Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 27

Babi na Goma Sha Takwas: Idan mai aikin dayanku ya zo masa da abincinsa yaya zaiyi?:271. An karbo daga Hajjaju dan Minhal ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Ziyad ya ce, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Idan dayanku bawansa ya zo […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 27
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 27

Babi na Goma Sha Takwas: Idan mai aikin dayanku ya zo masa da abincinsa yaya zaiyi?:
271. An karbo daga Hajjaju dan Minhal ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Ziyad ya ce, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Idan dayanku bawansa ya zo masa da abincinsa. To idan bai zaunar da shi suka ci tare ba, to ya samar masa ko da loma daya ko biyu, ko ya ce, abinci daya ko biyu. Domin lallai shi (yi masa haka) shi ne rigakafinsa (ga abincin, domin shi yake kawowa).”  

Babi na Goma Sha Tara: Bawa mai kiwo ne bisa dukiyar shugabansa. Da haka Annabi (SAW) ya jingina dukiyar zuwa ga shugaba:
272. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Salim dan Abdullahi ya ba ni labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai shi ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dukkanku (kowanenku) makiyaya ne, kuma kowa za a tambaye shi game da abin kiwonsa. Shugaba mai kiwo (makiyayi) ne, kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa. Mutum mai kiwo ne a cikin iyalansa kuma shi za a tambaya game da abin kiwonsa. Mace mai kiwo ce cikin dukiyar mijinta ita za a tambaya game da abin kiwonta. Bawa mai hidima mai kiwo ne cikin dukiyar shugabansa, kuma shi za a tambaya game da abin kiwonsa.” Ya ce, “Na ji wadannan daga Annabi (SAW) kuma ina tsammani Annabin ya ce: “Mutum cikin dukiyar babansa mai kiwo ne kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa, dukkanku dai masu kiwo ne kuma dukkanku za a tambaye ku game da abin kiwonku.”

Babi na Ashirin: Wanda duk zai bugi bawa to ya nesanci (bugun) fuska:    
273. An karbo daga Muhammad dan Ubaidullahi ya ce: “dan Wahab ya ba mu labari ya ce, Malik dan Anas ya ba ni labari ya ce, dan Fulan (dan wane) ya ba ni labari daga Sa’id Makburi daga Babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) Hawwala Sanad. Ya ce, “Abdullahi dan Muhammad ya ba mu labari ya ce, Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Hammam daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Idan dayanku zai yaki (bugi) bawansa ya nisanci bugun fuska.”