Taron kasa: Abin boye zai fito fili

Duk abin da ya yi farko, zai yi karshe, ban da ikon Allah. Ga shi nan kuma a ranar Litinin din da ta gabata an fara gagarumin taron kasa da ake ta zancen za a yi a Abuja don kyautata matsayin Najeriya a siyasance da kuma ta fuskar mulki, kuma nan da watanni uku masu […]

Taron kasa: Abin boye zai fito fili
Taron kasa: Abin boye zai fito fili

Duk abin da ya yi farko, zai yi karshe, ban da ikon Allah. Ga shi nan kuma a ranar Litinin din da ta gabata an fara gagarumin taron kasa da ake ta zancen za a yi a Abuja don kyautata matsayin Najeriya a siyasance da kuma ta fuskar mulki, kuma nan da watanni uku masu zuwa zai zama tarihi. Amma sai dai watakila sakamakonsa, ya kasance abin alheri ga kasar nan, ko kuma ya zamanto matsalar da za ta dora ta bisa mawuyaciyar turbar daidaicewa. Dalili kuwa shi ne wata boyayyiyar manufa ce ake neman fitowa da ita fili yayin da ake tsakiyar gudanar da wannan taron.
An dai rigaya an san matsayin  Shugaba Goodluck Jonathan da kuma makarrabansa game da taro irin wannan, wanda suka la’ance shi, suka kuma soki lamirinsa ganin cewa babu ta yadda za a yi a gudanar da shi hakan nan zikau-mikau idan dai ba ana son a yi wa Majalisar kasa kishiya ce ba. Amma kwatsam sai ga shi nan Shugaba Jonathan ya nuna cikakkiyar aniyarsa ta kiran irin wannan taro a lokacin da aka gargade shi game da rashin dacewar hakan, musamman ma saboda kusancin taron da babban zaben shekara mai zuwa da kuma haramtattun kudaden da zai kashe kan yawancin wakilan da shi da gwamnoni za su zaba don zuwa taron da kuma makomar sakamakon taron shi kansa.   
Yanzu dai wadannan batutuwa sun zama tarihi, an fara taro, sai a jira a ga yadda muhawarori kan batutuwa goma sha biyu da za a yi yayin taron za su wanye, da kuma yadda za ta kwaranye a kwaryar dakin taron. Sa’annan kuma talakawan Najeriya sun zura idanu su ga yadda Shugaba Jonathan zai yi da sakamakon zaben, domin an ce wanda ya daure kura shi zai kwance abarsa. Illai kuwa dabara ba ta kare wa Shugaba Jonathan ba game da haka, domin a jawabinsa yayin kaddamar da taron ya bukaci Majalisar kasa da ta hanzarta aiwatar da gyare-gyaren kundin 1999 da take yi a halin yanzu, wadanda suka hada da kokarin cusa batutuwan zaben raba gardama kan wasu mawuyatan al’amuran kasar nan daidai da yadda mutanensa ke son a yi gyara ga sashi na bakwai na kundin don hakan ya bayar da damar samar da wani kundi, sabo fil bayan an kawar da na 1999 da ake aiki da shi yanzu.
Kamar yadda su Shugaba Jonathan ke  bukata, Majalisar kasa na iya yin wadannan gyararrakin da sauri kafin taron kasa ya wanye, don a samu sukunin gabatar da sakamakonsa ga talakawan da za su amince ko watsi da abin da ya kunsa a zaben raba gardama. Idan har an amince da abubuwan da aka dukunkuna a cikinsa shi ke nan sai a yi amfani da su don rubuta sabon kundin tsarin mulki, a jingine na 1999.
Babbar magana! Wai dan sanda ya ga gawar soja. Anya hakan kuwa na iya yiwuwa, ganin cewa jami’iyyar PDP ba ta da kashi biyu bisa uku na ’ya’yanta a cikin majalisun dattijai da kuma ta wakilai da za su amince a hanzarta yin wadancan muhimman gyare-gyaren da za su ba ta damar gabatar da sabon kundin tsarin mulki? Baicin haka nan kuma zaben raba gardama, kamar mace ce da ciki, ba wanda ya san abin da za ta haifa, idan har an gama taron lami lafiya, Jonathan ya nemi jama’a su raba gardama kan abubuwan da ya kunsa, sai suka sanya kafa suka shure su, sai kuma kaka? Irin wannan zaben sabon al’amari ne a kasar nan, kuma ganin yadda ba a kwashewa lafiya a lokutan zabubbuka hakan na iya haddasa gagarumar fitinar da  za ta iya wargaza kasar. Ka ga garin neman kiba sai a jajibo rama ke nan. Hakan da ake son yi kuma na iya jinkirta kammala matakan da ake so a dauka don yin gyararrakin har a kai ga lokacin zaben 2015, da kuma karshen wa’adin dukkan zababbu, kuma daidai da dakika guda ba za a kara wa kowa ba. Wannan ba zai iya janyo rikicin da ba wanda zai iya kayyade aibunsa ba?
To idan har ma ta kai za a yi zaben raba gardama kan sakamakon babban taro, ina za a samo kudaden gudanar da shi? Ai an ki yi zabe ne don samar da wakilan da za su halarci wannan taron da ake yi domin an ce wai shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega ya ce za a dauki watanni biyar ana shiryawa kuma zai ci Naira miliyan dubu shida, sa’annan sai an yi gyara ga dokar da ta kafa hukumarsa don ta samu damar gudanar da zabe irin wannan.
Tun da farko dai Shugaba Jonathan bai san abin da zai yi da sakamakon zaben da ya kira da rana tsaka ba, sai daga bisani ne ya ce zai tura wa majalisar kasa su san na yi da shi, ga shi kuma yanzu ya ce zaben raba gardama za a yi bayan ’yan majalisa sun yi gyara ga kundin 1999 don a samu sukunin yin  haka. Bisa ga dukkan alamu dai makasudin kiran wannan taron shi ne tsara dabarar samar da wani kundin tsari mulki sabo fil daga sakamakonsa.
Idan ta-bi-ta-daga-daga na kurya ka sha kashi, an zura ido a ga yadda abin boye zai fito fili.