Taron goyon bayan Jonathan na Asaba ya haifar da ce-ce-ku-ce

Wata Sabuwar kungiya mai da’awar samar wa ‘yan Arewa mazauna kudu zaman lafiya da yanci a jihohin da suke zaune, inda kungiyar mai suna Arewa Initiatibe for peaceful Co-edistence ta yi wani gangami a Asaba na nuna goyan baya ga Goodlock Jonathan Ebele, inda taron ya janyo ce ce ku ce a ranar Asabar din […]

Taron goyon bayan Jonathan na Asaba ya haifar da ce-ce-ku-ce
Taron goyon bayan Jonathan na Asaba ya haifar da ce-ce-ku-ce

Wata Sabuwar kungiya mai da’awar samar wa ‘yan Arewa mazauna kudu zaman lafiya da yanci a jihohin da suke zaune, inda kungiyar mai suna Arewa Initiatibe for peaceful Co-edistence ta yi wani gangami a Asaba na nuna goyan baya ga Goodlock Jonathan Ebele, inda taron ya janyo ce ce ku ce a ranar Asabar din da ta gabata. Taron dai an gudanar das hi ne a karkashin jagorancin Shugabanta, Garkuwan Sakkwato, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa.

Alhaji Bafarawa ya yi bayanai da dama a ciki har da bayanin makasudin kafa kungiyar inda ya ce ‘’Mun kafa wannan kungiyar ne domin samarwa ‘yan Arewa mazauna kudu tabbatacen zaman lafiya tsakaninsu da ’yan kudu, tare kuma da yancin samun guraben aiki da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya, kuma da yake lokaci ne na siyasa muka ga ya dace mu kira gangamin, mu nuna wa shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan muna tare da shi, kuma mun gayyato shi ya zo taron ya tabbatar da gaske muke yi,’’ a cewarsa.
Shugaba Goodluck Jonathan da aka gayyato ya yi wa mutane jawabi a taron, inda ya tabo batutuwa daban-daban da suka shafi aikin da gwamnatinsu ta yi wa kasa. Sai dai kuma masu fasa baki sunce ajawabinsa na taron ‘’
A cewar masu fashin baki: “Da alama Shugaban ya manta da bai ambaci batun tsaro da cin hanci da rashawa da wutan lantarki da tattalin arzikin kasa da faduwar darajar Naira da batun kudin mai da batun talauci da rashin aiki da kiwon lafiya da sauransu ballentana ko ya tuna ya ya zai magance irin wadannan matsalolin kawai shi dai yana bukatar asake zabansa karo na biyu.’’.
Ko’odinatan kungiyar na kudu maso kudu Alhaji musa Saidu ya ce ‘’wannan kungiyar mun kafata kuma tana aiki anan kudu kuma a Arewa kife da kwariya banda shi Alhaji dalhatu Attahiru Bafarawa babu wani Shugaba na daga Arewa da ya taba shigo nan kudu domin ya taimaka mana akan matsalilinmu saboda haka babu ruwanmu da masu ce wa wai saboda neman kuriun mutane ya sa muka yi wannan ya kamata su gane mu yanci muke nema saboda haka idan PDP ta taimakemu muna tare da ita kuma zamu bi ta ’’.
Sai dai kuma ainihin Shugabanni na alumman Arewa mazauna kudu din sunce ba za ta sabuba kawai don siyasa wasu su ari bakinsu su ci musu albasa kamar Alhaji Badamasi Sale wanda yake Shugaban yan Arewa mazauna jihar Edo daga kudu maso kudu ga abin da ya ce’’Abin da zan fada anan idan har akwai wata kungiya mai samarwa yan Arewa mazauna kudu zaman lafiya da kabilun jihohin kudu bamu ganta ba saboda haka wannan taro da aka ce sun yi a Asaba sunanta kwadayi mabudin wahala domin muna gani ake diban tsirarun mutane da basu san mutuncin kansuba suke basu dan canji da bai kai kudin cin abincisu na wuni gudaba domin su je su marawa kariya baya da watsar da yancinsu.
An yi wa Bafarawa martini, da cewa ko akwai lokacin da ya taba zuwa kudu ya tara ’yan Arewa ya wayar musu da kai akan su zauna da yan kudu lafiya; kuma kada ya manta ba da nesa ba an taba kama ’yan Jigawa a Kudu, me ya yi akai na taimakawa ? A cewarsu, ya sani kungiyarsa ta PDP ce ba ta ’yan Arewa mazauna kudu ba da wannan ina jawo hakalin shugabannin APC akan su yi hattara, domin akwai bara gurbi a cikinsu, wato ungulu da kan zabo.”
Mai bai wa Gwamnan Jihar Edo shawara akan harkokin da suka shafi al’ummar Arewa mazauna jihar, Alhaji Sahabi ALiyu (JP), cewa yayi ‘’A gaskiya wannan shiri ne na jam’iyyar PDP ba na Yan Arewa mazauna kudu ba, kuma wasu tsiraru ne da aka biya su kudi suka yi.
“Wadannan masu nuna kudin suna yaudarar mutane, ba za su kai labara ba a lokacin zabe, duk da cewa mun san kasar nan mutane na fama da talauci, wannan ya sa da zaran sun ji an ambaci batun kudi sai ka ga hankalinsu ya bace,” inji shi.