Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi

 Babu na Goma Sha Shida: Sharudda cikin bayar da rance. Dan Umar da Adda’u (Allah Ya yarda da su),, sun ce: “Idan mutum ya sanya ajalinsa ga wanda ya ba shi rance to ya halatta.”: 432. An karbo daga Laisu ya ce: ‘Ja’afar dan Rabu’ah ya ba mu labari daga Abdurrahman dan Hurmuz daga Abu […]

Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi

 Babu na Goma Sha Shida: Sharudda cikin bayar da rance. Dan Umar da Adda’u (Allah Ya yarda da su),, sun ce: “Idan mutum ya sanya ajalinsa ga wanda ya ba shi rance to ya halatta.”:

432. An karbo daga Laisu ya ce: ‘Ja’afar dan Rabu’ah ya ba mu labari daga Abdurrahman dan Hurmuz daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Lallai shi ya ambaci labarin wani mutum ya roki Bani Isra’il rancen Dinari dubu, sai ya ba shi bisa sharadin zuwa wani lokaci sananne.”

Babu na Goma Sha Bakwai:

Rubutun fansa da bayanin abin da ke halatta da ga sharuddan da su saba wa Littafin Allah ba. Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya yi magana game da rubutun fansa cewa: Wasu sharudda ne da ke tsakaninsu (bawa da shugaba).” Dan Umar ko ya ce, Umar ya ce: “Dukan sharadin da ya saba wa Littafin Allah batacce ne ko da sharudda dari ne.”

433. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Yahya daga Amrata daga A’isha (RA) ta ce: “Barirah ta je gare ta tana rokonta cikin biyan kudin fansarta sai (A’isha) ta ce: “Idan kin so zan biya iyalanki amma waliccinki na gare ni.” Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya zo ta ambata masa. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ki saye ta, ki ’yanta ta, domin lallai waliccin bawa yana ga wanda ya ’yanta (shi).” Sa’an nan Manzon ya mike bisa mumbari ya ce: “Me ya sami mutane suke sanya sharudda wadanda babu su a cikin Littafin Allah? Duk wanda ya shardanta wani sharadi da babu shi cikin Littafin Allah ba ya da wannan abu, ko ya shardanta sharudda dari ne.”

 Babu na Goma Sha Takwas:

Abun da ke halatta daga sharudda da togiya cikin furuci. Da sharuddan da mutane ke fahimtarsu a tsakaninsu ko da (wani) ya yi sharudda dari (ne) to daya ce mai kyau. Dan Aunu ya ce daga Dan Sirin ya ce: “Mutumin da ya ce mai hayarsa, shigar da abin hawanka idan ban fita da kai cikin ranaku kaza-da kaza ba to kana Dirhami dari bai fitar da abin hawan ba.” Shuraih ya ce: ‘Wanda ya shardanta wa kansa biyayya ga abin da ba a tilasta shi ba, to shi ke da abin da ya yi sharadin.” Ayyub ya ce, “Daga Dan Sirin cewa: “Lallai wani mutum ya sayi hatsi (abinci) ya ce, idan ban zo gare ka ba ranar Laraba ba, to babu ciniki tsakanina da kai.” Sai aka yi dace bai zo ba,” sai Shuraih ya ce: “ga mai sayen kai ka karya alkawarinka,” sai ya yi hukunci a kansa.                        

434. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari ya ce Abu Zinad ya ba mu labari daga A’raji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Yana da sunaye casa’in da tara dari babu daya wanda ya kiyaye su ya shiga Aljanna.”

Babu na Goma Sha Tara: Sharudda a cikin wakafi (bayar da sadakar fili ko gida ko gona amma rikonsu yana ga mai su):

435. An karbo daga Kutaiba dan Sa’id ya ce: “Muhammad dan Abdullahi mutumin Madina ya ce: “Dan Aunu ya ba mu labari ya ce: Nafi’u ya ba ni labari daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Umar dan Khaddab ya samu wata kasa (gona) a Khaibara sai ya tafi zuwa ga Annabi (SAW) yana neman shawarinsu (umarninsa) a cikinta. Ya ce: “Manzon Allah! Lallai ni, ina da wata kasa a Khaibar ban taba samun arziki irinsa ba wanda nafi so, to me za ka umarce ni game da ita? Ya ce: “Idan ka so sai ka rike asalinta ka yi sadaka da ita (amfanin gonar).” Ya ce: “Sai Umar ya yi sadaka da ita, cewa; “Ba a sayar da ita, kuma ba a kyauta da ita, kuma ba a gadonta, ya yi sadaka da ita ga talakawa cikin makusanta da bayi da hanyar daukaka kalmar Allah da matafiyi da bako.” Kuma babu laifi ga wanda ya shugabance ta da ya ci wani abu daga cikinta bisa kyautatawa, kuma yana iya ciyarwa ba ga wanda ke tarawa (boyewa) ba.” Ya ce, “Sai na bayar da wannan labari ga Dan Sirin ya ce: “Ma’anar kada a bayar ga wanda yake nufin tara dukiya da roko.”

Subhanakallahumma wa bihamdika, Ash’hadu an la’ilaha illa anta astagfiruka wa atubu ilaika