ne (Annabi) ya samu Juwairiyyatu, da wannan Abdullahi dan Umar ya ba ni labari haka ya kasance a wannan yaki.”
257. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Rabi’atu dan Abu Abdurrahman daga Muhammad dan Yahya dan Habban daga dan Muhairiz ya ce: “Na ga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi), sai na tambaye shi sai ya ce: “Mun fita tare da Manzon Allah (SAW) a yakin Musdalik sai muka samu ganimar fursunonin yaki Larabawa. Sai muka rika sha’awar mata har balagarmu ta yi tsanani muna zubar da miniyyi, sai muka so da dai mu rika yin azalu (rashin zubar da miniyyi cikin farjin mace). Sai muka tambayi Manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Abin da ya fi muku kyawo kada ku aikata haka, domin kuwa babu wata rai wadda za ta kasance zuwa Ranar kiyama face ta kasance kafin haka.”
258. An karbo daga Zuhair dan Harb ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Umaratu dan ka’ka’u daga Abu Zur’atu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Ban gushe ba ina son kabilar Bani Tamim.” Ya ce, “dan Sallam, ya ba mu labari ya ce, Jarir dan Abdulhamid ya ba mu labari daga Mughiratu daga Haris daga Abu Zur’atu daga Abu Huraira, daga Umaratu daga Abu Zur’atu daga Abu Huraira ya ce: “Ban gushewa ina son Bani Tamim tun kamar shekara uku, don na ji Manzon Allah (SAW) yana magana game da su. Kuma na ji shi (Annabi) yana cewa: “Su ne suka fi tsanani (fitina) cikin al’ummta fiye da Dujjal.” Ana nan wata rana sai ga sadakokinsu sun zo sai Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘Waccan nan, sadakokin mutanenmu ne, lokacin da wata baiwa fursunar yakin cikinsu ta kasance a wurin A’isha, sai (Annabi) ya ce: “Ki ’yantata domin lallai ita, tana daga cikin ’ya’yan (zuriyar) Isma’il (A.S).