Tarihin bacewar jiragen sama a duniya

Tarihi ya nuna ba jirgin saman  Malaysia mai inkiyar MH370 ya fara bacewa ba domin kuwa akwai wadansu jiragen saman da suka yi  irin wannan batan-dabon.Da yammacin ranar  5 ga watan Disamban shekarar 1945 ne, wani jirgin soji mai suna Flight 19 wanda ya tashi daga garin Florida da ke Amurka inda ya nausa ta […]

Tarihin bacewar jiragen sama a duniya
Tarihin bacewar jiragen sama a duniya

Tarihi ya nuna ba jirgin saman  Malaysia mai inkiyar MH370 ya fara bacewa ba domin kuwa akwai wadansu jiragen saman da suka yi  irin wannan batan-dabon.
Da yammacin ranar  5 ga watan Disamban shekarar 1945 ne, wani jirgin soji mai suna Flight 19 wanda ya tashi daga garin Florida da ke Amurka inda ya nausa ta cikin yankin nan mai cike da hadari na Bermuda Triangle. Matune 13 da ke cikin jirgin har yau ba duriyarsu. Wani jirgin kuma da aka aika ya nemo shi, shi ma har zuwa yau ba a ji labarinsa ba.
Wani jirgi mai sunan Star Ariel ya bace bayan ya tashi daga garin Bermuda  a hanyarshi ta zuwa kasar Jamaika a ranar 17 ga watan Janairun shekarar 1949. Haka dai a kai ta neman shi ba labari, har zuwa lokacin da aka gaji da aikin nema kuma aka hakura da mutane fiye da 20 da ke cikin shi.
Jirgin mai suna Flight 571 ya yi hadari a tsaunin kankara na  Andes saboda rashin kyahun yanayi. Cikin mutane 45 da ke cikin jirgin, mutane 12 ne suka mutu. Shida kuma sun mutu ne jim kadan bayan hadarin, takwas kuma tsananin sanyin kankara ne ya kashe su. Sauran 19 kuwa rashin cimaka sai da ya kai su fara cin gawarwakin ‘yan uwansu da suka mutu. Sun kwashe kwana 10 suna tafiya da kafa ba tare da isa gari ba.
Air France Flight 447 wani jirgin saman ne da ya bace da fasinjoji 288 a tekun Atlantic a shekaran 2009. Watan Mayun shekarar 2011 an gano wasu daga cikin gawarwakin fasinjojin, sauran kuwa har yau ba a ji duriyarsu ba.
Hadarin jirgin Flight 191 kuwa shi ne daya da cikin hadari mafi muni a tahirin hadarin jiragen saman Amurka. Ya fadi ne bayan ya tashi daga filin jirgin saman Chikago a cikin shekarar 1979. Mutane 271 suka mutu sakamakon hadarin.