Tare muka kammala jami’a da Tinubu a Amurka —Ogunsanya

Durojaiye Ogunsanya ya ce Tinubu ne shugaban kungiyar dalibai a shekarar da suka kammala jami’ar CSU da ke Amurka

Tare muka kammala jami’a da Tinubu a Amurka —Ogunsanya

Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Durojaiye Ogunsanya, ya ce ajinsu daya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jami’ar Chigaco State University (CSU) da ke Amurka. 

Durojaiye Ogunsanya ya shaida wa gidan talabijin na TVC cewa tare aka yaye su daga fannin Aikin Akanta da Gudanar da Mulki na jami’ar a shekarar 1979, kuma a lokacin Tinubu ne shugaban daliban sashen.

An jima dai ana takaddama kan takardun shaidar karratun Tinubu, inda ‘yan adawarsa ke ikirarin cewa mai suna Tinubu da ta halarci jami’ar ba na miji ba ne, mace ce.

A kan haka ne tsohon mataimakin shugaban kasa kuma babban abokin hamayyan Tinubu a zaben 2023, Atiku Abubaukar ya aike wa jami’ar takardar neman bayanan karatun Tinubu.

Amma da yake jawabi a TVC, Durojaiye Ogunsanya ya ce a jami’ar shi da Tinubu suka fara asnin juna, “A Jami’ar Jihar Chicago, dukkanmu muna sashen aikin akanta, kasuwanci da mulki, kuma ajinmu daya har muka kammala a 1979.

“Ina kuma ba da shaida cewa dalibi ne na kwarai a lokacin da yake jami’a.”

Game da zargin cewa Tinubu bai kammala jami’ar ba, Ogunsanya ya ce, “Mutane sun fiye shiririta, a ce mutum ya yi gwamna shekara 8, ya yi aiki a Mobil na tsawon shekaru, amma kuma a ce bai je jami’a ba, shin zai yiwu?

“Ta yiwu wani lokaci yana zuzuta lamarin, amma wannan ba ya nufin bai je jami’a ba, bayanansa na nan, duk mai bukata zai iya zuwa ya bincika.

“Ni dalibin jami’ar ne, ko da yake da farko a bangaren Injiniya na fara karatu, amma na bari na koma wata kwalejin; dadinta da Amurka shi ne komai sun saukake shi, kowa zai iya farowa daga kasa, har ya gina kansa, ko da kuwa ta takardar high school ce, za su bari ka yi jarabawa.

“Idan ka ci za ka iya neman kwaleji, idan ka faro daga karamar kwaleji na tsawon shekara biyu, kana iya zarcewa da credit dinka zuwa babbar kwaleji ta shekara hudu.

“Ina jin abin da shi  ma shugaban kasa ya yi ke nan. Ya faro daga Richard J college, sa’annan ya koma kwalejin shekara hudu, wato jami’a.

“Amma ni ba wannan karamar kwalejin na yi ba, wata daban na yi sannan na koma jami’a, inda muka hadu.

“Wani malaminmu ya taba tambaya ta cewa, ‘kai dan Najeriay ne’, an ce masa ‘e’. Ya ce, ‘Ka san Bola?’ Na ce masa, ‘a’a’. Shi ne ya ce, ‘to ya kamata ka san Bola’.

“Daga baya ne muka hadu, na san shi  ma dan Najeriya ne, muka zama abokai, kuma mambokin kungiyar daliban fannin akanta.

“Ya ba ni mamaki a yadda ya ci zabe ya zama shugaban dalibai. Da farko mutane na masa dariya saboda yanayin maganarsa ta ’yan Najeriya, amma a hakan ya lashe zabe ya zama shugaban dalibai na shekarar 1978/79.

“Mai so zai iya zuwa ya bincika,” in ji shi.

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa