Taron kasa: A dauri kashi ko a bata igiya?
Shugaba Goodluck Jonathan da kuma Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Dabid Mark suna daga cikin mutane uku da mukamansu suka dara sauran na ‘yan Najeriya, kuma dukkansu ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Baicin haka nan kuma a majalisar da Dabid Mark ke shugabanci ne ake tsara dokokin da Shugaba Jonathan kan amince da su kafin su fara […]
Shugaba Goodluck Jonathan da kuma Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Dabid Mark suna daga cikin mutane uku da mukamansu suka dara sauran na ‘yan Najeriya, kuma dukkansu ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Baicin haka nan kuma a majalisar da Dabid Mark ke shugabanci ne ake tsara dokokin da Shugaba Jonathan kan amince da su kafin su fara aiki, domin shi ne mafiya rinjayen ‘yan Najeriya suka zaba, suka amince masa don aiwatar da harkokin da suka shafi rayuwa da yanayin zamantakewarsu.
Ba a nan kadai dangantakarsu ta kare ba: dukkansu sun sha sukar lamirin taron kasa da a Turance ake kira ‘National Conference’ don tattauna matsalolin da ke addabar kasar nan a siyasance, da kuma gano mafita daga gare su, domin a ganinsu wannan ita ce hanya mafi sauki da za ta tayar da wata gagarumar fitinar da za ta raba kan kasar nan, ta kuma kawo fitintunun da za su hana zaman lafiya.
Sun yi imanin cewa wannan taron ba zai yi wani tasiri ba, domin kuwa ba zai yiwu a gudanar da shi ba alhali kuwa akwai majalisar da daukacin jama’ar kasar nan suka tuttura wakilansu can don tsara manufofi da yin dokokin da suke da fa’ida wajen gudanar da harkoki da al’amuran kasa. Sa’annan akwai shugaban kasa mai aiwatar da dukkan dokokin da majalisa ta kafa, kuma bayan Shugaba ya yarda da su sai su fara aiki. To idan kuwa haka ne ashe ba wanda zai muzanta su idan har suka yi dari-dari da duk wata manufa ta yin wani taron da suke gani ba shi da muhalli a tsarin mulki ko dalilin gudanar da shi, ko kuma ba wanda zai kyare su idan suka washi duk wani take-taken da za su kai ga yin haka.
To, amma kuma kwatsam sai ga Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Dabid Mark ya fito fili, firi-falo a ‘yan makonnin da suka gabata, yana ta zakewa game da goyon baya ga kiran irin wancan taron da aka dade da watsi da shi, kuma a lokacin ne jama’ar kasa nan suka fara tunanin cewa ruwa bai tsami banza. Idan ba akwai wata kullalliyar maganar da ya jajibo ta daga kasashen ketare ba, inda ya je shakatawa yayin da Majalisar ke hutun watanni biyu, me ya kai shi furta irin wannan kalamin da wanda duk ya ji zai san an ingiza shi yin katobarar da za ta tayar da zaune-tsaye ce a kasar? Kafin kakabin da ke zukatan jama’a ya kwaranye, sai kuma ga uban tafiya, Shugaba Jonathan shi ma ya caba magana irin waccan, jim kadan bayan komowarsa daga bulaguron da ya yi a Amurka a watan jiya, inda ya gana da Shugaba Barack Obama da wasu kusosin gwamnatinsa.
Wannan al’amarin ya sa ‘yan Najeriya shan jinin jikinsu, musamman ma saboda ganin yadda wadancan manyan shugabanni biyu suka canja ra’ayinsu da rana tsaka game da batun wancan taro da ‘yan kudancin kasar nan suka yi ta dada kawunansu da kasa game da shi, hakan kuma ya sa ‘yan Arewa kyamatar abin saboda sun tabbatar tamkar tauraruwa mai wutsiya zai kasance, gudanar da shi ba zai yi masu alheri ba. Sun tabbatar bakin Jonathan da na Dabid Mark daya ne hadin kai tsakaninsu zai iya wanzar da yanayin da zai canja wasu muhimman al’amuran gudanar da mulkin kasar nan.
Ba daidai ba ne a wannan marrar da batutuwan addini da na kabilanci suka dade da wargaza hadin kan talakawan kasar nan a ce za a kawo wannan batun, domin kuwa yin haka wani sabon salo ne da za a dauka da gangan, don farfado da bambance-bambancen addini da kyamar juna a zauren taron, kuma babu ta yadda za a yi a ce za a yi wannan taron, a gama lami lafiya, ba tare da an cusa wadannan batutuwan don su kara dagula al’amuranmu ba, watakila ma hakan ya jawo wargajewar kasar. Wannan wata dabara ce don sake amfani da addini a jawo fitinar da za ta kara fadada yanayin da ya sa ake ta samun tashin-tashina don wasu su samu hujjar neman ballewa daga Najeriya.
A takaice dai babu wani abin da wancan taron zai tsinana illa rarraba kawunan ‘yan adawa, musamman na yankin Kudu-maso Yamma, wadanda tun can fil-azal su ne suka faro zancen irin wanan taron. Baicin haka nan kuma taron zai kara gwara kawunan jama’ar da yanzu haka ba su jituwa ne saboda matsalolin da aka kasa kawarwa, wadanda taro irin wancan bai iya magancewa. Saboda haka nan ina ranarsa? A dauri kashi ko a bata igiya kawai?