Tarihin sabon Sarkin Nasarawa Alhaji Ibrahim Usman Jibril
Sabon Sarkin Nasarawa da ke Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Usman Jibril, wanda kuma shine tsohon Ministan Muhalli na Najeriya kuma tsohon Wamban Nasarawa, Aminiya ta duba tarihinsa a takaice: Sarauta musamman a Nahiyar Afirka, tana da daraja matuka. Shi ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin karamci ya kira tsohon Ministan Muhalli, Alhaji Ibrahim Usman […]
Sabon Sarkin Nasarawa da ke Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Usman Jibril, wanda kuma shine tsohon Ministan Muhalli na Najeriya kuma tsohon Wamban Nasarawa, Aminiya ta duba tarihinsa a takaice:
Sarauta musamman a Nahiyar Afirka, tana da daraja matuka. Shi ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin karamci ya kira tsohon Ministan Muhalli, Alhaji Ibrahim Usman Jibril a matsayin “Mai martaba” a taron Majalisar Zartarwa na ranar 12 ga watan Disamban bara (2018). Wannan shi ne taron karshe da sabon Sarkin ya halarta a matsayinsa na Minista bayan da aka nada shi a matsayin Sarkin Nasarawa ranar 7 ga watan Disamban 2018. Yayin da Shugaban Kasa ya halarci zauren, majalisar bayan an kammala taken Najeriya, sai ya ce “Mai martaba ya yi mana addu’a.” Yadda ake karrama sarauta ke nan.
Iyaye da asali
An haifi sabon Sarkin Nasarawa Alhaji Ibrahim Usman Jibril ne ranar 27 ga watan Janairun 1958 a Nasarawa, mahifinsa shi ne Fagacin Nasarawa, Alhaji Usman Maikwato Jibril da Hajiya Fatima Ibrahim (Allah Ya rahamshe su, amin).
Mahifinsa dan Makama Jibril, babban dan Sarkin Nasarawa na takwas, Umaru Maje Haji. Sabon Sarkin ya zamo jikan-jika kuma jinin Umaru Dogo wanda ya kafa Nasarawa.
Ilimi
Sabon Sarkin ana kiransa da suna “Baba na Kulu”, ya taso ne a gaban iyayensa, kuma kamar yadda al’adar Musulmi Hausawa da Fulani take, ya fara karatun Kur’ani ne a Fadar Sarki a karkashin Malam Babba da kuma Malam Jibril Jatau na Bakin Kogi.
Ya shiga makarantar firamare ta Central da ke Nasarawa a zamanin Malam Hussaini Katukan Nasarawa da Malam Dallah. Bayan ya kammala aji bakwai, sai ya ci gaba da karatu a Makarantar Gwamnati ta GSS Nasarawa wacce aka sauya mata suna zuwa Makarantar Jeka-ka-dawo GDSS, Nasarawa.
Aiki da shahara
Bayan ya samu takardar shaidar kammala makarantar sakandare, ya fara aikin koyarwa ne a makarantar da ya yi wato makarantar Firamare ta Central ta Nasarawa inda ya yi aikin koyarwa na shekara daya kafin ya samu gurbin karatu a makarantar share fagen shiga jami’a ta da ke Yola a tsohuwar Jihar Gongola, wacce a yanzu take Jihar Adamawa a 1978 sannan ya kammala a 1978.
Ya dawo makarantar da ya kammala wato GSS Nasarawa ya fara koyarwa kafin ya samu gurbin karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano a 1980 inda ya samu digiri a fannin Ilmin Muhalli a 1983.
Ya yi aikin yi wa kasa hidima na shekara daya (NYSC) a makarantar sojoji masu yaki da manyan bindigogi (Atilare) da ke Kachiya a Jihar Kaduna inda ya koyar da Ilmin Taswirar Muhalli a 1984.
Bayan nan ya yi aiki na dan lokaci a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Nasarawa kafin ya fara aiki da Ma’aikatar Ilimi ta tsohuwar Jihar Filato inda aka tura shi garin Karshi a matsayin Malamin Sakandare.
A 1985, Alhaji Ibrahim ya koma aiki da Ma’aikatar Birnin Tarayya Abuja inda ya ci gaba da koyarwa a Makarantar Gwamnati ta Kuje har tsawon shekara biyu.
Zurfafa karatu
Sarkin ya koma Jami’ar Bayero da ke Kano inda ya yi karatun digiri na biyu a fannin albarkatun kasa da gudanarwa ya kammala a 1990.
Manyan mukamai
Bayan ya kammala karatun digiri na biyu, an sauya shi daga fannin ilmi zuwa fannin fili da safiyo a 1990 inda ya yi fice sannan aka rataya masa ayyukan da suka hada da Sakataren Kwamitin Tarawa da Tabbatar da bi Tsarin Asali na Abuja, da tarawa da tsara filayen birnin a na’urar kwamfuta.
Ya shafe shekara 25 a fannin fili a matsayin jami’i har ya kai matsayin Mataimakin Daraktan Bangaren Bunkasa Birnin, inda ya yi aiki da ministoci biyar kafin ya zama Daraktan Fannin Gudanar da Fili.
Bugu da kari, ya yi aiki da Hukumar Tsara Filaye ta Jihar Nasarawa (NAGIS) inda ake yi masa lakabi da “Sarkin Aiki” kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Minista.
Sarkin Ibrahim Usman Jibril ya gudanar da aikin NAGIS fiye da Dalar Amurka miliyan 17 inda ya yi amfani da sababbin dabarun zamani don sabunta samarwa da raba filaye a Jihar Nasarawa.
Zama Sarki
Bayan da Allah Ya yi wa Sarkin Nasarawa Alhaji Hassan Ahmed II rasuwa, masu zaben Sarkin Nasarawa suka zabe shi a matsayin Sarki, sannan Majalisar Sarakuna ta Jihar Nasarawa ta amince da shi.
Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Nasarawa, Haruna Iliya Osegba ya ce, “Gwamnna Umaru Al-Makura ya amince da zaben Alhaji Ibrahim Usman Jibril a matsayin sabon Sarkin Nasarawa bayan da taron Majalisar Sarakunar Jihar ya amince da shi.” Wannan ya sa malamin makaranta, jami’in gudanarwa sannan daga bayan nan Minista ya zama sabon Sarkin Nasarawa.
Iyali
Sarki Ibrahim yana da mata biyu, Hajiya Hauwa Kulu da kuma Hajiya Mairo, sannan yana da ’ya’ya.