Tarihin mata da ’ya‘yan Annabi Muhammad SAW a takaice
Babu shakka matsayin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) matsayi ne mafificin girma cikin dukkanin halittu, wanda darajarsa ta dara da dukkan wani abin da Allah Madaukakin Sarki Ya halitta. Bisa ga madogara ta nassin Hadisai na tarihi da fadin Magabata na kwarai, ga wani dan taikataccen tahiri game da mata da kuma ’ya’yan fiyayyen […]
Babu shakka matsayin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) matsayi ne mafificin girma cikin dukkanin halittu, wanda darajarsa ta dara da dukkan wani abin da Allah Madaukakin Sarki Ya halitta.
Bisa ga madogara ta nassin Hadisai na tarihi da fadin Magabata na kwarai, ga wani dan taikataccen tahiri game da mata da kuma ’ya’yan fiyayyen halitta kamar yadda wani Shehin Malamin Sunna, Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ya wallafa.
Matan Annabi a takaice
- Saudatu bint Zam’ah (RA): Annabi (SAW) ya aure ta a watan Shawwal bayan shekara 10 da aiko shi da manzanci. Mijinta ya rasu a Habasha kuma kulawa da rayuwarta ya koma hannun gyatumarta wadda a lokacin ta tsufa. Tana daga cikin wadanda suka musulunta suna manya. Ita Manzon Allah (SAW) ya fara aure bayan rasuwar Khadijah. Ta zauna da Manzon Allah (SAW) tsawon shekara 13, kuma ta rasu shekaru 54 Bayan Hijira.
- A’ishatu (RA): A’ishatu (RA) ’yar Abubakar Siddiq (RA), babban abokin Manzon Allah (SAW) kuma Khalifansa na farko. Annabi (SAW) ya aure ta gab da zai yi hijira, tana da shekara 6 ko 7, ya kuma tare da ita tana da shekara 9. Ita kadai ce Manzon Allah (SAW) ya aura tana budurwa. Ta taka rawa a fagen ilimi kuma Annabi (SAW) ya nemi izinin matansa don ya yi jinyar ajali a dakinta. Don haka a dakinta ya yi jinya, a dakinta ya rasu kuma a dakinta aka binne shi. Ta zauna tare da Manzon Allah (SAW) tsawon shekara 13, kuma ta rasu ne a cikin watan Ramadan shekara ta 58 Bayan Hijira.
- Hafsat bint Umar Al-Khattab (RA): Annabi (SAW) ya aure ta a watan Sha’aban shekara ta 3 Bayan Hijira kuma ta rasu a watan Sha’aban shekara ta 45 Bayan Hijira. Ta zauna tare da Manzon Allah (SAW) tsawon kimanin shekara takwas.
- Zainab bint Khuzaimah (RA: Ita ake kira ‘Ummul Masakin’ saboda yawan alherinta da ciyar da miskinai. Annabi (SAW) ya aure ta a shekara ta 5 Bayan Hijira. Ta rasu Annabi (SAW) yana raye, ta yi wata takwas ne kawai da Annabi (SAW) sai Allah Ya yi mata rasuwa.
- Ummu Salamah Hindu bint Abu Umayyah (RA): Tana daga cikin wadanda suka yi hijira sau biyu (ta yi hijira zuwa Habasha) tare da mijinta. Mijinta ya rasu a Yakin Uhud, kuma Annabi (SAW) ya aure ta a watan Shawwal shekara ta 4 Bayan Hijira. Ta rasu a shekara ta 59 Bayan Hijira.
