Tarihin Mai shari’a Sidi Dauda Bage Sabon Sarkin Lafiya
A mako jiya ne aka zabi Sabon Sarkin Lafiya da ke Jihar Nasaraka inda daya daga cikin alqalan Kotun Qoli Mai shari’a Sidi Dauda Bage ya yi nasarar zama Sarki. Sabon Sarkin ya samu nasarar lashe zaben ne bayan ya kada ’ya’yan sarki da suka fito daga gidajen sarauta na Dalla Dunama da na Ari […]
A mako jiya ne aka zabi Sabon Sarkin Lafiya da ke Jihar Nasaraka inda daya daga cikin alqalan Kotun Qoli Mai shari’a Sidi Dauda Bage ya yi nasarar zama Sarki. Sabon Sarkin ya samu nasarar lashe zaben ne bayan ya kada ’ya’yan sarki da suka fito daga gidajen sarauta na Dalla Dunama da na Ari Dunama. Kadanda suka fafata a zaben sun hada da Alhaji Isiaka Dauda da Alhaji Abdullahi Yusuf da Alhaji Muhammed Makama da Alhaji Maisallau Musa da Alhaji Dunama Dauda da Alhaji Muhammed Kaziri da Alhaji Mustapha Ya’u da Alhaji Safiyanu Bage da Alhaji Abdullahi Bage da Alhaji Aliyu Muhammed da Alhaji Abdullahi Abbas da Alhaji Ramalan Musa da Alhaji Idris Musa da Alhaji Musa Isa Mustapha Agkai da kuma Alhaji Abdullahi Agkai.
Da yake sanar da sakamakon zaben Kkamishinan Qananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Nasaraka Honorabul Haruna Osegba ya ce, masu zaben Sarki 5 ne suka yi zaben inda a qarshe Mai shari’a Sidi Dauda Bage ya samu quri’a 4 cikin 5, yayin da dan marigayi Sarkin Lafiya Musa Mustapha Agkai ya samu quri’a daya. Ya ce ma’aikatar ta bi tanadin dokar zaben sarakuna ta jihar ta 1986 kadda a cekarsa ta buqaci a tabbatar da tsarin karba-karba a zaben kujerar Sarkin Lafiya a tsakanin gidajen sarauta biyu kato Ari-Dunama da Dalla Dunama kadanda a cekarsa take dauke da sanya hannun Gkamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.
An haifi sabon Sarkin Lafiya Alhaji Sidi Dauda Bage ne a ranar 22 ga Maris din 1956 a garin Lafiya. Ya yi karatun firamare a Dunama Primary School da ke Lafiya daga 1963 zuka 1969. Ya yi karatun sakandare a Gobernment Secondary School, Lafiya, daga 1970 zuka 1974. Daga nan ya ci gaba a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi Difloma a fannin shari’a daga 1975 zuka 1977.
Sabon Sarkin ya ci gaba da karatu a jami’ar inda daga bisani ya samu shaidar digiri na farko a fannin shari’a a 1980. Daga nan ya ci gaba da karatu a Makarantar Shari’a ta Qasa, (Nigeria Lak School) da ke Legas inda ya kammala a 1981.
Mai martaba Sabon Sarkin Lafiya Mai shari’a Sidi Bage ya fara aiki ne da ofishin Rudunar Sojin Sama da ke Kaduna a matsayin lauyan rundunar. An kuma nada shi Mai shari’a a kotun Majistare ta 2 da ke Jos a Jihar Filato a 1982. Ya samu qarin matsayi zuka majistare na 1 a 1984.
Daga nan ya samu qarin matsayi zuka Mataimakin Babban Magatakardan Kotun Shari’a a Abuja a 1991. Har ila yau ya samu qarin girma zuka Babban Magatakardan Babbar Kotun Abuja a 1992. Daga nan sai ya zama Alqali a Kotun Daukaka Qara ta Tarayya, inda daga bisani ya samu qarin matsayi zuka Mai shari’a a Kotun Qoli ta Qasa a shekarar 2016.
Yana riqe da kannan matsayi ne aka zabe shi a matsayin sabon Sarkin Lafiya.
A halin da ake ciki kuma kakilinmu ya gano ceka, masu fatan alheri da abokan arziki dana kusa da sabon sarkin Lafiya Alhaji Sidi Bage daga ciki da kajen jihar suna ci gaba da kkararoka gidan sabon Sarkin da ke Bukan-Sidi a Lafiya don taya shi murnar nasarar.