Tarihin Farfesa Abdullahi Mahdi (1945-2022)
Muhammad Nura, ya ce ya san Mahdi ya dauki nauyin karatun yara fiye da lissafi musamman makafi da guragu da sauransu.
An wayi garin ranar Asabar 17 ga watan Disamban 2022 da labarin rasuwar Farfesa Abdullahi Mahdi, tsohon Shugaban Jami’ar Ahamdu Bello ta Zariya (ABU).
Farfesa Mahdi, masanin tarihi kuma Shugaban Jami’ar Jihar Gombe na farko, ya koma ga Mahaliccinsa ne yana da shekara 77.
Takaitacen tarihi
Tasowarsa
An haihifi Abdullahi Mahdi a garin Gwoza na Jihar Borno a watan Disamban 1945, inda ya halarci makarantar firamare ta Warrabe, daga nan ya tafi Gwoza Central sannan ya yi Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kirkire-kirkire (Goverment Craft) da ke Maiduguri.
Aiki
Farfesa Abdullahi Mahdi, shahararren masanin tarihi, ya fara koyarwa a Jami’ar Ahnadu Bello da ke Zaria (ABU) a shekarar 1984 a matsayin Babban Malamin Jami’a a Sashin Nazarin Tarihi.
Ya kasance Shugaban Jami’ar ABU daga shekarar 1998 zuwa 2004.
Bayan barinsa ABU ya zama Shugaban Jami’ar Gwamnatin Jihar Gombe (GSU) na farko, sannan shi ne Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta garin Kumo Gombe kafin ya koma Jami’ar Lincorn da ke Malesia.
Hidima
Marigayi Farfesa Abdullahi Mahdi, shi ne ya assasa Gidauniyar Mahdi Foundation da ke yaki da kwararowar hamada (Mahdi Reforestation).
Saboda jajircewarsa da kuma sadaukarwa da hidimta wa kasa, an karrama shi da lambar yabo ta CON.
Kyakkyawar shaida
Farfesa Abdullahi Mahdi, ya rasu da dare ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba, 2022 yana da shekara 77.
Wasu daga cikin dalibansa da suka zanta da wakilinmu sun bayyana shi a matsayin gwarzo kuma haziki mai taimakon al’umma.
Muhammad Nura, ya ce Mahdi ya dauki nauyin karatun yara fiye da lissafi musamman makafi da guragu da sauransu.
Ya ce daga cikin daliban da marigayin ya dauki nauyin karatunsu akwai daya da yanzu yake koyarwa a Sashen Kimiyyar Siyasa kuma shi ne shugaban Kungiyar Nakasassu ta Kasa.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin shi Isiyaku Adamu, dan jin yadda ya ji da mutuwar ta farfesan ba mu samu jin sa ba.