Tarihi da rayuwar Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan Oyo
Bayan rasuwar tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi, sakamakon fama da matsananciyar rashin lafiya a Legas, mun tsakuro muku wasu muhimman Abubuwa game da rayuwarsa. Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis 25 ga watan Yunin 2020 yana da shekara 70 a duniya, a asibitin First Cardiology Hospital, Ikoyi a jihar Legas bayan ya yi fama […]
Bayan rasuwar tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi, sakamakon fama da matsananciyar rashin lafiya a Legas, mun tsakuro muku wasu muhimman Abubuwa game da rayuwarsa.
Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis 25 ga watan Yunin 2020 yana da shekara 70 a duniya, a asibitin First Cardiology Hospital, Ikoyi a jihar Legas bayan ya yi fama da matsanciyar rashin lafiya.
Ga kadan daga cikin tarihin rayuwarsa:
Tasowarsa
- An haifi Abiola Ajimobi ranar 16 ga watan Disambar 1949 a Oja-Iba, da ke Ibadan, Jihar Oyo.
- Ya yi karatun Firamare a Saint Patricks, da ke Oke-Padre a Ibadan.
- Ajimobi ya kasance mai shiga harkokin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ciki har da kwallon kafa inda ya zama mai jagorantar harkar wasanni a makarantar sakandaren da ya halarta.
- Tsohon Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi ya rasu
- Jihar Oyo ta samu lafiya -Gwamna Ajimobi
Karatunsa
Marigayi Ajimobi ya karanta Harkokin Tafiyar da Kasuwanci da Kudade a Jami’ar Jihar New York da ke a Buffalo a kasar Amurka – inda ya samu shaidar digrinsa na farko.
Sa’annan ya yi digiri na biyu a bangaren Nazarin Kasuwanci da Kudade a wata Jami’a mai suna Governors State University da ke Illinois a Amurkar.
Iyalansa
- Ya auri uwargidarsa Misis Florence Ajimobi a shekarar 1980 inda suka haifi ‘ya’ya biyar.
- ‘Yarsu ta fari, mai suna Abisola Kola-Daisi ta kasance mai hazakar harkar kasuwanci ta mallaki wani katafaren shago mai suna Florence H Luxury.
- Shi ne mahaifin mijin diyar Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje , wata Fatima.
Siyasa
- A shekarar 2003, Ajimobi ya zama dan majalisar dattawa daga jiharsa ta Oyo. Ya zama Mataimakin Shugaban Marasa rinjaye a zauren.
- A shekarar 2007 ya yi takarar gwamna karkashin jam’iyyar ANPP, amma bai yi nasara ba a lokacin.
- Sai dai ya sake gwada sa’arsa a shekarar 2011 karkashin jam’iyyar ACN inda ya yi nasarar darewa kujerar gwamnan jihar Oyo.
- Ya sake neman wa’adi na biyu a zaben shekarar 2015, a karkashin jam’iyyar APC; inda ya fafata da tsoffin gwamnonin jihar biyu da suka rike mukamin gabanin sa, wato Christopher Alao Akala da Rashidi Adewolu Ladoja.
- Da ya yi nasar da shi ne zai fara zama gwamna da ya taba yin tazarce zuwa wa’adi na biyu a jere a tarihin Jihar Oyo.
- An zabe shi a matsayin Sanata karkashin jam’iyyar APC daga mazabar Oyo ta Kudu a ranar 28 ga watan Satumban 2018.
- A ranar 9 ga watan Maris, 2019, Ajimobi ya sha kaye – a yunkurinsa na neman zarcewa kan kujerar, a hannun dan takarar jam’iyyar PDP Kola Balogun.
- A ranar 17 ga watan Yunin da muke ciki ne Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar APC ya sahale masa da ya zama shugaban riko na jam’iyyar na kasa.
Karshen rayuwarsa
A ranar 18 ga watan Yunin an yi ta yada jita-jitar cewa Ajimobin ya rasu; amma daga bisani aka gano cewa karya ce.
A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni 2020 ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya mai tsanani.
Yadda Ajimobi yabar duniya
Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya rasu bayan ya shafe makonni yana fama da rashin lafiya mai tsanani da aka danganta da cutar coronavirus.
Ajimobi ya rasu yana da shekara 70, a asibitin First Cardiology Hospital, Ikoyi a jihar Legas inda aka yi jinyar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari.
Rasuwar tasa na zuwa ne bayan a makon jiya an yi ta baza jita-jitar ya rasu kafin daga bisani iyalai da makusantansa su karyata rade-radin.
Wasu majiyoyi na cewa Ajimobi ya shafe mako guda yana halin rai kwakwai mutu kwakwai kafin kafin daga bisani rai ya yi halinsa.
Kafin rasuwarsa, Ajimobi shi ne wanda Kwamitin Gudanarwa (NWC) na Jam’iyyar APC ya nada shugabanta na riko, amma rashin lafiyar ta sa aka nada Hilliard Eta mukaddashinsa.
Kafin nadin, shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar (Kudu-maso-Yamma), kuma ya yi Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Oyo.