Tarihi da rayuwar Sheikh Ahmed Lemu (1929-2020)
Muhimman abubuwan game da fitaccen malamin Musulunci Sheikh Ahmed Lemu
A safiyar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020 Allah Ya yi wa fitaccen malamin Mususlunci Sheikh Ahmed Lemu yana da shekara 91.
Dansa Nuruddeen, wanda ya ce Sheikh Lemu wanda aka haifa a 1929 ya rasu ne a Minna, Jihar Neja, inda ake shirin yin jana’izarsa.
- Ta’aziyyar A’isha Lemu: An yi rashin kundin ilimi
- Hajiya Maryam Sheikh Ahmad Lemu: Yin Da’awah sai mai juriya
- ’Yan fashi sun harbe mai yi wa kasa hidima
- An kara lokacin rajisatar lambar dan kasa da layin waya
“Inna lillahi wa inna liayhi raji’un; Allah Ya yi wa mahaifinmu, Mai Shari’a Dokta Sheikh Ahmed Lemu rasuwa da sanyin safiyar yau (Alhamis) a Minna; Nan gaba za a sanar da shirye-shiryen jana’iza,” inji.
Jama’a na yin ta’aziyya tare da addu’o’in Allah Ya rahamshi Sheikh Lemu, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne, alkali, kuma jagora wurin wanzar da zaman lafiya da yada musulunci a Najeriya da ma duniya.
Ga kadan wasu abubuwan da muka tsakuro muku game da tarihi da rayuwar Sheikh Lemu:
Yarinta da iliminsa
- A ranar 12 ga watan Disamba, 1929, aka haife shi a garin Lemu, Jihar Neja ta yanzu.
- A 1932 ya fara karantun allo yana dan shekara uku.
- Yana makarantar allo aka sanya shi a ta elemantare (firamre) wadda ya kammal a 1939.
- Bayan firamare ya tafi kwale wadda ya a 1948 a mahaifar tasa.
- Ya yi Makarantar Shari’a (School of Arabic Studies a yanzu) inda ya samu karamar shaida a 1950.
- A 1952 ya samu takardar shaidar koyarwa ta Grade Two a harshen Larabci, Ilimin Musulunci da Shari’a da kuma koyarwa.
- A 1954 ya halarci Jami’ar London a kasar Birtaniya inda ya yi karatu a tsangayar nazarin halayyar al’ummar Afirka da Turawa.
- A nan ya samu babbar shaidar nazarin Tarihi da harsunan Larabci, Hausa da Fasha a 1961.
- A Jami’ar din kuma ya samu Digirinsa a kan hallayar al’ummar Afirka da Turawa a 1964.
Aiki da kuma kwarewa
- Sheikh Lemu masani ne na harshen Larabci, Turancin Ingilishi da kuma Ilimin Musulunci.
- Ya shekara sama da 50 a rayuwarsa yana aikin koyarwa tare da yada addinin Islama.
- Ya koyar a makarantar Sakandaren Gwamnati ta GSS Bida, Jihar Neja daga 1953-1960.
- Daga nan ya zama babban malamin Turanci, Larabci da Tarbiyya har ya zama mai kula da wannan fanni a Makarantar Karatun Harshen Larabci (SAS) da ke Kano.
- A 1965 ya zama Mataimakin Darakta mai kula da Makarantun Sakandaren Gwamnati.
- Ya zama Shugaban Kwalejin Horas da Malamai na Larabci a 1966 kafin ya zama Babban Mai Lura da Ilimi a 1970.
- Ya zama shugaban wannan sashe a 1971 zuwa 1973 a Jihar Sakkwato.
- A 1974 ya zama Darakata na Musamman, sannan a 1975 ya sama Daraktan Tsare-tsaren Ilimi na Jihar.
- Shi ne alkali na farko a Kotun Daukaka Kara ta Shar’ia Musulunci a Jihohin Sakkwato da Neja a shekarar 1976-1977.
- Ya zama Babban Alkalin Kotun Daukaka Karar Shari’a a Jihar Neja a 1976-1991.
- Ya zama kwararren mai bayar da shawara kan ilimi na Jami’ar Osogbo a 2009.
Gudunmuwar Sheikh Lemu ga al’umma
- Ya bayar da gagarumar gudunmuwa a tattaunawar samar da tsaro da zaman lafiya bayan samun matsalolin tsaro a Arewacin Najeriya.
- Ya shekara sama da 50 yana koyarwa tare da yada addinin Islama.
- Mutum ne mai takawa da kira ga rungumar juma.
- Mamba ne a hukumomin Musulunci a fadin duniya.
- Ya gabatar da laccoci da darussa da tarukan kara wa juna sani a kokarinsa na yada ilimi, ci gaba da kuma Musulunci
- Ya wallafa litattafai aka shafe shekaru ana amfani da su domin fahimtar addinin Islama a Najeriya.
- Ya kafa kungiyoyi, makarantu da gidauniyar Musulunci da ta kai ga hadin gwiwa da Bankin Musulunci wurin bunkasa ilimi a Najeriya.
- Babban jagora ne wurin kare hakkokin mata Musulmi.
- Kokarinsa ya kai ga kafa kungiyoyin mata Musulmi a Najeriya, yada zaman lafiya da kuma yaki da rikice-rikice tsakanin dariku.
- Shi ne ya kafa cibiyar yada Musulunci ta Islamic Da’awa Institute domin yaki da tattsauran ra’ayin addini.
Karramawar da ya samu
- Hukumomi da cibiyoyi na cikin gida da ma na duniya sun ba wa Sheikh kyaututtuka da lambobin karramawa saboda hidimarsa ga addini da al’umma.
- Jami’ar Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ta ba shi Digirin Digirgir Girmamawa a 1996
- Ya samu Digirin Digirgir na Karramawa daga Jami’ar Osogbo 2011.
- Sannan Jami’ar Al-Hilal ta ba shi makamanciyarta a shekarar 2013.
- Shugabannin Kasar Najeriya sun ba shi lambar girmamawa ta kasa.
- Gwamantin soja ta Ganar Abdulsalami Abubakar ta ba shi girma ta karramawa (OFR) a 1999
- Shugaba Olusegun Obasanjo ma ya ba shi makamanciyarta ta 2001.
- A 2014 ya samu Kyautar Sarki Faisal na Kasar Saudiyya kan yi wa Addinin Musulunci Hidima.
- A shekarar ce kuma aka nada shi Shugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar Bayar da Tallafin Musulunci ta Duniya.
Rasuwarsa
- Sheikh Ahmed Lemu miji ne ga mashahuriyar mai da’awar kuma marubuciyar Musulunci, Aisha Lemu.
- Ya rasu ‘yana da shekara 91 a duniya a ranar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020.
- Ya rasu ya a garin Bida, Jihar Neja, ya bar ‘ya’ya da jikoki.
- Daga cikin ‘ya’yansa akwai shahararriyar mai gabatar da laccoci, Maryma Lemu.