Tarihin sarautar Dan-Isa a Masarautar Zazzau

Banda sarautar Wambai da Dan Galadima da kuma Sa’i da Turaki sauran sarautun suna ƙasan Dan-Isa ne.

Tarihin sarautar Dan-Isa a Masarautar Zazzau

Tattaunawa a game da tarihin sarautar Dan­Isa a masarautar Zazzau tare da Wakilin Tarihin Zazzau Alhaji Shehu Ahmed.

Aminiya: Za mu so ka yi mana bayanin tarihin sarautar Dan-Isa.

Wakilin Tarihi: Akwai Isa ta Sabon Birni da Isa ta Gobir da kuma Isa ta Madawa kowanne akwai ma’anar sunan.

A garuruwa galibi sai dai su ara amma a masarautar Kano aka fara sarautar kuma masarautar Zazzau ta fara naɗa sarautar a lokacin marigayi sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

Tun daga sarki malam Musa ba a taɓa sarautar Dan-Isa ba kamar yadda Ciroma Aminu Bamalli ya fara zama Ciroma a masarautar Zazzau wadda aka aro ta daga Kano inda har Ciroman Labarai akwai a Zazzau.

Aminiya: Zazzau ta aro sarautar Dan-Isa daga Kano kenan?

Wakilin Tarihi: Mai martaba sarki ya yi tunani ya ce akwai babban wansu kuma autan Sambo malam Abdulkarim ɗan Nasiru ɗan Sambo saboda haka sarki ya duba irin sarautar da zai yi masa ya karrama shi to shi ya sa ya ɗauko ta ya ba wansa Abdulkarim bayan rasuwarsa sai aka naɗa ƙaninsa.

An fara naɗa Dan-Isa Uwaisu bayan rasuwarsa sai aka naɗa Dan-Isa Aƙilu bayan rasuwar Akilu sai aka naɗa Dan­Isa Ummaru Shehu Idris, wadda ya rasu kwanannan kuma yanzu haka an ba Mustapha Aliyu Shehu Idris sarautar

Dan-Isan Zazzau dukkan waɗanda suka riƙe wannan sarauta ta Dan-Isan Zazzau a gidan Katsinawa suke. Ba a taɓa bayar da ita ga sauran gidajen sarautar da ke masarautar Zazzau ba.

Aminiya: Ita sarautar Dan­Isa sai ‘ya’yan sarki ake naɗawa ko ana iya bayarwa ga waɗanda ba ‘ya’yan sarki ba?

Wakilin Tarihi: A chan inda aka aro sarautar ba a taɓa naɗa wani da ba ɗan sarki ba. Ƙarin bayani a nan shi ne duk sarautar da ka ji an fara da Kalmar ɗan, to ta ‘ya’yan sarki ce a Kano.

Aminiya: Me ya sa ba ku ƙirƙiro ta ku ba sai dai ku ka aro?

Wakilin Tarihi: Ha ha ha, Akwai wani abu da masarautu ke yi a tsakaninsu musamman na amfani da sunan sarauta inda suke bayayya a tsakaninsu ta hanyar rubuta takarda ga masaraútar da za a yi amfani da irin sunan sarautarsu kamar yadda su ma sukan ara amma sarautar Dan-Isa ban sani ba ko Kano su ma sun aro ne daga wani gari.

Aminiya: Wannan Dan-Isan shi ne na nawa a masarautar Zazzau?

Wakilin Tarihi: Shi ne na huɗu, amma yanzu an sami na biyar su ne Dan-Isa Uwaisu da Dan-Isa Abdulkarim sai Dan-Isa Akilu sai Dan-Isa Ummaru sai kuma yanzu Dan­Isa Mustapha Aliyu Shehu Idris.

Aminiya: Wace alfarma sarautar Dan-Isa take da shi?

Wakilin Tarihi: Babbar alfarmar sarautar ita ce kusanci da sarki kuma ɗan sarki ake yi wa. Kuma shi ke shugabantar wasu al’amurra na Sarki, sannan a cikin sarautun da ke gidan Katsinawa idan aka aro abu ya zaunu to ko shakka babu ya zaunu ke nan.

Banda sarautar Wambai da Dan Galadima da kuma Sa’i da Turaki sauran sarautun suna ƙasan Dan-Isa ne.

Aminiya: Sarautar Dan-Isa ta tsaya a gidan Katsinawa kawai mene sirrin?

Wakilin Tarihi: Ikon Allah ne da kuma lokaci.

Aminiya: A ƙarshe Mene ne fatanka?

Wakilin Tarihi: Fatana Allah Ya haɗa kansu kuma su kalli yadda sarauta ta tsaya a ɗaki ɗaya ba tare da ta fita ba.

Aminiya: Akwai yiwuwar sarautar Dan-Isa ta fita daga gidan Katsinawa ta faɗa wani gidan a nan gaba ke nan?

Wakilin Tarihi: Ƙwarai kuwa akwai yiwuwar haka in hali ya bayar nan gaba

Aminiya: Ko za ka lissafa mana sarautun da suka fi ƙarfi a masarautar Zazzau?

Wakilin Tarihi: Ta farko sarautar Madaki sai Magajin­Gari sai Wali sai Dan Galadima sai Iya sai Wambai sai Turaki ita sarautar Dan-Isa ita ce ta kusan ta takwas a jerin sarautun ƙasar Zazzau, sai ga shi a yau Allah Ya ba Jika sarautar ya shige gaban iyayensa.

Aminiya: Ko za ka ba mu tarihin sabon Dan-Isan Zazzau a taƙaice.

Wakilin Tarihi: Mustapha Aliyu Shehu Idris, ɗan marigayi Madakin Zazzau Aliyu Shehu Idris ne kuma yana aiki ne a Babban Banki Nijeriya (CBN) kuma yana da mata ɗaya da yaro ɗaya.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano