Taron kaddamar da shugabanni a Zariya: Sako na musamman ga Gizagawan Zumunci

A yayin da kungiyar Gizago ke bikin kaddamar da sababbin zababbun shugabanni a gobe Asabar, a Zariya, daya daga cikin iyayenta, Malam Mahmoon Baba-Ahmed 08053235544, ya shiga rigar dattijai, ya ba Gizagawa shawara, domin dai a ci gaba da tafiyar da harkar zumunci da taimakon juna cikin fa’ida. Ga shawarar dattijon kamar haka:Ina yi wa […]

Taron kaddamar da shugabanni a Zariya: Sako na musamman ga Gizagawan Zumunci

Zaratan Gizagawan Zumunci, a yayin da suka kai wa Malam Mahmoon Baba Ahmad ziyarar bangirma, a Kaduna, kwanakin bayaA yayin da kungiyar Gizago ke bikin kaddamar da sababbin zababbun shugabanni a gobe Asabar, a Zariya, daya daga cikin iyayenta, Malam Mahmoon Baba-Ahmed 08053235544, ya shiga rigar dattijai, ya ba Gizagawa shawara, domin dai a ci gaba da tafiyar da harkar zumunci da taimakon juna cikin fa’ida. Ga shawarar dattijon kamar haka:
Ina yi wa Gizagawa murnar hallara a yau don gudanar wani gagarumin aikin mai muhimmanci, wajen kara daukaka kungiyarmu ta Gizago Social and Cultural Association. Wannan ba shi ne lokaci na farko ba da ’ya’yan kungiya ke kokarin sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kungiyar ya dora masu, wato zaben shugabannin kwamitin zartarwa amma sai dai wannan shi ne lokaci na farko da hakan zai wakana a karkashin sabon jagorancin kungiyar na kasa baki daya. To amma na tabbata ’yan kungiya na sane da muhimancin wannan aikin, za su kuma kokarta don yin dukkan abubuwan da suka wajaba don kai wa ga nasara.
A lokaci irin wannan da kuma sauran lokutan da ake daukar matakan yi wa kungiya hidima don daukaka martabarta, tilas ne a yi la’akari da dokoki da kuma ka’idojin da ke kunshe cikin kundin tsarin wannan mashahuriyar kungiya, don a tabbatar an yi dukkan abubuwan da suka wajaba, yadda ya kamata, ta yadda za a guje wa wata tangardar da za ta iya jawo rashin gamsuwar wasu ’ya’yanta har hakan ya kai ga samun baraka.
Ina sane da cewa wannan kungiya tana hannun shugabanni nagari ne, adalai, masu sha’awar ganin an kamanta gaskiya, an kuma tsayar da adalci a dukkan al’amuran da suka shafi ’ya’yan kungiyar, saboda haka ba ni da haufi game da matakan da aka dauka don gudanar da zabubbukan da aka tsara don samar da ingantattun shugabannin da za su tabbatar da dorewar manufofin raya kungiya da kuma ayyukanta na ciyar da kasa gaba.
Ya kamata kuma shugabanni da wakilan wannan muhimmin taro su yi taka-tsan-tsan, su nuna sanin-ya-kamata a dukkan lamurran da ke gabansu don a gudanar da zabe lami lafiya, ta yadda za su tsira daga zargi, su kuma kare mutuncin kungiya. A yanzu haka daukacin al’ummomin Najeriya sun zura ido kan shugabanni da ’ya’yan wannan kungiya don shaida yadda za a gudanar da wannan zabe. To ya kamata wadanda suka tsara shi su ba mara da kunya, ta hanyar guje wa dukkan ababen da za su kawo tangarda ko magudin da zai haddasa jidali. Najeriya ta yi kaurin suna game da magudin zabe, kuma ba wasu ba ne can daban daga wata nahiyar duniya ke tsara zabe da gudanar da shi a Najeriyar, illa ’ya’yanta. To, ku ma fa ’ya’yan Najeriya ne da ke zama cikin irin wadancan mutanen masu murda zabe da kuma aikata ha’inci wajen bayyana sakamako. Ya kamata ku nuna wa duniya cewa ai ba a taru an zama daya ba. Idan jam’iyyun siyasa sun gwanance wajen magubin zabe, sauran kungiyoyi, musamman ma ta Gizago, ba haka nan take ba, za ku gudanar da zaben da kowa da kowa zai kwarzanta saboda ingancinsa, kuma hakan ya zama abin koyi ga sauran kungiyoyin har ma da jam’iyyun siyasar da ake gani kamar sun yi nisa, ba su jin kira.
Ina fata yadda Allah Ya hada ku a wannan wuri lafiya, zai ba ku ikon gudanar da al’amuran da ke gabanku lami lafiya, Ya kuma koma da ku gidajenku lafiya.
***
Sanarwa:
A gobe Asabar, Gizagawan Zumunci na da gagarumin bikin kaddamarwa da rantsar da sababbin shugabannin Gizagawa na kasa da na jihohi. Za a gudanar da taron ne a Zauren Taro Na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Kwalejin Barewa, Zariya; da misalin karfe 9:00 na safe. Ana gayyatar daukacin Gizagawan Zumunci da kuma sauran al’umma. Allah ba da ikon zuwa, amin.
***
Shi kuwa Zanwan Lafiya 08096430960, a nasa sakon, yana cewa: “Gizago, bayan gaisuwa mai yawa da fatan an yi Sallah lafiya, Allah Ya sa haka, amin. Ina so a mika mani godiya ta musamman ga shugabannin Gizagawan Jihar Nasarawa, musamman Sakataren Tsare-Tsare na kasa da tawagarsa, da suka kawo mani ziyarar gaisuwar Sallah a fadata da kuma fadar mai martaba Sarkin Lafiyar Bare-Bari. Allah Ya saka da alheri, Ya bar zumunci. Aminiya kuma Ya kara mata daukaka, amin.”
***
Shi kuma Alhaji Abdulrahman [email protected] tsokaci ya yi game da sharhin Gizago da ya gabatar makon shekaranjiya, mai taken: “Duk Shekara Sai Na Je Umrah – To Sai Me?” Ga abin da yake cewa:
“Assalam Alakum, alhamdu lillah. A gaskiya na ji dadin ganin wannan shafi mai amfani matuka, wanda yake da za a samu irinsu a kai-a kai, da an sami saukin lamurra da dama. Kamar kana shiga cikin zukatan mutane kana hango abin da ke faruwa yanzu! Wasu ma in suka biya wa mutumin da yake cikin talauci Umrah (ga iyali, abinci daya suke samu a rana), idan ya ce ya gode, don Allah a taimake shi a ba shi kudin, sai a ce in ba ya zuwa magana ta kare! Da dama a dole suke zuwa. To irin wannan, anya akwai lada kuwa? Shi ya sa muke son a yi kokari a bude mana filin da za mu rika tambaya ana ba mu amsa, don mu san abin da muke yi gaba daya. To na gode kuma ina fatan za ka bude mana shafin tambaya da amsa ta intanet ko sakon waya.”
***
A labarin jajantawa kuwa, mun samu labarin cewa shugaban Gizagawan Jihar Ribas Sa’idu Abubakar Badarawa 08036517450, yayar matarsa ce Allah Ya yi wa rasuwa a makon nan.
Muna rokon Allah Ya yafe mata kura-kuranta, Ya saka mata da gidan Aljanna. Haka ma sauran al’ummar Annabi, iyayenmu da malumanmu da suka riga mu gidan gaskiya, Allah Ya yi masu rahama. Mu kuma da muka rage, Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani, idan lokacinmu ya zo. Amin! – Gizago.