Tarihin Farin Jakada (SAW) (2)
Dukan wadannan dauloli, manyansu da kananansu sun shahara wajen yake-yake da kare al’adun Jahiliyya da cudanya addini da bautar gumaka da son kai da bautar wanin Allah. Kuma ba kawai bautar gumaka tsarin Jahiliyya ya gadar wa al’ummomin Larabawan wancan lokaci ba, kuma sun rayu bisa tsarin wasu munanan al’adu. Daga cikin tsarin rayuwarsu akwai […]
Dukan wadannan dauloli, manyansu da kananansu sun shahara wajen yake-yake da kare al’adun Jahiliyya da cudanya addini da bautar gumaka da son kai da bautar wanin Allah.
Kuma ba kawai bautar gumaka tsarin Jahiliyya ya gadar wa al’ummomin Larabawan wancan lokaci ba, kuma sun rayu bisa tsarin wasu munanan al’adu. Daga cikin tsarin rayuwarsu akwai kyamar haihuwar ’ya’ya mata, inda suke binne su da rai. Akwai kisan rayuka ba tare da nuna wata damuwa ba, akwai daukar fansa bisa dalilan kabilanci. Sai yawaitar ayyukan barna irin su shan giya da caca da zinace-zinace da sauransu.
Amma duk da irin wannan rayuwa ta Jahiliyya da kabilun Larabawan Makka da sauransu suka samu kansu a ciki, wani babban al’amari da ya fito fili, kamar yadda malaman tarihi suka ruwaito, shi ne addini da zamantakewar mutanen yankin sun kunshi birbishin rayuwa da addinin zuriyar Annabi Isma’il (AS) duk kuwa da cewa Annabi Isma’il (AS) da mahaifinsa Annabi Ibrahim (AS) sun rayu ne fiye da shekara dubu biyu da dari biyar kafin zuwan Annabi (SAW). Za mu iya fahimtar wannan ta hanyar nazarin irin rayuwarsu da ayyukan bautarsu. Larabawan Makka ba su gushe ba suna ambaton Allah wajen neman taimako, suna ibada a dakin Ka’aba tare da sauran rukunan aikin Hajji irin su dawafi da Talbiyya, suna zaman Mina da Muzdalifa da ziyarar Jamra da sauransu. Wannan ya tabbatar da cewa sun gaji addinin kakansu Annabi Isma’il (AS). Tsarin shugabancinsu ya sake fito da tasirin addinin Allah a rayuwarsu ta al’ada, domin daga cikin muhimman ayyukan mulki da suke yi, akwai kula da shayarwa da ciyar da abinci ga masu ziyarar dakin Ka’aba lokaci-lokaci, sannan akwai daidaita tsare-tsaren kasuwancinsu su dace da lokutan aikin Hajji.
A lokacin da aka bai wa Abdulmuddalib matsayin mai kula da samar da ruwa da abinci ga baki mahajjata, an samu ci gaba mai yawa ta hanyar farfado da rijiyar Zamzam da inganta kasuwanci a tsakanin Larabawan Makka. Wannan ya janyo mutane suka rika tururuwa zuwa Makka don ziyarar ibada da kasuwanci. Wannan kuma ya jawo hankalin wasu al’ummomi da ke gogayya da su, wanda hakan ya sanya wadansu sarakuna suka yi kokarin katse hanzarin ci gaban wannan kabila ta Larabawa da ke garin Makka. Sakamakon haka ne Abrahata, Sarkin Sana’a da ke Yamen, wadda ya gina dakin ibadar addinin Kirista a birninsa kuma ya yi burin ya janyo hankalin mutane daga ibadun da ake yi a dakin Ka’aba zuwa gare shi, ya yi yunkurin kawo hari garin Makka da burin wargaza dakin Ka’aba don cimma burinsa.
Darasi na Biyu
Darajar Birnin Makka inda aka haifi Annabi (SAW):
Kamar yadda Allah Ya zabi wadansu mutane Ya ba su fifiko a kan wadansu, haka su ma garuruwa da birane Allah Ya fifita wasu a kan wasu. Idan kuwa ana magana a kan kasashe da manyan biranensu kuwa, to Makka ita ce Uwar Birane “Ummul kura” Uwar bisa nassin Alkur’ani. (Suratul An’am:92 da Suratus Shura:7).
