Taron kan noma na Jaridar Daily Trust zai fara 26 ga Nuwamba
Taron kan noma da kuma baje kolin amfanin gona karo na uku da Kamfanin Buga Jaridun Daily Trust da Aminiya, zai gudana a ranakun 26 zuwa 27 ga watan Nuwamban nan, a otel din Federal Palace Hotel, da ke Tsibirin Bictoria Island, a birnin Legas. Taron da aka yi wa taken: “Gyara Tsarin Noman Shinkafa […]
Taron kan noma da kuma baje kolin amfanin gona karo na uku da Kamfanin Buga Jaridun Daily Trust da Aminiya, zai gudana a ranakun 26 zuwa 27 ga watan Nuwamban nan, a otel din Federal Palace Hotel, da ke Tsibirin Bictoria Island, a birnin Legas.
Taron da aka yi wa taken: “Gyara Tsarin Noman Shinkafa da Sukari da Harkar Samar da Madara domin Rubanya Samar da su,” ana sa ran zai tattauna muhimman batutuwan da suka jibinci noman shinkafar da sarrafa sukari tare da madara a cikin Najeriya da zimmar kara samar da su.
Ana sa ran Mista Emmanuel Ijewere, wanda shi ne Babban Jami’in Kasuwancin Noma, zai halarci taron a matsayin Shugaban Taro, yayin da Ministan Ayyukan Gona, Alhaji Muhammadu Sabo Nanono, zai zama Babban Bako a wajen taron.
Masu ruwa-da-tsaki a harkar noma da suka hada da ma’aikatun gona na jihohi da na tarayya da na tsare-tsare da kuma hukumomin da ke da nasaba da aikin gona; ire-iren su cibiyoyin nazarin noma na kasa da Hukumar Inganta Sukari ta Kasa da Hukumar Bincike da Inganta Kayayyakin Noman da ba a kai ga Sarrafa ba da kuma Hukumar Alkinta Amfanin Gona ta Kasa, ake sa ran su halarci taron.
Saura wadanda ake tsammanin su halarci taron, sun hadar da masana’antun da ke sarrafa kayayyakin amfanin gona da sauran magunguna da bankunan ’yan kasuwa da kungiyoyin masu sarrafa shinkafa da sauran wadanda ke da bukatar halartar taron.
Za a fara taron ne da misalin karfe 9:30 na kowace safiya.