Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Babi na Talatin da Uku: Kwadaitarwa game da yaki. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ka kwadaitar da mummunai bisa ga fita yaki…” (Q:8:65): 523. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Mu’awiya danAmru ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari daga Humaid ya ce: “Na ji Anas (Allah Ya […]
Babi na Talatin da Uku:
Kwadaitarwa game da yaki. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ka kwadaitar da mummunai bisa ga fita yaki…” (Q:8:65):
523. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Mu’awiya danAmru ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari daga Humaid ya ce: “Na ji Anas (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa Khandak (gwalalo) sai ga muhajirai da mutanen Madina suna tona ramin cikin wata safiya mai tsananin sanyi. Saboda ba su da bayin da za su yi musu wannan aiki. Lokacin da ya ga abin da ya same su na wahala da yunwa, sai ya rika cewa: “Ya Allah! Lallai rayuwa ba komai ba ce face rayuwar Lahira. Allah Ka gafarta wa mutanen Madina da masu hijira. Sai suka rika amsawa da cewa: “Mu ne wadanda muka yi wa Annabi Muhammad mubaya’a bisa jihadi matukar muna raye.”
Babi na Talatin da Hudu:
Tona ramin Khandak (gwalalo):
524. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari ya ce, Abdul’aziz ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Muhajirai da Ansar (mutanen Madina) sun rika tona ramin Khandak (gwalalo) a gefen Madina suna yashe turbaya bisa bayansu, suna cewa: “Mu ne wadanda muka yi wa Annabi Muhammad mubaya’a – Bisa jihadi matukar muna raye.”
Shi kuma Annabi (SAW) yana amsa musu da cewa: “Ya Allah! Lallai babu wani alheri face alherin Lahira. Ka sanya albarka cikin mutanen Madina da Muhajirai.”
525. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Abu Is’hak ya ce, “Na ji Barra’u (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: “Annabi (SAW) ya kasance yana cirar (tono) yana mai cewa: “Ba dominKa ba (Allah) da ba mu shiryu ba.”
526. An karbo daga Hafsu dan Umar ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Abu Is’hak daga Barra’u (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na ga Annabi (SAW) a ranar Yakin Ahzab yana tono kasa har kura ta rufe hasken cikinsa yana mai cewa: “Ba dominKa ba (Allah) da ba mu shiryu ba. Da kuma ba mu yi sadaka ba, kuma da ba mu yi Sallah ba . Allah Ka saukar da natsuwa gare mu kuma Ka tabbatar da duga-duganmu in mun hadu wajen yaki. Lallai jama’ar farko sun yi zalunci a kanmu. Sun yi nufin fitina da mu, muka ki.”
Babi na Talatin da Biyar:
Hukuncin wanda uzuri ya tsare shi daga fita zuwa yaki:
527. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari cewa: “Lallai Anas ya ba su labari ya ce: “Mun komo daga Yakin Tabuka tare da Annabi (SAW).”
528. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya kasance yana fita zuwa yaki. Sai ya ce, “Lallai wadansu jama’a daga mutanen Madina sun saba mana (wajen fita), alhali ba mu taba fita bisa wani gwadabe ko cikin wasu kwarurruka ba face suna tare da mu (wajen lada), amma uzuri ya hana musu fita yaki.”
Babi na Talatin da Shida:
Fiffikon yin azumi domin Allah:
529. An karbo daga Is’hak dan Nasar ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Xan Juraij ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Sa’id da Suhail dan Abu Salih cewa: “Lallai su sun ji Nu’aman dan Abu Iyyash sun karbo daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya azumci yini daya domin Allah. Allah zai nesantar da fuskarsa daga wuta da kamar nisar tafiyar shekara saba’in.”