Tarihin Sa’adu Zungur: Ɗan siyasar farko a Arewacin Najeriya
Shi ne ɗan Arewa na farko da Turawan Mulkin Mallaka suka tura shi makarantar gaba da sakandare a Kudancin Najeriya
Malam Sa’adu Zungur ya shahara ne a Arewacin Najeriya sanadiyyar waƙoƙin da ya wallafa.
Amma ko kun san shi ne ɗan Arewa na farko da Turawan Mulkin Mallaka suka tura shi makarantar gaba da sakandare a Kudancin Najeriya?
- Shettima da Ministan Tsaro sun je ta’aziyyar Harin Mauludin Kaduna
- Tuna baya: Tarihin Dokta Goodluck Ebele Jonathan
Ko kun san shi ne ya fara kafa ƙungiyar siyasa a Arewacin Najeriya?
Ko kun san shi ne ya fara shirya zanga-zangar ƙin amincewa da manufar gwamnati a Arewacin Najeriya?
Ko kun san shi ne ɗan Arewa na farko da ya riƙe muƙami a jam’iyyar siyasa ta ƙasa?
Ko kun san shi ne ya fara kai ƙarar Bature kotu kuma ya yi nasara a kansa a Arewacin Najeriya?
Wannan jajirtaccen ɗan gwagwarmayar, ya rayu ne tsawon shekaru 43 a duniya kuma ya rasu ana saura shekaru biyu Najeriya ta samu ƴancin kai.