Gari ne da Allah Ya sanya aminci da kwanciyar hankali a cikinsa. Alkibla ce ta Musulmi a duk inda suke a duniya. Zukatan muminai a ko’ina suna karkata zuwa ziyararsa, kuma idan sun koma gidaje ko kasashensu sai sun bukaci komawa. (Suratul Bakara: 125) A nan ne dakin Allah na farko da aka gina don ibada yake. A jikinsa akwai Hajarul Aswad daya daga cikin duwatsun Aljanna.
Shi ne kadaitaccen wuri da aka amince wa Musulmi ya shafa da sunan ibada. Sallah a wannan gari tana da karin matsayi sama da ninki dubu 100 a kan wani gari wanda ba shi ba.
Ba a zubar da jini a birnin Makka, ba a farauta ko tayar da hankalin tsuntsu balle dan Adam. Ba a cire ganye daga bishiya, ba a daukar tsintuwa sai idan za a yi cigiya. (Suratun Naml: 91)
Bukhari da Muslim sun ruwaito Hadisi daga Ibnu Abbas (RA) daga Manzon Allah (SAW) cewa, “Allah Ya haramta Makka, bai halatta wa kowa yaki a cikinta ba gabanina, haka ma ba zai halatta wa kowa ita ba a bayana. Ni ma awa daya ce daga cikin wuni aka halatta mini. Don haka, ba a tsinke ganyenta, ba a yanke bishiyarta, ba a korar dabbar farauta a cikinta, ba a daukar tsintuwarta sai ga wanda zai yi cigiya.” Sai Abdullahi dan Abbas (RA) ya ce, “Ban da Idhkir” bishiyar da muke yin rini da ita, kuma muke amfani da ita wajen rufe gawawwakinmu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “To ban da ita.”
Albarkacin addu’ar Annabi Ibrahim (AS) a kullum ana samun kowane nau’in abinci da kayan marmari a birnin Makka.(Suratul Bakara: 126). A karshen zamani kuwa idan Dujal ya bayyana, Allah zai tsare wannan birni daga kazantar takun kafafunsa kamar yadda Ya tsare shi daga sharrin Rundunar Giwaye.
Bukhari da Muslim sun ruwaito Hadisi daga Anas dan Malik (RA) daga Manzon Allah (SAW) cewa, “Babu wani gari da Dujal ba zai shiga ba, sai Makka da Madina. A lokacin bayyanarsa babu wata kafa a cikinsu (Makka da Madina) face Mala’iku sun yi sahu a kai suna kare su. Sannan Madina ta yi girgiza uku da mutanen da ke cikinta. Duk wani munafiki ko kafiri sai ya fita.”
A wannan tsarkakakken gari ne aka haifi Shugabanmu kuma Shugaban Ma’aika Annabi Muhammadu dan (Abdullahi) da Amina, (Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam).
Darasi na Uku
Shekarar Haihuwar Annabi (SAW):
A shekara ta 570 Miladiyya wadda ake kira da Shekarar Giwaye, Sarkin Sana’a ta kasar Yamen, mai suna Abrahata ya shirya mayaka ya nufi garin Makka don ya rushe dakin Ka’aba. Wadansu malaman tarihi sun ce bukatar rushe Ka’aba ta taso ne saboda Abrahata yana da burin ya mayar da daularsa ta zama matattarar ibada da bauta da kasuwanci a tsakanin kabilun Larabawa, maimakon garin Makka da ya samu wannan daraja saboda alfarmar dakin Ka’aba. Don haka ya yi shiri sosai bisa kan giwaye tare da kayan yaki mai yawa, sannan ya jagoranci wannan tawaga shi da kansa. Labari ya bazu ko’ina, amma don karfinsa da shirinsa Larabawan Makka suka kasa daukar matakin hana shi shiga garin Makka.
Ibn Hisham ya ce a kan hanyar Abrahata, wadansu kabilun Larabawa sun yi kokarin tare shi, amma giwayensa suka tattake su. Kuma Abrahata ya bace hanya, amma Abu Rigal ya nuna masa hanyar. Haka suka yi ta tafiya har suka iso garin Makka.
A wannan lokaci Abdulmuddalib ya yi duk iyakar kokarinsa wajen sasantawa, ya kuma nuna masa cewa idan har nufinsa shi ne rushe Ka’aba, to Allah zai kare dakinSa don haka ba zai ci nasara ba. Su ma giwayen nasa sun yi kokarin turjewa tare da ja da baya, amma ina kaddara ta riga fata, don haka Abrahata ya kekasa kasa ya ce babu gudu babu ja da baya, sai ya cimma burinsa.
Za a iya samun Aliyu Muhammad Sa’id, Gamawa Ta +2348023893141
Email: [email protected]