- Zainab bint Jahshin (RA): Annabi (SAW) ya aure ta a watan Zil-Kida shekara ta 5 Bayan Hijira, lokacin tana da shekara 35.Ta rasu a shekara ta 20 Bayan Hijira. Ita ce ayoyin Al-kur’ani suka sauka game da aurenta: “Kuma a lokacin da kake cewa ga wanda Allah Ya yi ni’ima a gare shi, kuma kai ma ka yi ni’ima a gare shi, ka riki matarka, kuma ka bi Allah da takawa. Kuma kana boyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana, kana tsoron mutane, alhali kuma Allah ne Mafi cancantar ka ji tsoronSa. To a lokacin da Zaidu ya kare bukatarsa daga gare ta, Mun aurar maka da ita…”(Ahzab:37)
- Juwairiyyah bint Haris (RA): Tana daga cikin ribatattun yaki da Manzon Allah (SAW) ya sa aka saki, kuma ta fito ne daga gidan daya daga cikin jagororin kabilarsu. Annabi (SAW) ya aure ta a watan Sha’aban a shekara ta 6 Bayan Hijira, bayan an ’yanta ta. Ta rasu a shekara ta 50 Bayan Hijira.
- Ummu Habibah Ramlatu bint Abu Safyan (RA): Mijinta na farko ya rasu a Habasha, ita ce wadda Sarki Najjashi ya aiko sadakinta ga Annabi (SAW). Ya aure ta a shekara ta 7 Bayan Hijira, kuma ta rasu a shekara 44 Bayan Hijira.
- Safiyyah bint Huyyayi (RA): Babanta shi ne Shugaban Yahudawan Banu Nazir. Annabi (SAW) ya aure ta a shekara ta 7 Bayan Hijira. Ta rasu a shekara ta 50 Bayan Hijira.
- Maimunatu bint Haris (RA): Annabi (SAW) ya aure ta a watan Zul-Kida a shekara ta 7 Bayan Hijira, kuma ta rasu a shekara ta 61 Bayan Hijira.
Wadansu malaman tarihi sun kara da cewa Annabi (SAW) ya auri Ummu Shuraik Al-Ansariyya, amma bai tare da ita ba. Kuma ya auri Aliya bint Zabyan amma ya sake ta.
Akwai kuma wadanda ya yi sadaka da su a matsayin bayinsa. wadannan kuma su ne: Mariyatul Kibdiyyah da Raihanatu bint Sham’un. Amma dukkan wadannan da suka karu a kan 11 na farko, malaman tarihi sun yi sabani a kansu. Wallahu a’alam.
- Tahirin ’Ya’yan Manzon Allah a takaici
Dangane kuma da ’ya’yan Ma’aiki (SAW), magana mafi shahara ita ce Manzon Allah (SAW) ya haifi ’ya’ya bakwai ne a duniya, haka Almakdisiy ya ce a cikin kaulinsa.
Wadannan ’ya’ya kuwa sun kunshi maza uku da mata hudu, kamar haka:
- Al-Qasim: An haife shi shekara biyu kafin a aiko Manzon Allah (SAW) da manzanci. Da shi Al-Kasim ake yi wa Manzon Allah (SAW) alkunya, wato ake kiransa da Abul-Kasim, kuma Allah Ya yi masa rasuwa bayan ’yan kwanaki a duniya.
- Abdullahi: Ana kiransa Attayyib ko kuma Attahir. An haife shi a cikin Musulunci, kuma shi ma ya bar duniya bai yi shekaru da yawa ba.
- Ibrahim: An haifi Ibrahimul- Mu’azzam a garin Madina, kuma shi kadai ne ba dan Khadijah (RA) ba a cikin ’ya’yan Manzon Allah (SAW). Mahaifiyarsa ita ce kuyangar Annabi (SAW) mai suna Mariyatul-Kibdiyya. Ya rasu yana da wata takwas a duniya.
- Zainab: Ita ce babbarsu, kuma ta auri Abdul Ass bn Arrabi’a bn Abdul Uzza.
- Ruqayyah: Ta auri sahabi kuma Khalifan Manzon Allah (SAW) Usman bin Affan (RA).
- Fadimatu: Ta auri Aliyu bin Abu Dalib, kuma ’ya’yanta biyu wato Al-Hassan da Al-Hussain su ne shugabannin samarin gidan Aljanna.
- Ummu Khulsum: Bayan rasuwar Ruqayyah ita aka aurar wa Usman bin Affan (RA), wannan ya sa ake kiransa Zun-Nuraini, wato ma’abocin haske biyu.