Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi (7)

139. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Usman dan Umar ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abdullahi zan Ka’ab dan Malik daga Ka’ab (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai shi ya kai karar dan Hadradin bisa wani bashi wanda ke bin sa a cikin […]

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi (7)
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi (7)

139. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Usman dan Umar ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abdullahi zan Ka’ab dan Malik daga Ka’ab (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai shi ya kai karar dan Hadradin bisa wani bashi wanda ke bin sa a cikin Masallaci, suka rika daga muryarsu wajen magana har Manzon Allah (SAW) ya ji su lokacin yana cikin gidansa ya fito zuwa gare su ya bude labulen dakinsa ya yi kira cewa: Ya Ka’ab, ya ce, “Na karba maka ya Manzon Allah! Ya ce, “Ka rage masa wani abu daga abin da kake bin sa bashi, ya yi masa nuniya da ya rage masa rabi ya ce: “Lallai zan aikata haka ya Manzon Allah! (Annabi) ya ce, wa dan Hadradin: “Tashi ka biya shi.”
140. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Urwatu dan Zubair daga Abdurrahman dan Abdul-kari’u cewa: “Lallai shi ya ji Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Na ji Hisham dan Hakim dan Hizam yana karatun suratul Furka’n ba yadda nake karantawa ba. Har na yi kusan in yi gaggawa a kansa sai na jinkirta masa har ya kare Sallah, sa’annan na rike shi ta gefen mayafinsa na tafi da shi ga Manzon Allah (SAW) na ce: “Hakika na ji wannan yana karatu ba yadda ka karantar da ni ba, sai (Annabi) ya ce mini: “Sake shi,” sa’annan ya ce, masa: “Karanta, sai ya karanta.” (Annabi) ya ce, “Kamar haka aka saukar da ita,” sa’an nan ya ce, mini:  “Karanta, na karanta.” Sai ya ce, “Kamar haka aka saukar da ita, hakika Alkur’ani an saukar da shi bisa haruffa (kira’o’i) bakwai, ku karanta daga gare shi abin da ya saukaka muku.”