Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Bakwai: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Lallai kaso daya cikin biyar na ganimar yaki na Allah ne da ManzonSa….”(K: 8:41). Har zuwa karshen aya, tana nufi Manzon Allah (SAW) yana iya raba ta ga duk wanda ya so. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ni mai rabawa ne, mai tsaro, kuma Allah ne […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Bakwai:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Lallai kaso daya cikin biyar na ganimar yaki na Allah ne da ManzonSa….”(K: 8:41). Har zuwa karshen aya, tana nufi Manzon Allah (SAW) yana iya raba ta ga duk wanda ya so. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ni mai rabawa ne, mai tsaro, kuma Allah ne Mai bayar da arziki.”

An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Sulaiman da Mansur da Kattada lallai su sun ji Salim dan Abu Ja’ad ya karbo daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), cewa, lallai shi ya ce: “An taba haihuwar wani yaro ga wani mutum daga cikin mu mutanen Madina. Sai ya yi nufin ya sanya masa suna: Muhammad.” Shu’abah ya ce daga Mansur a cikin hadisinsa ya ce: “Sai na dauke shi bisa kafadata, na tafi da shi zuwa ga Annabi (SAW).” Amma cikin Hadisin Sulaiman ya ce: “An haifa masa yaro sai ya yi nufin ya sanya masa suna Muhammad. (Annabi SAW) ya ce: “Ku sanya suna da irin sunana, amma kada ku yi alkunya da irin alkunyata (lakabin Baban Kasim), saboda lallai ni an sanya ni mai rabo, don in rika rabo a tsakaninku.” Husain ya ce: (Annabi) ya ce: “Saboda an aiko ni mai rabo ne kuma don in rika yin rabo a tsakaninku.” Amru ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Kattada ya ce: Ya ji daga Salim daga Jabir ya ce: “(Mutumin) ya yi nufin sanya wa dansa suna Alkasim, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku sanya suna da irin sunana, amma kada ku yi alkunya da irin alkunyata.”

64. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga A’amashi daga Salim dan Abu Ja’ad daga Jabir dan Abdullahi mutumin Madina (Allah Ya yarda da su), ya ce: “An taba haihuwar mana wani yaro ga wani mutum ya sanya masa suna Alkasim. Sai mutanen Madina suka rika cewa: “Ba za mu rika kiranka da Baban Kasim ba. Kuma ba za ka samu ni’imar wannan kalma ba.” Sai ya tafi ga Annabi (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah! An haifa mini wani yaro na sanya masa suna Kasim sai mutanen Madina suka rika cewa: “Ba za mu kira ka Baban Kasim ba,  kuma ba za ka samu ni’imar wannan kalma ba.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Mutanen Madina sun kyauta! Ku rika sanya suna da irin sunana, amma kada ku yi alkunya da irin alkunyata saboda ni ne Kasim (mai rabo).”

65. An karbo daga Habban dan Musa ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari daga Yunus daga Zuhuri daga Humaid dan Abdurrahman cewa: Lallai shi ya ji Mu’awiyya yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda Allah Ya nufe shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini. Kuma Allah ne Mai bayarwa, ni mai rabawa ne kadai. Wannan al’umma ba za ta gushe ba bisa rinjaye a kan duk wanda ya saba mata har al’amarin Allah ya zo suna masu rinjaye.” Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “In ba ku wani abu ko in hana muku, ni dai mai rabo ne kadai. Ina sanyawa ne inda aka umarce ni.”

66. An karbo daga Abdullahi dan Yazid ya ce: “Sa’id dan Abu Ayyub ya ba mu labari ya ce, Abul Aswad ya ba ni labari daga Abu Iyash sunansa Nu’aman daga Khaulatu mutumiyar Madina (Allah Ya yarda da ita). Ta ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Lallai wadansu maza za su rika kutsawa (batarwa) cikin dukiyar Allah ba tare da hakkinta ba. Lallai suna da wuta a kansu Ranar Kiyama.”

 

Babi na Takwas:

Bisa fadar Annabi (SAW) cewa: “An halatta mini ganimomi,” da fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah Ya yi muku wa’adin wasu ganimomi masu yawa wadanda za ku karbe su…” (K:48:20). Wannan aya tana karantarwa ga dukan jama’a ne face abin da Annabi (SAW) ya bayyana shi.

67. An karbo daga Musaddad ya ce: “Khalid ya ba mu labari ya ce, Husain ya ba mu labari daga Amir daga Urwatu Albarikiyyu (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Dawakin da aka tanada (kiwata) saboda yakin daukaka kalmar Allah akwai alheri bisa goshinsu. Akwai lada da samun ganima har zuwa Ranar Kiyama.”

 

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano