Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi

Babi na Ashirin da Tara:  Wanda ya zavi fita zuwa yaqin xaukaka kalmar Allah bisa ga yin azumi: 518. An karvo daga Adam ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari ya ce Sabitul Bananiyu ya ba mu labari ya ce, “Na ji Anas xan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abu Xalha (Allah […]

Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi

Babi na Ashirin da Tara: 

Wanda ya zavi fita zuwa yaqin xaukaka kalmar Allah bisa ga yin azumi:

518. An karvo daga Adam ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari ya ce Sabitul Bananiyu ya ba mu labari ya ce, “Na ji Anas xan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abu Xalha (Allah Ya yarda da shi), ya kasance ba ya yin azumin nafila a zamanin Annabi (SAW) saboda son fitarsa zuwa yaqi. Lokacin da Annabi (SAW) ya rasu ban tava ganinsa yana cin abinci da rana ba face ranan Idin Azumi ko Layya.”

Babi na Talatin: 

Masu shahada bakwai ne ban da mutuwar fagen fama:

519. An karvo daga Abdullahi xan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Summi daga Abu Salih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Masu shahada su biyar ne: Wanda ya mutu ta hanyar annoba da wanda ya mutu ta hanyar murxar ciki da wanda ya mutu ta hanyar nutsewa a cikin ruwa da wanda ya mutu ta hanyar rushewar gini a kansa da wanda ya mutu wajen xaukaka kalmar Allah.” (Mai ruwa ya ambaci biyar, na shida wanda ya mutu ta hanyar wutar gobara; na bawai wadda ta mutu ta hanyar haihuwa).

Babi na Talatin da Xaya:

Bisa faxar Allah MaXaukaki cewa: “Masu zama daga barin yaqi daga muminai, waxansun ma’abuta lalura da masu jihadi a cikin hanyar Allah da dukiyoyinsu da rayukansu, ba su zama daidai. Allah Ya fifita masu jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu a kan masu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Ya yi musu alqawari da abu mai kyau. Kuma Allah Ya fifia masu jihadi a kan masu zama da lada mai girma. Darajoji daga gare Shi da gafara da rahama. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai.” (Q:4:95).

520. An karvo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah daga Abu Is’haq ya ce, na ji Barra’u (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: “Lokacin da wannan aya ta sauka cewa: “Mazauna gida ba su zama daidai da mummunai…”(Q:4 :95). Sai Manzon Allah (SAW) ya kira Zaid ya zo da allon kafaxa ya rubuta ta. Sai Xan Ummu Makhtum ya kawo kukan lulurarsa (ta rashin gani). Sai aya ta sauka cewa: “Masu zama ga barin yaqi daga mummunai ba su zama daidai face mazowa lalura…” (Q:4:95).”

521. An karvo daga Abdul’aziz xan Abdullahi ya ce: “Ibrahim xan Sa’ad Zuhuri ya ce, Salih xan Kainsan ya ba ni labari daga Xan Shihab daga Sahlu xan Sa’ad Sa’idi cewa: “Lallai shi ya ce, “Na ga Marwan xan Hakam yana zaune a cikin Masallaci sai na shiga har na zauna a gefensa ya ba mu labari cewa: “Lallai Zaid xan Sabit ya ba shi labari cewa: “Haqiqa Manzon Allah (SAW) ya yi masa shiftar wannan aya da ke cewa: “Masu zama daga barin yaqi daga mummunai ba su zama daidai da masu fita yaqi domin xaukaka kalmar Allah face ma’abuta lalura….” (Q:4:95). Ya ce, “Sai Xan Ummu Makhtum ya je masa (Annabi SAW) lokacin yana mini shiftarta (imla’i), sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Da ina iya zuwa jihadi da na fita zuwa jihadi. Saboda ya kasance mutum ne makaho, sai Allah Mai girma da Xaukaka Ya saukar wa ManzonSa (SAW) aya lokacin cinyarsa na bisa cinyata sai (cinyata) ta yi nauyi na ji tsoron kada cinyata ta karye (tsage). Sa’an nan aka kuranye masa qarin da cewa: “face ma’abuta lalura….” (Q:4:95).

 Babi na Talatin da Biyu: 

Haquri lokacin yaqi:

522. An karvo daga Abdullahi xan Muhammad ya ce: “Mu’awiya xan Amru ya ba mu labari ya ce Abu Is’haq daga Musa xan Uquba daga Salim Abu Nadar cewa: “Lallai Abdullahi xan Abu Aufa ya rubuta wata takarda cewa: “Sai na karanta shi cewa, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan kun haxu da su (abokan gaba) to ku yi haquri.”

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos