Taron hadin kan kasa

A fahimtata tuntuni ya kamata a yi taron hadin kan kasa (ko taron duba makomar kasa) a Najeriya, amma yanzu ma ba a makara ba idan har alheri ake nufi da yin taron. Sai dai wajibi ne ya zama dayan biyu, kodai ya zama mai cin gashin kansa, wanda Shugaban kasa da gwamnoni da ’yan […]

Taron hadin kan kasa

Shugaban Kasa Goodluck Ebele JonathaA fahimtata tuntuni ya kamata a yi taron hadin kan kasa (ko taron duba makomar kasa) a Najeriya, amma yanzu ma ba a makara ba idan har alheri ake nufi da yin taron. Sai dai wajibi ne ya zama dayan biyu, kodai ya zama mai cin gashin kansa, wanda Shugaban kasa da gwamnoni da ’yan majalisun tarayya da na jihohi duk su sauka daga mukamansu; Babban Alkalin Najeriya da manyan alkalan jihohi su jagoranci taron, kowannensu ya zazzage kansa a bainar jama’a a tabbatar da tsarkinsu, haka jami’an tsaro; sojoji da ’yan sanda da jami’an hukumar tsaron kasa (SSS) da na leken asirin kasa (NIA) da Kwstam da na Hukumar Shigi da Fici (Immigration) da sauransu. Sannan a samu wakilan jama’a tsarkakakku, mutum daya ya wakilci mutum miliyan daya a kowace jiha. Jihar da take da mutum miliyan goma ta ba da wakilai goma, jiha mai mutum miliyan uku ta ba da wakilai uku, kowane mutum miliyan daya mutum daya ya wakilce su. Sannan sai su kafa kwamitin bin kadin kowane irin zalunci da aka yi wa kowane dan Najeriya, a kwato masa hakkinsa a danka masa. Idan ya mutu a ba magadansa. Har sai kowa ya samu hakkinsa ya koma hayyacinsa, sannan kowa ya ba da shawarar yadda za a zauna tare da irin mulkin da za a dora kasar a kai, don a samu ci gaban adalci mai dorewa.
Ko kuma shi Shugaban kasa da dukkan gwamnoni kowannensu ya zazzage kansa. Kamar yadda marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Murtala Muhammad ya yi. Sannan a tilasta wa duk wakilai da masu rike da amanar jama’a na kowanne fanni su zazzage kansu ko a zazzage su, duk abin da kowannensu ya mallaka ta hanyar da ba ta kamata ba, ya dawo da su ko a kwato, a mayar wa masu hakki kayansu. Sannan a fara maganar makomar kasar.
Idan hagu ta kiya sai mu koma dama!
Ina mika goron gayyata ga dukkan wadanda aka zalunta ko ake zalunta a mulkin da ake yi a Najeriya, mu hadu mu san juna mu fahimci juna, mu yi wa kanmu kiyamullaili da karatun ta-nastu mu sani Allah ne kadai Yake sonmu, mu ma ya kamata mu tsaya ga Allah mu nema wa kanmu makoma mafi dacewa. Kada mu yarda a yi mana hannun wa-ka-ci-ka-tashi. Mu tsaya tsayin daka har sai wadanda suka wawashe mana arzikin kasa, suka talauta al’umma, suka tsiyata su, suka yunwatasu, suka jefa mu cikin mawuyacin hali na rashin sanin gaba ko baya. Suka maida mu tamkar dabbar gida wadda tana gani ana kashe (yanka) ’yan uwanta har a zo kanta, akasin dabbar daji wacce ana taba ’yar uwarta za ta yi wo kan wanda ya taba ’yar uwar tata ko ta gudu.
Idan ma so ake yi a raba Najeriya sai a fara da tabbatar da kowa ya samu hakkinsa daidai-wa-daida kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin kasa ya tanada, sannan kowa ya fadi albarkacin bakinsa: ko a ci gaba da zama tare ko a rabu. Sai mun duba irin tanade-tanaden da ke kunshe a Kundin Tsarin Mulkin kasar zuwa yanzu a fannin tsaron rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowa da kowa.
(2) Tattalin arziki da siyasa; a tabbatar kowa ya samu hakkinsa bisa adalci.
(3) Sojoji da ’yan sanda da SSS da Kwastam da Shigi da Fici da sauran jami’an tsaro da ma’aikata su maida hankalinsu wajen neman hakkinsu maimakon sata da kashe mutane da kwace ko hada kai da masu laifi. Haka ma’aikatan da suka rasa ayyukansu ko hakkokinsu sakamakon rufe wuraren ayyukansu ko rage ma’aikata. Su rika yin zanga-zangar lumana kan hakkinsu maimakon yin tarzoma!

Alhaji Abdulkarim daiyabu, Kano
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN)        
08023106666, 08060116666

 

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50