Asali da Tarihin Kalandar Musulunci
Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani kan lissafin kwanan wata a kalandar Musulunci ta Hijiriyya
1 ga wayan Muharram shi ne ranar farko na shekarar Musulunci, wadda bana ake shekara ta 1446 Bayan Hijira.
Lissafin kalandar Musulunci ta Hijiriyya ta fara lissafi ne daga shekarar da Manzon Allah (SAW) ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina.
Amma sai bayan rasuwar Manzon Allah (SA) da shekara bakwai (17 Hijiriyya), a zamanin Khalifa na biyu, Umar Bin Khattab, aka kirkiro Kalandar Hijiriyyar.
A shekarar ce bayan samun wasu wasiku da kwanan wata amma babu shekara da aka aiko su, Abu Musa Al-Ash’ari (RA) ya bukaci Umar (RA) da cewa akwai bukatar yadda za a rika bambance kwanan watan da shekaru.
A sakamakon haka Umar (RA) ya shawarta da Sahabbai har a karshe aka amince da fara kirgen shekarun da shekarar da Manzon Allah (SAW) ya yi hijira zuwa Madina.
Ko da yake a lokacin ganawar akwai Sahabban da suka ba da shawarar a fara kirgen da shekarar rasuwar Manzon Allah (SAW), da wadanda ke ganin a yi amfani da shekarun Farisawa da masu ganin a yi amfani da shekarun Rumawa.
Shekarar Musulunci na da watanni 12, inda wanda farko da karshen kowane wata ke tabbata da ganin jinjirin wata.
Ana fara neman jinjirin wata ne a ranar 29 ga kowane wata, idan har an gani, washegari zai kasance ranar farko ta wata na gaba.
Idan kuma ba a ga jinjirin wata a ranar 29 ba, za a kara kwana guda, watan ya kasance mai kwanaki 3o, wanda shi me mafi yawan kwanakin watan Musulunci.
Jerin Watannin Musulunci
- Muharram
- Rajab
- Rabi’ul Auwal
- Ri’ul Sani
- Jumada Auwal
- Jumada Sani
- Rajab
- Sha’aban
- Ramadan
- Shawwal
- Zul-Kida
- Zul-Hajj
Watani Masu Alfarma
Daga cikin watannin, akwai guda hudu Masu Alfarma. Su ne:
- Zul-Kida
- Zul-Hajj
- Muharram
- Rajab
A cikin wadannan watannin an haramta yin yaki, sai da wanda aka kai wa hari.
Falalarsu:
Daga cikin falalolinsu:
- Allah Ya rantse da kwanaki 10 na Zul-Hajji
- A cikinsu (Zul-Hajji) ake aikin Hajji
- Babu yinin da ladan aiki a cikinsa ya fi na kwanaki 10 na farkon Zul-Hajj
- Akwai hani mai tsanini kan aikia sabo ko zalunci a cikinsu
- A cikin yini mafi girma a shekara a yake (Ranar Arfa)
- Babu azumin da ladansa ya fi na ranar Arafa, 9 ga Zul-Hajj
- A cikinsu (10 ga Muharram) Allah Ya halaka Fir’auna Ya tseratar da Annabi Musa
- A cikinsu ake azumin Tasu’a da Ashura (9 da 10 ga Muharram).
- A cikinsu Allah Ya fanshi Annabi Isma’il da ragon Layya daga Aljanna.
- A cikinsu ake Babbar Sallah da yin Layya