Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi(11)
Babi na Ashrin da Shida: daure wanda ake jin tsoron cutarwarsa. dan Abbas ya daure Ikramata bisa koya masa Alkur’ani da Sunnar (Hadisai Annabi) da hukunce-hukuncen gado. 143. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Sa’id dan Abu Sa’id cewa: “Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda […]
Babi na Ashrin da Shida: daure wanda ake jin tsoron cutarwarsa. dan Abbas ya daure Ikramata bisa koya masa Alkur’ani da Sunnar (Hadisai Annabi) da hukunce-hukuncen gado.
143. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Sa’id dan Abu Sa’id cewa: “Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) da wasu mayaka bisa dawaki zuwa Najad sai suka zo da wani mutum daga kabilar Hanifa ana ce masa: Sumamat dan Asal shugaban mutanen Yamama sai suka daure shi a daya daga cikin ginshikan Masallaci. Sai Manzon Allah (SAW) ya fito gare shi ya ce: “Me ke gare ka ya Sumamat? Ya ce, “Alheri ke tare da ni ya Muhammad, sai ya ambaci labarin (Annabi) ya ce: “Ku kwance Sumamat.” (Daga karshe dai sai ya musulunta kamar yanda ya gabata a Littafin Sallah).
Babi na Ashrin da Bakwai:
dauri da tsaro a cikin (Masallacin) Harami. Nafi’u dan Haris ya sayi wani gida don amfani da shi wajen tsare jama’a masu laifuffuka a garin Makka ta wurin Safawan dan Umayyatu bisa sharadin idan Umar (Allah Ya yarda da shi), ya amince to cinikin ya kullu. Idan Umar bai yarda ba Safawan na da Dinari 400. dan Zubair ya tsare masu laifi a Makka.”
144. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Abu Sa’id ya ba ni labari, ya ce: “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya aika da wasu mahaya zuwa Najad sai suka zo da wani mutum daga kabilar Hanifa wanda ake ce masa, Sumamat dan Usal, sai suka daure shi a ginshiki daga ginshikan Masallaci, (Masallacin Annabi).”